← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan ya fito daga wankan ƙaramar riga yasaka da kuma wando 3 quater,ganin bai ganta a ɗakin ba yasa ya fito falon,nan ma batanan,amma yana tsaye yaga ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da kofi.
A gaban kujerar dayake zama kullum ta ajiye,itama kuma ta zauna a gefe.
Har tagama komai yana nan tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana kallonta,shidai yasan wani abu yakeji gameda wannan matar a cikin ransa.
Da hannu ta nuna masa yazo ya zauna,ganin ya tsaya kaman wani soja (ohh dama sojanne ashe).
"Ciwon ƙirjinnaka ya lafa ne kokuma na samomaka maganin?"
Ajiye cup ɗin hannunsa yayi tareda yin ɗan ƙaramin murmushi.
"Idan nace ki nemo min maganin a ina zaki nemo?"
"A inda yake zan nemo"
"Wanne magani zakice a baki?"
"Uhmm maganin ciwon zuciya idan akayi mata abinda ba daidai ba"
Maganar tata ce ta bashi dariya,agogon É—akin ya kalla.
"Dare yayi yakamata ki tafi"
"Uhm amma zaka iyah........"
"Am not a child Sumaimah,nasaba da irin wannan yanayin zan kulada kaina. Nagode da kulawarki,amma kusancin mu yana yawa,kada ya wuce mizani"
ÆŠaga masa kai kawai tayi,domin batada tacewa a yanzun.
Rakata yayi har bakin ƙofa ta fita shikuma ya rufe.
Dare yafara kam,don goma ta wuce,saidai akwai farin wata daya haska gidan.

"Kinƙirani mommy,shin mai yake faruwa?"
Neelah ta tambayi hajiyah Maryam wacce take zaune ta haÉ—a kai da gwiwa.
Magana neelah tacigaba dayi mata,amma kuma babu wanda ta amsa mata a ciki,hasalima ko É—agowa batayiba daga tsugunnen.
Zama tayi a bakin gadon kusada itah kana ta sauƙe wani gwauron numfashi.
Sun daÉ—e a hakan kusan awa guda, hajiyah Maryam batace komai ba,itakuma Neelah ta gaji da tambayarta.
"Sumaimah batazo ba,baki haÉ—u da ita a hanya ba"
"Uhm banganta ba"
"Ta zabeshi kenan,banyi tunani ba amma tayi zabi mai kyau,takan tsallake duk abinda bana zato"
"Mai ya faru ne a gidan?"
"Duk da a idonta akwai tsananin buƙatar son jin abinda yake faruwa,amma ta zabi kasancewa dashi."
"Wa kike magana akai?"
"Sumaimah"
"Gata nan tashigo fah"
ÆŠagowa Hajiyah Maryam tayi daidai shigowar Sumaimah cikin É—akin,wato ba É—aya ta zaba ba,ta yanke shawarar zuwa kowanne bangarene.
Takowa tayi har zuwa gaban hajiyah maryam ɗin,fuskarta a dake kaman wata soja a fagen yaƙi.
"Meyasa?"
Shine tambayar data samu ikon furtawa hajiyah Maryam,duk da kuwa a cikin ranta ba iyah hakan taso ta tsayaba.
"Meyasa me?"
"Ba É—anki bane? Meyasa zaki masa haka,ko meyasa kike masa haka?"
"Saboda shiÉ—in É—ana ne shiyasa nayi masa hakan,idan ba É—ana bane bazan damu dashi harna bada rayuwata akansa ba"
"Amma abinda kikayi a cikin bainar jama'a hakan kaman ba taimakonsa kikayi ba,saima sakashi a cikin wani tsatstsauran yanayi"
"Taimakonsa nayi Sumaimah,saidai shi taimako kala kala ne da kowacce uwa da irin hanyar da takeyi akan ƴaƴan ta. Ni tawa ƙaddarar kenan taimakonsa a ta hanyar dazai ga kaman cutar dashi nake,kokuma wani daga gefensa"
"Taimako??? Menene dalilin yin wannan maganar toh,shegantashi kikayi fah a gaban kowa,kince shi ba É—an Alhaji Aliyu bane,to É—an waye kenan baki faÉ—aba?"
"Batun É—an waye karki damu kanki,yanada uba wanda ba kowanne É—a ne ma yake iya dacen samunsa a uba ba" dalilina nayin hakan kuwa ke baki san komai ba.
Siddabarun da Mulaifah tayi masa,tayine akan Alhaji Aliyu,amma kuma ba iya nan zai tsayaba,shima Ahmad anyi asirin da idan Alhaji Aliyu ya tambayeshi to dole sai ya amince,a matsayinsa na mahaifinsa.
Sai yana ganinsa a matsayin mahaifinsa tukunna asirin zayyi tasiri,wanda bazai karyeba har sai anyi auren.
Hakanne yasa nayi amfani da gaskiya na farfaÉ—o dasu daga tarkonta. Yanzu da Ahmad ya daina ganin Alhaji Aliyu a matsayin mahaifinsa to asirin ya karye akansa"
"To amma sai kinbi ta wannan hanyar kafin ki karya abin jikinnasa,abinda kika faÉ—aba i think ya tona abinda bai kamata a tona ba ne na tsawon lokaci,kinaga hakan bayyi yawa ba"
"Yawa?? Hmmmm Sumaimah kenan!! Abinda nayi a yau É—in shine ya dace ayishi tun shekara talatin baya,dan haka banji wani É—ar ko jin babu daÉ—i akan abinda nayi,hasalima tsuntsaye biyu na jefah da dutse É—aya. Shin kinsan mai zai faru idan banyi abinda nayi yau ba?"
Jijjiga kai Sumaimah tayi,harda Neelah wacce ta tsaya ƙyam tana kallonsu su biyun,kuma ta fara ɗago mai yake faruwa.
"Nafarko zan mutu,Mulaifah zata mutu sannan shima Ahmad bazata barshi ba zata kasheshi. Wannan shine kaÉ—an daga abinda zai faru,to kinga banida zabi face yin hakan,duk da raina dana Ahmad zai sosu akan hakan"
Mutuwa kuma,abin har yakai hakane,to waye mai ƙullah hakan,waye ya hana gidan gabaɗaya zama lafiya,idan har zancen da hajiyah Maryam ta faɗa gaskiya be,cewar ba itace takeyin abubuwannan ba?.
"Hajiyah Maryam shin idan nace na yarda dake har raina,zaki bani labarin abinda yake faruwa?"
"Bazan baki ba,saboda baki yarda dani É—in ba,saidai zan baki dan wani abun daban"
"Menene?"
"Saboda ke ɗin kin zama ɗaya daga cikin a halinnan,ko ki yarda ko kowa ya yarda,ko kiƙi yarda ko kowa yaƙi amincewa,keɗin kece surukata kuma matar ɗan gidan na farko,wanda shine magajin dukkan komai. Uwa uba kuma gashi hadda ɗa,wanda shine jika na farko a wannan generation ɗin. Dan haka a matsayinki na mahaifiyar jikana,kuma matar ɗana zan faɗamiki mai yake faruwa a ahalinnan tun daga farko har ƙarshe a taƙaice.
Barina je banÉ—aki na dawo,ki shirya kwana a zaune yau"

To kuma zaku kwana a zaunen mu fara,kokuma zakuyi bacci inyaso gobe sai mu cigaba.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2*
...20...
Chapter 27 · 0% Book details