← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 48

Sashe 46

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yau kwana na uku kenan a wajennan,har yanzu banga hajiyah Mammah ba duk da nasan itace ta bada umarnin a kawoni wajennan,sai wannan mai aikinnata mara imani,jinake da inada dama zan iya yimata komai.
Jikina kaman an jefani cikin ruwan zafi haka nake jinsa,hannuna na saka a kan É—an cikina,tausayinsa nakeji sosai,yunwar da suke barni da itah abinci sau É—aya,ga kuma rashin bacci da azaba,nasan dukka sai ya shafeshi..
Hannuna na É—aga sama ina addu'ar sirri ta Allah ya kawomin mafitah.
Yau har an kai hantsi amma bata zo ba,komai yasa oho. Duk da zata cutar dani amma abincin datake bani shima wani abunne.
Hannuna na kalla wanda aka ɗaureni da sarƙa zuwa jikin ƙaramin gadon dayake ɗakin,to wai tukunna ma nan inane. Gidane mai kyau amma ba kowa a ciki,ko a wanne garine wanne ƙarnine oho.
Jan jiki nake na isa bakin window gidane mai kyau sosai, amma ginin na É—an dane . babbane sosai kuma bakowa,ko ihu zanyi baza'a gane ba.
Wani hawayene ya zubomin kan kuncinah. Ƙarar buɗe ƙofar naji hakan yasa na juyah da sauri,nasan ma wacece tazo....
Ga mamakina wazan gani ya shigo,hajiyah Mammah ce itada kaltum. Wani murmushi tayimin kaman na matar arziƙi,ja da baya nake harna danganta da bangon ɗakin. Ƙirjina banda bugawa babu abinda yakeyi.
"Ohh kinsanma mai kikayi kenan,tunda daga shigowa har jikinki ya fara karkarwa,bansan ke wacece ba inata nemanki,sai gashi kin nunamin kanki da kanki a ruwan sanyi. Kece makasudin karyewar komai nawa,kama daga rushewar ƙungiyata,yaron dana tsana nake son yabi duniyah,shine kika zauna dashi a matsayin miji harda yaro koh?".
Kujera kaltum ta miƙomata ta zauna tana yiwa Sumaimah kallon ɗan tsako.
"Yanzun zaki faÉ—amin inda kika saka kwalbar da kika É—auka kokuma saina miki abinda nayiwa wacce ta gabaceki tukunna"
Kimm Sumaimah tayi da taurin zuciya ga ido a soye tana kallon hajiyah Mammah,vatace komai ba amma kana ganinta kasan batada niyyar yin magana.
Abinda kaltum ta azabtar da itah ta nuna mata,kuka ta saka tana shashshafa jikinta.
"Bazaki samu abinda kike nema ba har abada."
"Nikuwa zan samu,kinsan harda na nuclear information É—in zaki bani,shi ya manta mai yasameshi a baya,amma keda kike matarsa nasan bazaki gagara sani ba. Zaki ce in inaso na kasheki,amma karki manta nasan raunin mu mu mata......kaltum shigomin dashi"
Tana faɗin hakan Kultum ta fita sai gata da sayyid ta riƙo hannunsa,yaron sai kuka yake yana ƙiran deeja,idonsa cabb da hawaye.
Deejah ce ta shigo wani ƙaton mutum ya hankaɗota ɗakin itada inna larai,dukkansu jikinsu ya baci ka shatar duka.
Zaro ido Sumaimah tayi tareda jan hannunta wanda yake É—aure,jikinta yana rawa ta kalli hajiyah Mammah tana jijjiga kai.
"Karki tabamin ahalina,kada ki kuskura ki tabamin ahalina,su basumiki komai ba,ki barmin su"
Kuka take tana fincikar hannunta zata isa wajenda su Deejah suke.
Dukkansu sun nuna alamar tausayi banda Deejah wacce ta haÉ—e rai tana hararar hajiyah Mammah.
"Meyasa kika yiwa Anty Sumaimah haka,mai tayi miki zakiyi mata haka. Uhmmmmmmm(taja numfashi tareda rufe ido).
Baƙin ruhi,ke baƙin ruhi ce,sannan kuma kina amfani da baƙin ruhi......yana kusa ina jiyishi,kin haɗa ruhinki dana Jinsin nas'ass(jinsin aljanune rabi mutum rabi aljani). Mayaudara kana marasa amana"
Bayan ta gama bayanin buÉ—e idanunta tayi ta kalleni. Nasan mai take shirin yi dan haka nayi mata magana.
"Deejah mai kike haka,kada ki kuskura ki koma gidan jiyah,bayan wahalar da kika sha muma muka sha,ban yadda ki koma wannan rayuwar ba"
"Ba komawa zanyi na,tarayyar danayi dasu na tun ina yarinya ne,duk da mun rabu dasu tunda na zabi mutane akansu,amma hakan bashi ya hanasu yimin alƙawarin taimako daya sashi jinsunsu ba. Karki hanani,bake kaɗai suka taba ba,sun tabamin sayyid wanda bazan iya haƙuri ba,yanzunnan zan dawo,zan arawa Harƙeelah jikina na wani lokaci. Kada ki damu tanada mutunci,itace ta cinye kazar inna rammah"
Tana gama maganar tayi Murmushi,kallon mu tayi ta kalli Hajiyah mammah ma kafin ta rufe ido..
Yin hakan keda wuyah ta ta faÉ—i a wajen kaman matacciyah.
"Mai take aikatawa,harƙeelah badai .......aljanar daji bace"
Zaro ido hajiyah Mammah tayi tareda zare wuƙah zata cakawa Deejah,ganin ta tura mata tsafi amma yaƙi cinta.
Ihu nayi tareda runtse ido na,shikenan zata kasheta shikenan........
Jin shuru ne yasani buÉ—e ido,Abbah nagani ya riqe hannun hajiyah mamman,idanunsa sun kaÉ—a sunyi jajur. Bayansa neelah ce,yah Musbahu Ahmad da kuma su Sameer. Iyah Fatee ce kawai babu saisu inna ladiyo da ummi.
Wani daÉ—ine da fatan nasara ya jiyarceni,saidai me.

SADI-SAKHNA ce
09035784150

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...38...
Chapter 46 · 0% Book details