← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 48

Sashe 28

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunana Maryam A.M Abubakar Rimi,ni kaɗaice ɗiya tall a wajen mahaifina mace,sai ƙannena maza guda biyu.
Duk da yanda na faɗamiki wannan muƙami da mahaifina keda shi,amma sam mu a wajenmu tamkar da babu yakene,domin bamuda yawan haula na dangi,ga mahaifiyarmu ta rasu a haihuwar Mujaheed ƙanin Taheer,tun bayan rasuwarta abbanmu bai ƙara aureba,haka ya zauna dagamu saishi sai kuma Wata mai kuladamu Anty Mommy.
Cikin kaɗaici muka tashi da rashin iyaye,domin abbammu baya zama a gida,saboda babban muƙamin daya samu a ƙarancin shekaru,sannan aikine na sojoji,shiyasa baya zaman gida sosai. Domin wani lokacin sai yayi sati uku ma baya ƙasar.
Rigima irinta yara duk bamuyi shi ba,koyaushe daga makaranta sai makaranta,in kinganmu a gida to da daddarene.
Ta inda Allah ta taimakemu shine da muka samu nanny mai mutunci da kuma tausayi a garemu.
A haka kwanci tashi cikin wanann halin har nayi graduation a secondry,lokacinne kuma aka kai Taheer makarantar sojoji bayan ya gama juniour school,shikuma Mujaheed yana jss one.
Kasancewar inada ilimi sosai mashaallah,kuma dama tsawon zamannawa a gidannamu karatu kawai nakeyi har na girma nayi wayo.
Saina roƙi abbanmu akan yabarni na tafi law school,bai hanani ba,hasalima yaji daɗin hakan sosai.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shiryamin komai da komai na tafiya law school a nan abuja.
Kasancewar abbah baya zama sosai,kuma yanzu na tafi makaranta,kuladani zayyiwa anty mommy wuya,sai abban mu ya tamƙa kulawata a hannun Gen Hammah,wanda shine mataimakin abbanmu,duk da cewar yafi abbanmu a shekaru,kaman yanda na faɗamiki ɗaukaka ce tasameshi a ƙarancin shekaru.
Abbah Hamma a lokacin yanada Æ´aÆ´a guda biyar,akwai Muhammad,sai Aliyu sai Aina'u,sai Mariyah da Zainab.
Muhammad shine babba,kuma ɗan hajiyah Fatima,ƙanwarsa ɗayace Zainab.
Saikum Aliyu shine mai ƙanne biyu,Aina'u da Mariyah,su kuma ƴaƴan hajiyah Mammah ne,kuma itace amarya a wajen Abba Hamman.
Zaman lafiyar dana gani a gidan farkon shigata da kuma yanda yaran suka tashi abune da zai burge duk wanda yagani,musamman ma irina da sukayi rayuwa da ƙaɗaici da rashin iyaye.
Bayan shekara Biyu da fara makaranta ta,abbanmu ya ɗebe Taheer da Mujaheed suka koma England da zama,babu yanda banyi ba akan ya tafi dani,amma firr yaƙi,a cewar sa ina mace bai kamata na bishi ba musamman da lokacin karatuna yafara ɗan nisa.
Haka dole inaji ina gani na hakura suka tafi,wanda kuma nasan bazai wuce da saka hannun Hajiya Mammah ba,don lokacin dana fara zuwa gidan ta jani a jiki sosai,amma ni ban fiya shiga sashenta ba,saboda bama shiri da Aina'u,nafi shiri da zainab. Ita kuma mariya lokacin ƙarama ce.
Kayana na tattara daga hostel na koma gidan Abbah Hamma da zama,hajiyah Mammah taso na zauna a sashenta amma naƙi,badan komai ba saidan abu biyu,. Na farko Banason faɗan da muke da Aina'u,duk tsiya ita gidansu ne,bai kamata ace nazo ina faɗa da ƴar masu gida ba kullum,sai kuma magana ta biyu Aliyu yana sona,nikuma har sannan ban bashi amsa ba gaskiya,bazance bana sonsa ba,bazan kuma ce ina sonsa ba,irindai kaji mutum yana burgeka amma ba so ba.
Saidai shikuma a nashi bangaren soyayya yake nuna min a gaban kowa,hakan sai ya fara takurani,shiyasa na sauƙa a sashen hajiyah Fatima dana dawo gidan da zama.
A tsawon dawowata gidan bamu haÉ—u da Muhammad ba,saboda shi yana England wajen abbanmu a can yake aiki a wajensa,yawanci mutane ma cewa suke shine mai gadon abbanmu a wajen aiki,domin yasha cewa Abbah Hamma ya bashi shi,saidai kawai yayi dariyah.
Bayan shekara huɗu da fara makaranta ta Allah ya kawomu gamawa,a lokacinne na roƙi abba yazo shida ƙannena dukka.
Duk da cewar dama yana xuwa wani lokacin,kokuma in anyi hutu nina je,amma hakan baikai a ce dominni zasuzo ba.
Tareda dukka gidan aka haÉ—u ana tayani murna da kuma shirye shiyen gamawar tawa.
Zuwa lokacin na zama Æ´ar gida sosai,tun inajina tamkar ba É—aya daga cikinsu ba,har yazamto yanzu in ba mutum yasani ba bazaice niba Æ´ar gidan bace.
Sauri nake hadda gudu gudu na nufi Wajen Zainab,saboda ance min ta karbo mana dinkinmu da zamu saka.
Jinayi na bugu da mutum,ɗagowa nayi muka haɗa ido da Muhammad,ƙifta ido nayi shine kuwa,kuma fah shine.
To ko su Abbah yabiyo shima domin zuwa murnar gama makaranta ta kai,kai anya kuwa.
Mutum ne shi mai sauƙin kai da kuma mutunci,amma fah akwai miskilanci dayin sha'aninsa daya shafeshi,bai fiya shiga harkar mutum ba in bawai an tsoma shi ba.
"Ahh yah Muhammad tare kuka......."
Tun kafin na gama maganar ya ɗagamin kai yana murmushi,nasan ba lallai yabani amsa ba,murmushin shine amsar,kai mutuminnan yana bani a jikina,duk sanda na ganshi rasa nutsuwata nakeyi da kuma guntun hankalina. Duk da ma saina ɗaga ido nagano shi,saboda yanada tsawo,nikuma ga ƙanƙantar jiki kaman ruwan aski.
Daƙyar na janyo ganina daga kansa na rabashi na wuce zuwa wajen abba nah da ƙannena,nabar batun ɗinki tunda naji ance sun iso.
Da tsalle na faɗa kan abban ina kuka,wanda kowa yasan na farincikin ganinsa ne,a tsaye suka a ƙofar gidan da Abbah Hamma,ina jinsa yanamin dariya sai sakaliya,nidai shuru nayi,Allah yaga ai ina ƙoƙari,ace mutum yana rayuwa wai kuma ƴan uwanshi suna wani wajen daban.
Gaisawa mukayi da sauran Æ´an uwannawa, kafin daga bisani muka shiga ciki anata murna.
Mun zo shiga cikin gidan naji zainab taja hannuna zuwa garden,tambayar ta nake mai yake faruwa amma sai jana take tana dariyah.
Bayan mun isa sakinta nayi tareda buÉ—e baki saboda mamakin abinda nagani. Da balloo akayi amfani wajen haÉ—a sunana da kuma murnar gama makaranta ta..
Abin ya burgeni matuƙa,har bansan lokacin da yah Aliyu yazo inda nake ba.
"Ina miki murnar gama karatunki maryam,sannan kuma dan Allah a yau É—in ki karbi so........."
Tun kafin yagama naji mai zaice zainab tazo akan wai ana kirana a cikin gida,da alama sun gama shirya walimar kenan.
Haka na juya batareda naji mai zaice ba nabi bayanta.
Riga ta da aka ɗinka saboda ranar,babu taron mutane sosai,amma wajen yayi kyau babu magana,a dai irin dai zamaninmmu kam abin ya ƙayatar.
Bayan an gama komai magana abba nah ya farayi,ganin yanada muhimmanci sosai yasa dukka kowa yayi shuru domin muji mai zaice.
Bayani akan murna da kuma farincikin gama makaranta ta,sannan ya miƙa gaisuwa ga Abbah Hamma,bisa rikeni dayayi amana har zuwa lokacin.
Bayan nan kuma hannun Abbah Hamma ya riƙe kaman mai shirin roƙonsa wani abun,abinda ya faɗane yasaka dukkan mutanen wajen zare ido,bama kamanni da kuma zainab da Aliyu.
"Abokina komai dana roƙeka kayimin harda wanda banyi zato ba,samun amini irinka sai an tona,nagode nagode da karamcinka a gareni."
"Haba Abbakar miye kakeyi hakane,a tunanina kaman mun wuce wannan abin an zama É—ayah."
"Ehh to in hakane,ina neman alfarmar kabawa É—ana Æ´ar taka mana aure"
Abbana yafaÉ—a yana nunani da kuma Muhammad.
Dukka wajen kowa shuru yayi cikeda mamaki,amma babu wanda yace komai ana jira aji ta bakin Abba Hamma.
"Indai hakane babu matsala na bawa Muhammad Æ´a ta Maryam,Allah ya sanya alkhairi a aurensu ya basu zuri'ah É—ayyaba. Kenan itama zaka janyeta can wajenka koh"
Dariyah abba nah yayi tareda cewa,
"Ba komai saina bar maka Taheer anan ai,dama shine mai son yin aiki anan"
To shikenan abu yayi kyau Allah ya ƙara haɗa kanmu dana ƴaƴan mu."
Haka taron ya ƙare,wasu yayi musu ɗaɗi,wani yayi musu bazata,yayinda Aliyu shida hajiyah Mammah da ƙannensa duniyar tayi musu duhu,yazamana gani suke tamkar an ware sune a rayuwar gidan. Amma banda Aliyu,shi abinda yasakashi cikin wani yanayi ganin yanda soyayyarsa ta subcene akan idonsa,kuma hakanma ba mallakin kowa nake shirin komawa ba sai dan uwansa na jini.
A bangaren hajiyah Fatima itama taso ƙin amincewa,saboda ta kulada Aliyu yana sona,amma kuma batada ikon hakan musamman ma da su Abbah sun riga sun yanke hukunci,nima kuma a lokacin naso kaina,ban kulada halinda Aliyu zai shigaba,nabi zabin zuciyata wato Muhammad ɗin.
A ƙurarren lokaci aka saka bikin,sai murna nake zan koma kusada mahaifina da zama,shikuwa Muhammad da akayi masa zancen babu yabo ba fallasa ya amince.
Shirye shiryen biki aka fara,inda a ranar wata juma'a aka ɗaura aurenmu nida Muhammad. Aliyu bayanan aka ɗaura auren,a cewarsa an turashi aikine ƙasar spain,amma a zahiri kuma shine da kansa ya cika neman aikin saboda yayi nesa da gida,a lokacin danaji ance zai tafi ana gobe ɗaurin aurenmu naji tausayinsa sosai,saboda ni shaida ce irin son dayakemin. Amma kuma bazan iya tsaidashi ɗin ba saboda banada abinda zan bashi,kai na kokuma wata soyayyar,babu mai yiwuwa a ciki.
Wanda suka san soyayyar da Aliyu yakeyimin haka suka manta,aka cigaba da hidimar bikina.
Bayan an É—aura auren bamu tafiba sai a washagari tukunna..
A lokacin nafara kunyar hajiyah Fatima da kuma Mammah,ganin da gaske fah matsayina ya sauya a gidan,nazama surukarsu.
A daren mun É—au lokaci da tsawo muna kuka nida zainab,ganin da gaske fah rabuwa zamuyi na tafi.
Kyauta mai tsoka matan gidan sukayimin,harda Abbah Hamma ma. Tareda Mujaheed muka tafi,aka bar Taheer anan.
Shikuma Abbah da mijinnawa jiya suka tafi,akan za'amin cuku cukun wajen aiki da kuma cigaba da karatu.

(Ba anan gizon yake saƙaba,nan hasken dana samu a rayuwata kenan kafin duhu ya lullubeni wanda bai yaye ba daga duniya ya har yau)

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...21...
Chapter 28 · 0% Book details