← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 48

Sashe 35

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duka da naushi Ahmad yake kaiwa Gen Buhari Bello,shima ramawa yakeyi kasancewarsa tsohon soja,ga Don 3 ya buge bindigarsa tun É—azu.
Ganin faÉ—an ya É—auke musu hankaline yasa don 3 É—auke wayar Gen BB ya fita.
Sun daÉ—e suna faÉ—an kafin Ahmad yasamu nasara akansa,ta hanyar É—aukar bindigar tasa,saita shi yayi da ita yana haki.
"Miye alaƙarka da wannann kungiyar,dama tsawon lokacin nan amanar sojoji kake ci,irinkune kesa a dunga yiwa jami'an tsaron ganin marasa gaskiya koh.......(kwafɗama sa ƙasan bindiga yayi saida ya faɗi)........kaine don 2 to wanene shugaban ƙungiyar,inaso ka faɗamin yanzunnan kokuma na jajjage kanka da bindigar nan"
Cikin ƙaraji da tashin hankali yake maganar.
Wata dariyar baka isa ba gen BB yayi wa Ahmad,cikin sauri yasaka ƙaramar wuƙa ya yanke wuyansa da itah,yana kakarin mutuwa Ahmad ya jefar da bindigarsa ya ƙarisa wajensa da sauri.
Tallafoshi yayi a razane,ga jini yanata zuba a wuyansa,abin har yakai ya kashe kansa akan yafaɗa masa wanene shugaban ƙungiyar nan?
"Yaaa....rrro kenan,mai amfanin na faÉ—amaka tunda nasan dama mutuwa zanyi idan ta gano kasanni........bazaka taba sanin wacece itttt.......ba"
"Dama macece ka faÉ—amin, wacece w......"
Shuru yayi tareda sakinsa ya koma gefe,ganin ya riga ya mutu,abin yayi matuƙar razana shi sosai.
Wayarsa ce tayi ƙara,hannunsa yana rawa ya ɗauka ganin Eemran ne.
"Hello sir mungama dasu,saidai wannan shugabannasu mun sameshi yana waya da wani"
"What definitely shugabarsu yake faÉ—awa mai ya faru"
"Eh nima nayi tunanin haka,na harbeshi a kafaÉ—arsa da dama"
"Ohh yakamata mu tafi,abin bai tafi yanda ake so ba,amma dai Alhamdulillah hakan ma mukeda nasara"

∆∆∆

"Ina jinka ka faÉ—amin mai yake faruwa a wajen Gen?"
"Hajiya an samu matsalane ba Ogah bane,Goje ashe sojane yayi mana baɗɗa kama,yanzu haka ya gane ogah kuma ya kamashi,na samu wayarsa ne na ƙiraki"
"Wayeshi ka faÉ—amin"
"Gen ........"
Kafin yaƙarisa aka katse ƙiran,kuma da alama harbeshi akayi don taji ƙarar bindiga.
"Waye ka faÉ—amin wayeeeeee......"
Ƙara ta saka tareda yin wurgi da wayar, kaltum ce ta tsugunna ta ɗauke wayar jikinta yana rawa.
Kallon fuskar hajiyah Mammah nakeyi,idan ka ganta zakace bazata wuce shekara talatin ba a duniya,babu wannan sunkuyawar da yamutsewar fuskar.
Mamaki abun ya bani,mai ta shafa haka ta sanja lokaci guda.
Masifa tacigaba dayi tana zuwa tana dawowa,ganin abin bazai mata ba ta jawo wani akwati a ƙarƙashin gadonta,ja ne yana glowing,kana gani kasan abun tsafi ne.
Hannunta ta saka ya buɗe,wani aljana ce ta bayyana a gabanta da baƙaƙen kaya,kamarsu ɗaya da itah,amma kana gani kasan ita ba mutum bace,to wacece kenan.
Jikina rawa ya fara daga inda nake labe da jikin ƙofa ina leƙawa,dan karfin hali bana tsoron ma ta ganni.
"Ruhina inaso kayimin bayani shin mai kasani gameda abinda yake faruwa,ƙungiyar dana kafah wadda da ita nake control na manyan ƙasar nan ta rushe,mai yasa abubuwana suke rushewa"
Muryarta da bibbiyu take fita kamar wata na'urah.
"Hakan dama dole zai faru,tunda dodo ya baki kashedi akai,matar da kike gudun kada ta bayyana harta haifi magajin wannan matakin tariga ta bayyana,kuma itace sanadiyyar karyewar alƙalaminki,indai ba kasheta kikayi ba to bazaki ƙara nasara ba"
"Kaman ya yarinya,ni banga kowa a tareda shi ba,Mulaifah ce itama kuma yanzu sun rabu"
"Hhhhhhhh duk da a zahiri kina kulada yarintarki amma hakan baya aiki a hankalin ki,shiya riga ya tsufah"
"Ruhuuuuuu karki ƙara magana akan tsufah na,bazan tsufah ba bazan taba tsufah ba,wannan fatar tsufan ina nuna ta ne kawai da iyalaina,suma in suka isheni dukka zan gama dasu nayi rayuwar ƴan ci na"
"To inba haka ba mai yasa kika kasa gane cewar Ahmad yayi rayuwa ba'a gabanki ba na tsawon shekara shida,bai kawomiki anan ya gamuda itah ba,sannan kuma yayi rayuwa a cikin ƙungiyar da kike karewa. Sannan ya bar mata da kuma ɗa a rayuwarsa ta baya.......munkasa gane hakanne a da dayake ta Addu'a a lokacin,yanzu dayake kan aikin ruguza ƙungiyarki bayayi sosai shiyasa muka gani......amma duk da haka bamuga hoton madubin rayuwar ba har yanzu"
Jikin hajiya Mammah rawa yafara bakinta yana fitar da wani hayaƙi,ganin Kultum zata fito yasa nayi saurin barin sashen nima nawa jikin yana rawa.
Me suke nufi,kenan nida É—ana mune sanadin karyewarta a yanda ta yarda,in hakane to kuwa muna cikin hatsari,sannan dole kada tasan koni wacece, matar nan ta wuce yanda nake zato.
Ina cikin tafiya ina tunani naji na bangaji mutum,saurin dawowa hankalina nayi tareda kallon Fatee.
"Ke ina kike gani haka, kaman wata sabuwar makahuwa,kije mommy tana nemanki "
Daga haka ta wuceni tana karairaya,nidai binta nayi da ido kafin na wuce sashen hajiya Maryam.
A zaune na gansu itada Neelah suna magana,ita kuma yaushe ta dawo,da alama yaune.
Saida na giashesu kafin na zauna a akan kujerar,Neelah ce ta kalleni tareda cewa.
"Miye ya faru haka Sumaimah naganki kaman wacce taga fatalwa,ko kema kinji labarin nasarar da Ahmad yayi akan ƙungiyar BC?"
"Uhm yayi nasara amma kuma yasake buɗe ƙofar gane shirinmu,domin a yanzu haka hajiya Mammah tasan da labarin yayi rayuwa a cikin ƙungiyar BC,kuma yanada ɗa da mata,duk da batasan sunanmu da fuskarmu ba amma nasan bazata zauna ba saita gano hakan"
Abinda nagani a É—akin hajiyah Mammah na sanar dasu,duk da basu wani razana ba,amma sunyi mamakin yanda takai har haka a shu'umanci.

Mun daɗe muna tattauna,wanda duk yawanci gargaɗi hajiyah Maryam takemin akan nayi taka tsantsan, lamarin,tunda yanzu yafi nada muni,ga zaman dazan ƙarayi a sashen hajiyah Mammah,domin inkana son kama damisa dole saika shiga sansaninsa.
A ranar Ahmad yadawo daga yankinnamu,anyi murna sosai da nasararsa ciki kuwa harda hajiya Mammah,kaman ba fadarta ya ruguza ba. Musamman A.M Aliyu ba ƙaramin farin ciki yayi ba da nasarar. Ana ta murna amma bandani,domin wajen zamannawa na kullum wato lambu na tafi na zauna. Zuciyata nason ganin Ahmad domin nayi kewarsa sosai,amma kuma ina tuna kashedin da yayimin na cewar kada na kuskura nasake nuna fuskata a gabansa.

∆∆∆

Bayan sati ɗaya da wannan nasarar da gen Ahmad yasamu nutsuwarsa ta ɗan dawo ba kaman da ba,saidai duk da haka yakasa tsintar kansa da jin komai ya ƙare. Koda yake dama yasan akwai sauran rina a kaba,tunda har yanzu bai kama shugabar ƙungiyar ba,amma tunda yasan macece yanzu zarginsa kashi tamanin a cikin ɗari yana kan hajiya Maryam ne,don abinda yake kwanannan kenan saka mata ido na shige da ficenta,domin ya kula tashiga cikin tashin hankali da abinda yafaru,sannan ta tsiri zama cikin busy.
Biron hannunsa yake dannawa yana É—agoshi,duk da hakan akwai wani abun da babu.
"Ohhh that girl why....meyasa nake missing É—in matar wani,kaddai na fara son matar da bazata taba zama mallakina ba kai,ahah no ba sonta nake ba,inajin haushi ne da kuma zunubin abinda na aikata mata"
Cije cije yake yace wancan yace wancan shi kaÉ—ai,a iya sati guda daya wuce gabaÉ—aya yaki ko gidan baya son komawa,domin yana shiga zaiji yana so ya ganta,wanda kuma yasan bazai gantan ba,shida kansa ya bata umarnin kada ya sake ganinta a inda yake.
Kai inaga barin ƙasar zayyi naɗan wasu watanni ko zaiji daɗi,dama abbah yabashi hutu tunda yasamu wannan nasarar.
Yana cikin wasiwasinne Eemran ya shigo office É—in.
"Eemran kayimin arrenging na zuwa hutu gobe"
"Ogah anya kuwa hakan zayyi wu,don an fitar da aiki daga headquater,kuma naga hadda kai a cikin wanda zayyi supervising"
"Supervising É—in me"
"Uhmm a cikin trainee ɗin aka dauka masu ƙwaxo zaku tafi dasu Russia na tsawon wata Uku"
Komawa jikin kujerar Ahmad yayi tareda sakin dogon numfashi.
"Yaushene tafiyar?"
"Gobene ogah"
"Ohk"
Abin yabawa Eemran mamaki,yayi tunanin zaice bazai jeba,amma saiyaji sabanin haka,kenan so yake yabar garin kota wacce hanya.
Washagari bayan an gama tsara zaman sojojin a jirgi sun tafi kafin manyan suka bisu a private jet,duk cikinsu Ahmad ne kaɗai ƙarami.
Lokacin dazai taho ko Æ´an gidan bai fadamusu zai tafi ba,iya Neelah ce kawai tasani sai Saleem.
Masauƙinsa aka kaimasa kayansa, bayan ya watsa ruwa yasaka riga marar nauyi ta shan iska.
Fitowa yayi wajen cin abinci,amma shi a hadene da sauran ƙananan sojoji.
Bayan ya zauna an saka masa abinci,har zai fara cin abinci yaga wani yazo ya zauna a opposite É—insa,mamaki abin yabashi,dan yasandai baizo dasu Eemran ba bare su zauna.
Ɗagowa yayi suka haɗa ido da wani matashi,zaiyyi shi a haife,kallon rashin sani yake masa,amma kuma sai yaji kamar ya taba ganinsa. Shima kallonsa yake ko ƙiftawa bayayi,sai can kafin yace.
"Goje mai kakeyi a nan,bayan batanka kaima soja ka shiga,amma meyasa baka faÉ—i inda kake ba,kasan kuwa halin da Sumaimah tashiga a sanadiyyar rashinka?"
Maganar da bawan Allahn yayine ta dakeshi da ƙarfi,zaro ido yayi tareda ajiye cokalin yana kallonsa.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...28...
Chapter 35 · 0% Book details