← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 47

Sashe 9

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ƙarar jiniya naji na ƴan sanda,ina jin su Tunga suka tashi tsaye,so suke nace musu mu tafi kaman koyaushe,saidai yanda na jingina da jikin katangar banason na tashi.
Muryar DSP ce ta ziyarci dodon kunnena,hakanne yasaka ni dagowa na kalleshi.
"Goje abubuwan da kake a garinnan kare bazai ciba,dan haka ka biyomu ofishimmu yanzunnan kaida yaranka,dolene ka fuskanci hukunci,sannann kuma ka biya tarar mutumin daka buɗewa ciki. Babu wanda yafi ƙarfin doka duk shu'umancin sa"
"Hannu ɗayane kawai ya soka masa wuƙa,kuma wannan hannun na gojene,dan haka a dokance iya gojene zai biku kawai koh,don haka muje.
Kai Tunga ko zata mutu ko kuma tayi rai to a ƙaddamar,in kunji lafiya ku sama ta gora kawai"

Murmushi nayi lokacin dana shiga motsar ƴan sandan,idon DSP yayi zuru zuru,da alama ya ankare da saƙon dana aikawa su Tunga.
KishingiÉ—a nayi a cikin mota kafin a isa,har bacci ya fara É—aukata.Duk daren duniyata yanda naga ranar haka nake ganin daren,musamman ma idan na taimaki wani,kokuma wani yayimin abu ban ramaba,narasa mai yasa nake haka,shin kowa haka yake ko kuma ni kaÉ—aine tawa halittar daban.
Amma yau kam tunda nayi abinda rannawa yakeso to da alamar zan iya samun bacci.
Saida naji motar ta tsaya kafin na tashi zaune,dama bacci nake so nayi inda wadancan yaran bazasu takuramin ba,haka ma inna a gida,tunda zan kwana a wajen sai nayi ta bacci babu wani shedule a kaina.
Suna buÉ—e bayan motar na nufi É—akin danake zama idan na biyosu,babu wanda yafi doka injisu da faÉ—a,to gashi na kawo kaina amin hukunci.
Maganar DSP naji yana yiwa wani ɗan sanda da muke tafiya tareda shi,hmmm su gama abinsu ma,daga ƙungiyar BC(black cobra) sun dawo gobe da yarjenjyata ta shiga ƙungiyarsu,to bazasu sake gani na ba ma,nasan zuwa lokacin nafi ƙarfin wannan kurkunnasu,duk da yanzu ma zancen manyan garine yasaka nake biyosu,amma wannan shine na ƙarshe,shiyasa nazo nayiwa wajen bankwana.
"Kai copur wannan abinda ake yi masa ya ƙare daga yau,ku kaishi cell ɗin da ake saka mai laifi irinnasa,sannann gobe a miƙashi ga kotu,dan ƴan uwan wanda ya sokawa wuƙa sune suka kawo ƙara,kuma sunce kotu zasu kai ƙarar"
Da nayi niyyar na ƙyalleshi na wuce,saidai kuma zuciyata bazata iya ba,in ba gargaɗi nayi masa to bazanyi baccin danake mararin yi ɗin bama
Dawowa nayi da baya har zuwa inda yake tsaye,da wani tulelen cikinsa a cikin rigarsa,an bubbunka haram ciki ya nuna alama.
"DSP sambo in kana cin ƙasa kasani ka kiyayi ta shuri,babu ruwana da wata ƙara dazasu kai,abune ya haɗani dashi shiyasa nayi masa hukunci,da kunsan abinda yake muku a garinnaku ma da godiya zaku min.
Sannan da kake wani tada ƙayar baya nasan biyanka kuɗi sukayi koh? In mutum yasamu kuɗi kuma iyalansa yake tunkara dashi. To in kanaso suci wannan kuɗin cikin lumana,ƙaramin yaronnan ya dunga zuwa makaranta da ƙafafunsa,sannan wannan ta gidan kar ta haihu lokacin ta bayyi ba.
Shi dana sokeshi ya rayu bari muga in muka mata tiyatar cikinta zata rayu?....."
Cikin sigar jan kunne na ƙarisa maganar ina jaddada masa gargaɗinnawa da idanuna,aikuwa hakan yayi aiki,dan lokaci ɗaya gumin tashin hankali ya lullube jikinsa sharkaff..
Bansake bi takansa ba na nufi ɗakin dana ke sauƙa innazo,har copur ɗin ya buɗemin ƙofah.
Ai wannan mutumin dan basu san sharrinsa bane da kuma makircin daya haÉ—amin harma da garin gabaÉ—aya,dana kasheshi ma da sai hakan yafimin daÉ—i.wawaye duk a zatonsu harda ni a lalatacciyar satar da aka yi musu,sun raina aikina ma da alama.
Mutum yayi sata a garinnan ko ya kwashi tsiya,inda ma kajine ko akuyah idan za'ayi gashi da sauƙi,amma kuɗi kan basuda wannan arziƙin..
Ina nan kwance akan katifar É—akin har bacci ya É—aukeni.

__***__
Chapter 9 · 0% Book details