← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 47

Sashe 30

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan na gama cinye tuwon inanan kwance naji kursiyyah tashigo É—akin.
"Sumaimah wai kizo inji gaji kiyi wanke wanke,ko bakisan hadda kwanukan yin awara ba a ciki?"
"Kije kice mata yau baxan iya yin aiki ba banida lafiyah"
"ChabÉ—i wlh ba wani rashin lafiyah,bakida lafiyar ne zaki cinye kuma tuwon dana kawo miki? Ai wlh saina cewa gaji wai kince bazakiyi ba ne"
Tana gama faɗin hakan ta fita daga ɗakin,runtse ido na nayi lokacin da cikinnawa yayi wani danƙa kaman zai cire taciki.
Tun safe nake juye juye akan gadon,bani na samu bacci ba sai wajen azahar tukunna.
Baccin duk da yana cikeda yunwa amma yana min daɗi sosai. Kaman a sama naji sauƙar ruwa a jikina,wata ajiyar zuciya nasaki tareda tashi na zauna ina rarraba ido.
Warin kashin shanu naji a cikin ruwan haÉ—e da warin soda. Tofarwa wanda yashiga bakina nake ina tari. Har sannan ban dawo hayyacina naga waya aikatamin hakan ba,amma nasan ba maiyyimin wannan aika aikar sai gaji.
Juyowa nayi,saidai maimakon naga gajin,da fuskar kare muka haɗa ido yana min gurnani,saikuma wasu ƙafafu a tsaye. Binsu nayi da kallo zuwa sama,har idanunnawa suka haɗu dana goje,wanda ƙasumbarsa ta ƙara yawa,ga idonnan kaman na zaki yaga abin farautarsa.
Ihu nakeson yi kozan tashi daga mafarkin danake,amma kuma nasan ba mafarkin bane zahiri ne..
Matsawa nake da baya har nakai jikin gini akan gadon,tunda nasan shine ban É—aga idona na sake kallonsa ba.
Magana yafarayi da wannan maganar tasa mai diri.
"Yaushe nayi wasan dazaki rainani,shin abinda nasakaki kenan dana tafi,nace miki kada ki karya É—aya daga cikin ayyukan dana sakaki,amma wani abin takaicin ko guda É—aya daga cikinsu bakiyi ba,wato duk abinda zanyi nayi koh?"
"Dan Allah kayi haƙuri wlh"
Fizgo hannuna yayi ya jefani a tsakiyar É—akin,jikina banda karkarwa babu abinda yake,saboda razanar danayi jinina ya tsinke sai zuba yake duk ya bata kan gadon da kuma jikina,nasan yagani amma ko a jikinsa,Allah yasama yasan menene.
"Ki rufemin baki,kada ki kuskura ki ambaci wannan kalmar da na tsani jinta in anyimin laifi wato haƙuri,saboda bana haƙurin"
Since sarƙar jikin karen hannunsa yayi,da alama banni dashi zayyi ya fiffigani,aikuwa hakanne dan sunshe shi yayi yana shirin barin ɗakin.
Wani takaici ne gamida baƙin ciki suka tokare min maƙoshi,take kuwa sukayi nasarar kawarda tsoronsa dayake cikin zuciyata,yazamana haushinsa da kuma mamaki irin na halinsa sunfi gaban tsoron danakeyi masa. Wannan ba mutum bane,taya mutum zai dunga jin tsoron halitta irin wannan ma.
"Dakata kada ka fitah"
Nikaina nayi mamakin umarnin dana bashi,yaushe nasamu wannan jarumtar haka? Tsayawar kuwa yayi bai fitan ba,ba wai danna isa ne yasakashi tsayawar ba,saidan mamaki daya cikashi.
Juyowa yayi tareda ɗaga gira yana kallona,yayinda nima na ɗaga nawa idon nasaka su a nasa,saƙo nake son isarwa da ruhinsa bawai shi ba,saƙon kuma bazai kai inda nakeso ba idan ba idonsa nake kalla ba.
"Badai kasheni kakeson yi ba,idan kasheni zakayi ka kasheni da kanka,basai kasaka halittar da batayiwa Allah komai ba ɗaukar rai,Naga abubuwa da yawa a rayuwata sannan duk da banda galihu a duk ina naje,amma hakan bashi zai saka nakasa tsarewa kaina darajata wanda Allah yabani na ƴa mace. Bana fatan labarin mutuwa ta ya yaɗu cewa karene ya yayyagata a ɗaki har ta mutu,gwanda mutane suce mijinta ne ya yankata,wanda bai san cinta ba,baisan shanta ba,baisan ya ta kwana ko ta tashi ba,dabbarsa ta fita daraja,Dan kawai yayi tafiyar da bata san ya tafi ba,yadawo yaga batayi aikin daya sakata ba,bai tambayi dalili ba kawai sai ya yankata. A wannan tafiyar bai ajiye mata abinci ba ko kuɗin magani,sannan bai bata izinin tafiyah ko ina ba,shin dutse ya ajiye kamai,saniyar sa ya damu da itah akan a bata abinci,amma matar da ajiye ko oho. Duk da hakan tayi iya koƙarinta wajen ganin cika umarnin daya bata,amma ƴan gindasu sunƙi barinta ta cika ɗin,shikuma bai biɗi sanin daliliba hukunci kawai ya iya zartarwa na son kansa."
Kukane ya kufcemin na abubuwan da suka faru a gidan wanda suka dawo cikin kaina.
"Indai wannan rayuwar ce mai kamada ta bautar mutanen farko to wlh ka kasheni goje bana tsoro,duk hukuncin dazaka min na daɗe da sanin kwatankwacinsa,kaya da kake faɗa kuma ƴaƴan gaji ne suka zuba a kewayen saniya,na kasa wankewa ne saboda hannyena ciwo ne dasu......bazan iyaba ka ɗau raina kawai kaman yanda kake iƙirari ko yaushe,ka ɗauka kawai na huta,dama tunda nake mai na tsinta na farinciki a duniyar ne??? Kullum zullumin mai zai faru. In baka kasheni bama yunwar cikina zata kasheni,gaji bazata sake bani abinci ba nasan,saboda bazan iya yimata aikin da innayi take bani ba. Dan haka ni gwanda ka kashenin ma kafin yunwar da kasheni"
Rarrafawa nayi na riƙe ƙafar wandonsa,har raina ni na gaji da wannan zaman rayuwar.
Jikina karkarwa yake na wuyah,dakuma kukan danakeyi,karen dayake gefena sai gurnani yake,amma ba tashi nake ba,na daina ma tsoronsa,mai jiran mutuwa wanne tsoro zaiji ne"
"Tashi .....ki tashi nace"
Abinda yakeson nayin nasan bazan iya ba,amma barina gwada nagani.
Miƙewa nayi daga rarrafen inaso na tsaya akan ƙafata,wani juuuuu jiri yaɗebeni,kafin idona ya rufe sai naji ni a hannun mutum ba tsakar ɗaki ba.

Nauyi idanuwan sukayimin,amma haka na dage na buɗeshi,akan farin cilin idonnawa ya sauƙa,fanka tanayi walwal a samana.
Gefe na kaikaita kaina na kalla,window nagani na glass ga kuma farin fenti,tunani na fara na shin a ina nake ne.
Yunƙurin tashi nayi sai naji hannuna a ɗaure,hannayen na kalla duk an ɗaɗɗauresu da bandeji,da alama magani aka shafamun to waye yayi min.
Allura na gani a É—ayan hannun wata igiya tayi sama ruwa yana shiga jikina,Asibitine wai??
Na tambaya a raina,gyaran murya naji hakanne yasa na kalli mutumin dayake kan kujera a zaune,tun É—azu yake kallo na ban kulaba.
Ƴar razana nayi ganin ya kafeni da ido.
"Meyasa kika taba abinda kinsan jikinki bayaso?"
"Soda ce"
"Ban tambaye ki menene ba,cewa nace meyasa kike amfani da itah,bayan kinsan jikinki bayaso,Tunga ya faÉ—amin cewar yabaki dubu biyu,mai kika siya toh?"
"Uhm na ajiye banganshi ba,wanda na siya kuma......"
"Ƴaƴan gaji sun sace,sannan sun ɗauke wanda kika siyah"
"Uhm"
"Sannan kayana ma sune suka saka a wajen saniya"
Nan ma É—aga masa kan kawai nayi,tunda hakanne kuma ya riga ya gane.
"Wajibine na gyara saitin gidannan,ke kuma kina zaune suka miki hakan ke ga asararriyah koh?.tunda kin tashi barina je na dawo,ga nan abinci a gefen gadon kici ki gyara jikinki zan dawo na maidaki gida inna gama abinda zanyi"
ÆŠaga kai nan ma kawai nayi,
"Bakya magana ne,É—azu ban tambayeki ba kikayi da faÉ—i ba'a tambayeki ba,yanzu kuma kinkoma kurmiyarki"
Daga haka cikin tafiyarsa ta isashshe ya fita.
Mamaki ne yakamani anya kuwa ba mafarki nake ba,wai asibiti ya kawoni?"
Ledar daya kawomin na buɗe,maltina ce a ciki da kuma peak na madara,sai magani a ciki. Ɗaya ledar kuma indomie ce aka soya ta da ƙwai.
Toh ikon Allah....Sumaimah zataci daÉ—i kenan..
Nafaɗa a raina bansan sanda murmushi ya ƙubcemin.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[20]
Chapter 30 · 0% Book details