← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 47

Sashe 20

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikeda borin kore kunya ya kaÉ—a rigar sa yabar gidan,amma kana ganin fuskarsa kam kasan abin ya dameshi.
(Hmm baka ga komai bama)
Ammi tana shiga ƙofar tasu taji ihun inna rammah a ɗaki.
Ƙarisawa ɗakinnata tayi da sauri dan ganin mai yafaru.
Leƙawa tayi ta samu aljanar da aka ƙira da Deejah ta kafa haƙoranta a cinyar inna ramm,irin wanda tayiwa kazarta ɗazu.
Ammi ce tashiga É—akin ta janye ta daga jikinta,jini sai zuba yake a wajen.
"Wayyo na shiga uku,cinyeni zatayi nima kaman yanda ta cinye kazata,wlh bazan zauna ba uwaisu ya kawo abinda zai halaka ni ya halaka Æ´aÆ´ana"
A bangaren Deejah kuwa ammi tana banbareta daga jikin rammah ta koma kan gadonnata tasake kwanciyah luff kaman ba ita tayi ba.
"Rammah mai kika mata ta cije ki?"
"Ammi ganemin wannan masifar,tace a ɗakina zata zauna na kawota,wai kawai dan taga ɗana akan gado saita jefoshi.Aradu badan na cafkeshi ba a ƙasa zai faɗi,haushin hakanne yasa na mareta,aikuwa tafara wannan gurnanin,wai ba'a dukanta,kannaceme naji ta maƙare a jikina tana yakushi na. Muna haka zanina ya kunce,tana ganin cinyata ta gasa min cizo.Wani zafine ya jiyarceni shiyasa na zuba ihu. Dan Allah Ammi ki taimakeni na fitar da ita a ɗakina"
Deejah tana jin abinda rammah ta faÉ—a ta É—ago idonta.
"Idan kukayi yunƙurin ta'bani saina bunkawa ɗakinann wuta na babbakeshi,ke kuma idan kika sake shiga in muna fada to ɗakinki zan koma da zama. Zanyi bacci kafin na tashi ku sama min abinci,idan ba haka ba kaza ta gaba ce abincin na,sannan duk ɗan daya shigo ina bacci saina karya ƙafarsa".
Tana gama faÉ—in haka ta koma ta kwanta.
"Kinji koh ammi dan Allah........"
"Ahah dakata bakyajin abinda tacene,ko bakiga yanda tayiwa kazarki ba kai,bazaki É—au darasi daga haka ba. Ni kinga tafiya ta ba dani ba.
Takaicine ya ishi rammah,hakanne yasa ta fito filin ƙofar tasu tana safa da marwa,burinta kawai uwaisu ya shigo gidan ta direshi da masifah,a jima ta leƙa ɗakinnata,duk sanda ta hango Deejah a kwance tana birgima akan gadonta sai wani takaici ya jiyarce ta.
Tun tana tsammanin jiran uwaisu shuru shuru har yamma tayi,bata manta ba kuwa yana shigowa tasha gabansa.
"Allah ya shigo dakai,maza kasan yadda zakayi ka fitarmin da waccar halittar daga É—akina,dan wallahi bazan zauna da itaba,saidai na bar gidannan akan haka"
"To yanzu ykk so nayimiki kenan,shigowata kenan tun fitata,baki bani abinci ba kuma kece da abinci"
"Abinci zancen abinci ma kake kenan,to ni tunda ka kawo wannan masifar ko ruwa ban saka a bakina ba,kanace wasa nake koh,koka fita da ita kokuma nayi gidanmu. Kalli inda ta cijeni fah har yanzu jini bai tsaya ba"
Masifa rammah take kan gari ya gari,akan koya fitarda Deejah a É—akinta kokuma ta tafi gidansu.
Ganin abinnata bana sanyi ne nan kusa ba yasa uwaisu ƙirna mazan gidan akan su fito da Deejah a cikin ɗakin.
Ubaidu aka ƙira yaran gidan maza kaman su biyar akan su fito da itah.
"Haba baba kace yarinya ce ƴar shekara sha biyu,miye kuma sai an ƙiramu kusan mu biyar,saikace wani gardi"
Ubaidu yafaÉ—a da sanda a hannunsa yana dariya rainin hankali"
"Uhm uhm ubaidu kudayyi a hankali,bakuga yanda tayiwa kazar rammah bane É—azu,nan da nan fah ta cinyeta a gabanmu,kuma itama kanta ramman data cijeta saida fatar da É—aye"
Ammi tafaÉ—a cikeda tsoro.
Duk cikin mazan babu wanda ya yarda da zancen ammi,amma dai basu ajiye sandan ba suka shiga dashi.
Deejah tana ganin shigowar mazan da sanda É—akin ta tashi ta zauna.
Kallonsu take kafin idonta ya sauƙa kan rammah da uwaisu waɗanda suka shigo daga baya.
"Mazakuyimin da waÉ—annan sandunan,ke kika turo su ko dan kawai zan zauna a É—akinki? Kaikuma dan kawai nace na yarda ka zama ubana na biyu shine zaka saka a dakeni"
Cikeda mamaki bawai na tsoro ba take kallon su dukka,baƙincikine yasake shaƙar rammah,musamman data gano inda dejah ta kwanta,tajiƙe wajen jaraff da fitsari,hmm dama yaushe za'a raba wannan da fitsari,da batayi kashi bama.

Yakuke ganin shin Deejah zata fita daga É—akin ramma kuwa????

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[13]

"Ehh nina ɗakkosun su fita dake,au harma mamakin hakan kike,da a tunaninki zan zauna dake ne a ƙarƙashin rumfah ɗaya,kalli fah yanda kika jiƙemin gado,abinda ko ɗana baya yimin ƙatuwa dake. Ubaidu kuyi ta dukanta,shegiya aljana kawai"
Ubaidu ne yakai hannu zai zawota daga kan gadon ta goce.
"Ohh dama ta gaske kuke,naga aljanuma ai da basaso na zauna a jejinsu mun daidaita ballanta na kuma ku,nafiku iskanci bari ku gani. Kekuma da banyi niyyar yi miki komai ba,amma tunda kika nunamin kalarki bari kiga tawa"
Tana gama faɗin hakan ɗakin yakama da uwa ta ko'ina,tsakiyar gadonne kujera ne,cikin ƙankanin lokaci hayaƙi ya turnuƙe ɗakin.
Fita sukayi da ciki kowa yana toshe hanci saboda numfashinsa daya shaqe,rammah kuwa sai ihu take tana neman agaji na É—akinta dayake shirin zama toka.
Ruwa aka fara zubawa,jama'a tana kawo ɗauki daga waje,daƙyar aka samu wutar ta lafah,kayan ɗakinta kam saidai wasu idan tayi.
"Jama'a ku taimaka ba kwa ganin É—akina ne,komai na fah yana ciki,wayyo Allah na"
Burburwa rammah take tana birgima a ƙasa,sai riƙeta ake zata faɗa cikin wutar,gidan yacika da mutane da kuma hayaniya.
Har dare yayi gidan bai lafa ba,rammah kam ita akayiwa,babu abinda ta tsira dashi a É—akin sai ginin kawai,zuwa lokacin tama daina magana sai bin mutane da ido.

___***__

[Sumaimah a mahangar gani]
Chapter 20 · 0% Book details