← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 47

Sashe 15

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Hannu naji yana bubbagani,can kuma sai naji murya ƙasa ƙasa tana min magana..
Saida baccin ya dan bar idona kafin na naji ashe inna ce take tashina.
"Ƴar nan tashi kiyi sallah anyi assalatu,ko bakyayine"
Tasake maimaitawa a sanyaye.
Juyi nayi kafin na tashi zaune,ohh ban taba tunanin kwana na nafarko a gidan zanyi bacci hadda juyi ba kamar haka.
Kallonta nayi da farin hijabi a jikinta,hannunta riƙeda carbi tana kan sallaya.
Na lura da hakanne saboda hasken É—an Club da ake haÉ—awa ya haska É—akin..haka kawai naji ta burgeni,indai bawai mantawa nayi ba,tunda nake babu wanda ya taba tashina sallahr asuba a gidan mu.
Saƙƙowa nayi daga kan gadon wanda yanxu yazama nawa.
Inda buta take ajiye na nufa na É—auka domin zuwa banÉ—aki.
Bayan na idar da sallah gaisheta nayi ta amsa cikin sakin fuska,har zuwa lokacin lazimi takeyi,nima danaga haka ban koma baccin ba saina fara nawa.
Muryar ta can sama sama naji tanamin magana,firgit na kalleta,kenan bacci na cigaba dayi a zaune.
"Sumaimah ki koma ki kwanta mana,ke ba kaman mu ba da baccin mu yanzu yayi ƙaranci,bare kuma kunsha hidimar biki,ki koma kiyi baccin ki kinji"
ÆŠaga mata kai nayi,dan dama hakan nakeso.
Muryar inna naji tana magana da wasu yara,hakanne yasa na buÉ—e idona,lokacin rana ta fito tangargar.
Fitowa nayi daga É—akin na zauna a tabarmar da take zaune..
"Kin tashi kenan,ga abin karyawa toh.."
"ÆŠumamen tuwo ne sai kuma wani É—an kwano da awara a cikin kaman guda bakwai,sai kuma kofin kokoh"
"Hmm kiyi haƙuri fah ƴar nan,amarya da aka sani da cin kaji a ranar farko kega abinda kika samu,wlh banda kuɗine,awarar ma a wajen gaji na karbo nace ta bawa baƙuwa"
Allah sarki tausayinta ne yakamani,hmm batasan a hakan kayan daÉ—i tabani ba akan abinda nake ci a gidan.
"Lahh inna karki damu,shimfiÉ—ar fuska ma da kika bani tafimin komai da kike tunani,fatana Allah bamu ikon zama cikin aminci"
"Ameen ƴar nan,gaskiya ko kusa baki dace da wancan huhun ba,kawai dai ƙaddara ce da idan tazo baza'a tsallake ba. Sannan dan Allah kiyi haƙuri da son kaina,dan lokacin da naji wannan batun nayi niyyar na hanashi,amma kuma sai nayi tunanin wataƙila sanadin shiryuwarsa ne aurennaki. Yanzu dana ganki ma na ƙara tabbatar da hakan,dan inaga sai an zage garinnan kafin a samu mace irinki,kiyi haƙuri kiyi haƙuri kinji"
"Inna kidaina bani haƙuri,nima lokacin da Naji labarin kwana nayi ina Addu'a akan Allah kar ya hadani dashi,amma dana ga an ɗaura aurena dashi jiya sai nayi tunanin inaga shine mafi alkhairin dana daɗe ina roƙon Allah yabani,dan haka ki daina wannan bada haƙurin ba laifinki bane,fatana Allah yabani ikon jure duk abinda zaije yazo."
"Ameen kiyi ta haƙuri da sannu zakiga mafita"
Zancen duk ya isheni,tunda gani nazo gidan to kuma banason tuna wai dama ban xo ba,dan haka nayi ƙokarin kawar da zancen..
"Uhm inna wanne aikin za'ayi ne a gidan?"
"Ehh toh banice yanzu da tuwo ba gaji ce take saita bani,wanke wanke kuma atika ce take,idan bata nan kuma ninayi in su farida suna nan su jijjiƙa"
"Toh bari naje na gaishe ta ma,sainaji wanne aiki zan kama mata"
"Ahah kijidai ku gaisa,amma batun aiki ko zakiyi ma ai sai kinyi kaman sati ko sati biyu,dan haka kada ki damu kanki atika ai tana nan zata zo tayi wanke wanken"
To nacewa inna tareda kallon inda uban tulin wanke wanken yake,wasu manyan tukwane na abincin siyarwa da kuma su kansu kwanikan abincin siyarwar sun cika wajen famm,ƙudaje sai bin miyar data bushe suke,kaman dai na gidanmu haka yake..

Sallama nayi a bakin ƙofar,babu wanda ya amsa,sai hayani ya suke,inaga ma basuji shigowa ta ba.
Ban dai yi ƙasa a gwiwa ba na ƙarisa wajen da suke zaunen.
Gaji ce suke ta musu itada wata matashiyar budurwa,wacce ta juya bayan ta can.
"Haba gaji,idan baki yarda dani ba wazai yarda da nine,nace miki ban É—au kuÉ—inki ba,yakikeso nayi ne wai?"
"Atika nafasan halinki,kwanannan na kula bakida kuÉ—i,koya nayi wasafai dana wa É—ebewa zakiyi,ya za'ayi ace har dubu biyu ta b'ata a cikin cinikin"
"To shikenan ai gani ki cazeni mana,kokuma ka jaka ta nan"
"Ohh shasha zaki mayarni ma,na caje........"
"Salamu alaikum"
Nasake sallama dan su san ina wajen..
A tare suka juyo inda na É—ora idona akan Budurwar..
"Atika??"
"Na faÉ—a cikeda mamaki"
Wani kallon juya ido tayimin tareda cewa cikin muryar duniyanci..
"To ya ranki,kinyi mamakin gani nane komai?"

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[10]
Chapter 15 · 0% Book details