← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 47

Sashe 41

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Me kikace abbanku ya dawo?"
Hajiya Maryam tafaÉ—a cikeda damuwa tana kallon fatee.
"Ehh mommy yanzunnan ya shigo gidan,naga ya nufi sashensa bai shigo cikin gidaba"
Tana cikin bayanin hajiya maryam tanufi sashennasa tana tafiyar karairaya kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƙwanƙwasawa tayi,jin shuru ba'a amsaba yasa tasaka kai cikin ɗakin.
A tsaye yake a gaban window yana kallon lambun dayake bayan É—akinnasa,kana ganinsa kasan faÉ—awa yayi cikin zurfin tunani.
"Me yasamu wannan babban jarumin naganshi a haka,kaddai kacemin har yanzu baku samu inda barayin sukeba,kuma sun gudu da akwatin baku kamasu ba?"
Tafada kaman mai jin tausayinsa,amma kanaki kasan ta biyu take zancen.
Zan ajiyar zuciya A.M Aliyu yayi tareda cewa.
"Maryam,waishin yaushe zaki girma ki daina wannan abunne kam iyeee,Æ´aÆ´an ki ma bazasuyi abinda kikeyi ba,yanda kikeyi haka kikeso Æ´aÆ´an ki suje gidan mijinsu suyi ne? Ace tsawon sati guda ba nan ina office,duk akan wani abu daya shigemin duhu,amma daga dawowata babu magana mai daÉ—i sai ta izgili? Shiyasa fah banshiga gida ba bare ki ganni,amma saida kika biyoni kina murnar na faÉ—i koh ?"
"Uhm dagajin yanda kake magana baku kamasu ba da alama,kenan wannan akwatin dayake É—auke da bayanai masu hatsari yana hannun 'baya gari"
Juyowa yayi yana kallon hajiyah maryam,wacce take tsaye ta dan goce irin tsayuwar celebrity É—innan.
"Shin wai tukunnama taya kikasan cewar kundin a akwati yake,a tunani na dai bamuyi wannan zancen dake ba,kuma ko a kafar yaÉ—a labarai ba'a faÉ—a ba,taya kika sani?"
Tsareta yayi da ido tareda yimata kallon tuhuma,wanda hakan yasaka jujjuya ido tareda cewa.
"Ehh dama zaka fara yanzu,dan kasamu ma na kula dakai nazo ina tambayarka shine zaka faramin wannan kallon rashin yardar,tun batan Ahmad kakemin irin wannan kallon na rashin fahimta"
"Ohh dama 'bata yayi ba mutuwa yayi ba?"
Gum tayi da idonta tareda nemo abinda zatace.
"Mutuwa nakeso nace,kaima ai kasan mutuwar yayi tunda har gawarsa an kawo maka. Nida wannan abinda kakemin na ƙin raba sirrinka dani kokuma kana tuhumata ka daureni mana kawai ka huta iyee. Kaje cibiyar bincike kace zaka ɗaure matarka dayafiye maka"
Masifah ta cigaba dayi,ta inda take shiga ba tanan take fita,saida tayi mai isarta ta fice daga ɗakin tareda buga ƙofar.
Runtse ido AM Aliyu yayi tareda É—ora hannunsa a kansa.
Yana jin takun tafiyarta har tayi nisa.
Shin me yayi mata kuma wai itace dayin fushi,shine ya kamata ya ɗau mataki amma duk sanda yayi yunƙurin yin hakan sai yaji ya kasa.
GabaÉ—aya gidan mutane uku ne za'a ce daidai,daga Mammah,saleem sai Noor,su kaÉ—aine zaka gansu da sanyin hali. Amma Sameer kam da fatee kana gani kasan ita suka iyo. Shikuwa Ahmad lokacin dayake nan gwanda kowama dashi,domin ko sashensa a can gefe yake,bayason ana yimasa katsalandan,saidai kaima bazai maka ba.
Sannan yanada basira da sanin mai yake,komai shine yake zuwa a fari kafin sauran ,hakanne yasa kullum hankalin hajiyah maryam yana kansa,in za'ayi masa abu ma ita ke shiga da fita ta hana,shikansa yasan da hakan. Shiyasa ko sashenta baya taba zuwa sai yakama dole.
Kaman yadda AM Aliyu bai yarda da ita ba hakama Gen Ahmad,don daff da mutuwarsa ya buÉ—e wani file akan ta,tunda ta tafi kuma babu wanda yasake bi ta kan zancen har yau.
Tsohuwar lauyace mai zaman kanta,duk da yanzu bata aiki,amma kuma tasan takan binciken abinda take son sani sannan kuma da yanda zata gujewa mai son bincikarta. Tana da son mulki da son ganin ana mata hidima,don ko shi kansa AM Aliyu dayake shugaban sojoji bai kaita juya sojojin ba,kuma tanada mutanenta a cikinsu,wanda ko mai tace karsu faÉ—a babu wanda ya isa ya sakasu magana harda shi kansa uban gayyar.
Wannan abubuwan su suka sa kowa hatta Æ´aÆ´an ta suke shakkarta inta juyo ta kansu inka cire Ahmad shikaÉ—ai ne baya tsoronta,kuma shine ciwon idon dayake hanata bacci lokacin dayake raye,yanzu kuwa da baya nan baccinta take sha harda minshari.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[28]

[Sumaimah a mahangar gani]
Chapter 41 · 0% Book details