Sashe 33
Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bawani gyara ƙofar take buƙata ba,amma haka nasake gyarawa dai,saboda murnar dawowar innan.
Bayan na gama wanka nayi nasaka kayana na zaman gida.. Ina kwance har bacci ya É—aukeni.
Can kaman a mafarki nake jiyo sallamar mutum a baƙin ƙofar ɗakin.
Ɗan kwalina na ja na yafa na fito,himm naci karo da kaya a bakin ƙofar ɗakin.
Buhun shinkafah Æ´ar gwamnati,galon É—in manja dana mangyaÉ—a,katton É—in taliya ta leda,buhun gari na semo,macronni indomie harda su doyah da dankali.Sabon Risho a kwalinsa da kuma jarkar kananzir babba a ciki damm. Sabulai na wanke dana wanki masu kyau,harda macline.
Zare ido nayi ina dafe ƙirji,wannan kayan fah,wanene yayi batan kai ya shigo dasu haka?anyah bana gidan chairman bane ba kuwa.
Ina nan tsaye nayi suman tsaye tunda yashigo giɗan hannunsa riƙeda jakakkuna guda biyu,wani yaro ma yana biyeda shi da wata leda a hannunsa.
Dariyah Tunga ya tuntsire da itah ganin na ƙamekam kaman wata soja.
"Matar ogah wannan kallon fah,ogah yacemin dama kunyi maganar dashi ina,kan cewar za'a kawo. Ga wannan jakakkunan É—aya naki ne É—aya kuma na inna,wanann kuma wai ki soya shi ku dunga miyah dashi"
Jakakkunan na bi da kallo,sannan kuma da ledar da yaron ya miƙamin.
Har sannan ko ƙala ban ce ba,wasu kuɗaɗe yasake ƙirgowa ya miƙomin,hannu yana rawa na karba inaso naji su kuma na menene.
"Wannan kuma yace ki riƙe ki sayi abinda kikaga babu,in sun ƙare kiyi masa magana,ga yaronan zai dunga shigowa yana miki aika,inya kama sai ku dunga bashi abinci. Idan babu wani abin ni zan tafi"
"Ba.....bbbu komai ammmm....mmma kuwa ba mafarki nake ba?"
"Wanne mafarki ba mafarki,namune yake shirin hawa mulki,da kuma sabon ainkin ogah da yayi shima suka biyashi da tsoka,muma yanzu mun daina satar kajin mutane,gwangwajewa muke da daɗi,muma muka ci bareke matar ogah,ai ki sake jansa a jiki ki lashi arziƙi tunda Allah yakawoki a daidai sanda yayi kuɗi,dama ku kuke ganinsa kaman mungu,amma oga goje ai akwai kyauta,saidai in bata biyo ta kanka ba baya tunawa da shafinka. Inkika bi a sannu zaki gane kansa,kuma zakiji daɗin zama dashi,sannan akwai abu ɗaya danake son kiyi a rayuwarsa,in lokacin yazo da kanki zaki tambaya kuma nayi alƙwarin zan sanar dake.....zo mu tafi Yusuf"
YafaÉ—awa yaron suka fitah waje bayan sun barni a duhu tsulum da bayyanar tasu.
Ledar da take hannuna na buɗe,kaji ne Yankakku an gyarasu tass. Samun waje nayi na ajiyesu tareda ƙirga kuɗin dayake hannuna,dubu ashirinne ciff.
Komawa É—aki nayi na ajiye kuÉ—in da jakakkunan danaji kaman kayane a ciki.
Sauran kayan ma duk É—akin na kaisu na ajiye,da nayi niyyar kaisu É—aya É—akin inna ne wanda babu komai a ciki,saikuma na tuna akwai masu halin bera a gidan sosai,karsu yi É—an halin irin wanda sukamin a kuÉ—ina.
Babu abinda zan taba sai inna ta dawo,ko wanne lokaci nasna zata iya dawowa a yau É—in.
Dan har yanzu ban yarda Tunga da gaske yake gojene ya aikoshi ba tabbb wayaga duniya sabuwa.
__**__
"Wlh gaji da gaskene nake miki,wannan yaron yayah gojenne ya dunga shigowa da kayan abinci yana jibgawa a ƙofar inna mairo wajen Sumaimah,hadda wasu jakkuna da bansan menene a ciki ba"
"Ke ƴar nan banason ƙaryar banza fah"
"Hmmm kinace wai ƙarya nake,ki zo ki leƙa ki gani mana,gatacan tana shiga dasu ma ɗakin innan"
Jirif gaji ta tashi daga kason abincin da take ta leƙo ƙofar innan,daidai lokacin da Sumaimah take jan buhun shinkafar zuwa cikin ɗakin innan.
Zaro ido tayi tana kallon sauran kayan da suke wajen,katton É—in taliyah dana macaroni,kaman taje ta É—ebe haka takeji.
"Kambuuu wanne ƙusane yabasu waɗannan kayan abincin haka"
"Ohh baki sani ba,wanda goje yakeyiwa aiki shine ya tsaya takarar É—an majalisa,kuma ana tunanin shine zaici,har mashin ya siya fah saboda dal kina gani yake hawa. Sannan kwana biyunnan kullum sai an kawowa Sumaimah nama da shayi mai kauri,kina gani ma sanda take zubawa a shara"
"CabÉ—i wannan shine ka tura mutum rana an janyeshi cikin fadama,shegiyar yarinya haka zatayi ta famtamawa yanzu muna kallo....inaa aradu hakan bazai faru ba,bari Atika ta dawo daga talle musan nayi.hakama malam,ai dolene muma yabamu tunda ina matar ubansa,bazayyiyu a dangwali na banzar nan babu mu ba kam.."
Toh fah
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[22]
[Sumaimah a mahangar gani]
Tun ɗazu nake zuba idon ganin inna,motsi kaɗan saina leƙa ƙofar gida,safa da marwa nake yanzu ma a kan baranda ina tunanin anya kuwa zata dawo ɗin,ganin yamma tana shirin yi amma shuru bata dawo ba.
Kasancewar ban buÉ—e stove É—in na fara amfani dashi ba,kawai murhu na haÉ—a na gyara naman,saikuma na tafasa taliya..
Har na juya zan koma É—aki sainaga inna Mairo tashigo gidan,magana suke da almajirin daya shigo mata da kaya,wani farinciki na tsinci kaina dashi,ban lokacin dana tafi da gudu na rungumeta ba.
Dariyah tayi tana cewa.
"Allah sarki,duk da na tafi na barki amma kike murnar dawowa ta,nayi zaton ai zakiyi fushi ganin na ƙara sati guda"
"Uhm naji haushi kam har kuka nayi,amma ya wuce tunda kin dawo,zo muje ki zauna ki huta,daga gani kin gaji"
Jan hannunta nayi muka shiga cikin ɗakinnata,saidai tundaga bakin ƙofah danaga ta tsaya nasan abinda yabani mamaki ɗazu tagani,wato kayan da goje ya kawo.
"Sumaimah wannan abin kumafah,waye ya kawo wannan kayan haka?"
"Uhm goje ne ya saka Tunga ya kawo É—azu,wai yakamata mufara abincinmu"
"Eh to yanzu ba zancen abincinba,a ina yasamu kuÉ—in daya siyo waÉ—annan kayan,a sanina dashi bashida ko sisi,ko wajen mai shayi ma bashi ake rubuta masa,taya yasamu wani kuÉ—in siyan waÉ—annan kayan"
Cikeda zullumi take maganar,kanaji kasan bata yadda da kayan ba.
"Nima na faÉ—i haka sai Tunga yace wai É—an siyasar su ne yaci,suma haka suka samu kuÉ—in dayawa,inaga kuma shugaba"
"Oh na manta ma da abin zabe,in hakane shikenan Allah ya kyauta,amma zan sake tambayarsa,kai wannan ƙasa tamu wai dan zakaci zabe sai kayita rabawa matasa kuɗin al'umma?. Allah ya shirya shuwagabanninmu kawai"
"Ameen ya Allah"
Gyalen dayake wuyanta ta ajiye tareda zama a bakin ƙaramin gadonta.
"Yana sameku Sumaimah ya mutanen gidan,da zan shiga ƙofar gaji nace mata na dawo,sai kuma naji wai ta tafi anguwa. Wannan kayan ki gyarasu mana shima abin girkin ki buɗe ki jerashi,ina kin iyah amfani dashi?"
"Ehh na iya,ina dafawa yaya Musbahu indomie a nasa na ƙofarsa"
"Yawwa toh ki shirya komai,ai dama da kinyi tun É—azun basai kin jirani ba"
To nace tareda ɗakkowa kuɗin daya bani ɗazu na miƙa mata.
"Inna gashi wannan ai a ajiye inda abinda za'a siya na amfani"
"Ahah ki riƙe a wajenki tunda kece mai siyan abubuwan,ni bazan riƙe kuɗi ba a hannuna,kiyi yanda ya dace kawai,in neman shawara ce saiki tambayeni,amma batun na karba bai taso ba. Sannan a kayan ki ɗebi wasu ki kaiwa su gaji,duk da an san zaman da akeyi amma tayi ƙoƙari sosai nayin abinci"
Maida kuɗin nayi inda na ajiye,abincin na zuba mata taci sannan muka hau hira,wadda duk na abinda ya faru ne da batanan,wani tayi dariya wani kuma ta jijjiga kai. Abinda take cewa kawai nayi haƙurine watarana zai wuce,a lokacin baya bana yarda da zancen ta,amma yanzu nafara yarda da zai wuce watarana sai labari.
Kafin dare na shirya komai yanda zanyi amfani dashi,Sannan su gaji ma na cire musu wanda zan kaimusu.
Jakakkunan da Tunga yabani kuwa kayane a ciki na sakawa,kowanne kala uku da hijabi da takalmi flat mai kyau,idan nace banyi murna na wlh ƙarya nake,ko a mafarki bantaba tunanin samun kayan a lokacin ba.
Tunda magriba nake jiran naji gaji ta dawo,amma sai bayan isha tukunna naji muryarta tana magana da hamisu akan wai bai É—ebi ruwan da ta sakashi ba.
Sallama nayi na shiga,hannun É—auke da kayan dana kai musu,shuru tayi da faÉ—an tana kallona,duk da bani take kallo ba sai abin hannuna..
Washe baki tayi tana min magana,abinda tunda nake bata taba yimin ba sai yau.
"Ahh Sumaimah kece da darennan,naji Addah Mairo ta dawo ko,yanzu nake shirin zuwa nayi mata sannu da dawowa ai"
Wai meee?? Ba mafarki nake ba kuwa,gajice take waÉ—annan kalaman masu daÉ—i.
Dawowa nayi daga mafarkin dana tafi nace.
"Ehh ta dawo run É—azu da bakyanan,ga wannan kayan abinci ne,sannan inna tace mu faÉ—amiki ta gode sosai,zamu dunga girkinmu yanzu"
"Ahhh me yayi zafi daza'a raba girki haka rana tsaka,mai zai hana ma ni zan dungayi kaman koyaushe,kice mata ta kawo kayan girkin za'a dungayi ba matsala"
Anya kuwa gaji tanada kunya? Nayiwa kaina wannan tambayar,juyowa nayi ina mata kallon mamaki.
"Ahah karki damu gaji babu komai zan dungayi,yanzu ai gurege yazo ga harawa,koda zata kare walau nan kusa kokuma ya daɗe,amma dai yanzu kam zaici ya more. Kuma karki damu inna bazata ƙwace gonar marigayi ba a hannun babansu Atika,sannan kuma injin markaɗenta ma bazata karba a wajensa,dama ina dasu ake ciyar da gidan,yanzu babu mu a ciki kuci iyah ku kaɗai"
Ban tsaya jin abinda zatace ba na fita daga ƙofar bayan na ajiyemata kayan,a zaton ta duk abinda take ba'a sani ba,nunawa take kaman ita take ciyarda gidan,bayan gonar da ake noma hatsin ba nasu bane,injin markaɗen da baban su Atika yasaka yara suna aiki dashi yana karbar kuɗin duk na inna ne.
Kayan aikina da nazo dasu na fito dasu,tunda nazo gidan yau wata na guda sai yau zanyi wani abu na Æ´an cin kaina.
Kula tuwo da miya na É—akko na abincin goje,saikuma kwanukan da zanyi amfani dasu na aikace aikace.
Da daddare ban sake abinci ba,kasancewar wanda nayi ma na rana bamu cinye ba,kuma goje yace ba lallai yadawo ba.
Dan haka hirarmu muka sha har bacci ya É—aukemu,cikin farinciki da annashuwa.
__***__