← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ina komawa ɗakin inna tsalle na farayi da murna,banyi zaton zai barni na fita hakan cikin sauƙi ba.
Sai yanzu ne zan yi fita ta daÉ—i,ba wancan É—iban ruwan ba,shikenan idan naje sai magriba nadawo.
Hijabi na saka wanda inna mairo tayimin a auren,babu laifi mai kyau nekam a daidai kuÉ—insa.
Takalmin shima na É—akko,dan tunda aka kawoni gidan ban ta'ba sakashi ba sai yau.
Bayan na shirya ƙofar gaji na shiga yi mata sallama,hmmmm zata kulani ne ma,tana fama da jinyar ƴar ta.
Nazo shiga ƙofar tsayawa nayi jin abinda suke cewa.
"Ai duk laifinkine gaji,tun yausshe kike cewa zaki yi maganinsa har yanzu abu yaƙiyi,kai ba abin ka ɗakko masa ƴan daba ba shine shugabansu,mutanen garinma tsoron hukuntashi sukeyi,sannan asiri tun yaushe kike cewa zakiyi har yanzu bakiyi ba"
Atika ce take faÉ—a tana kuka saboda gaji tana dunduma mata jikinta take faÉ—a.
"Dallah yimin shuru,ke bakiga abinda kikayi ba koh,kinje kinyi ciki a wajen zubarwa kince nasa ne,dama ai dole zance ya koma kunnensa,kuma sanin kankine ba shuru zayyi ba da wannan lamarin.....waccar yarinyar cema dole zata shiga hannuna na kamata gamm,har wuyanta yayi ƙwari tana gasamin magana son ranta? Lallai batasan wacece niba da alama"
Jijjiga kai nayi jin maganganunnasu ba wasu sabi bane,dama na saba dajin irinsu tun a gidanmu.
Ƙarisawa nayi cikin ƙofarta ta bakina ɗauke da sallama,sun ɗan razana saboda tsarguwar kona ji mai suke cewa,nikuwa ban basu ƙofar dazasu san cewar na jisun ba sam.
"Uhm gaji nizan tafi gidan ƙawata saida magriba zan dawo"
Wata harara ta maka min,daganan bata sake cewa komai ba tacigaba da kulada ƴar tata,nima kuma daman ban tsammaci amsar ba,na faɗa mata ne saboda haƙƙinta ne a matsayinta na wacce muke zaune gida ɗayah.
Tafiyah nake cikin nutsuwa hankali kwance har na isa gidan su Shareefah,kasancewar ranar asabar ce nasan daman tanan bata tafi makarantar islamiyyah ba.
Da tsalle ta tarbeni tana murna muka zauna,sai dariyah take tarasa abincewa,da alama zuwannawa yayi mata bazata.
"Shareefah ya mutanen gidan?"
"Uhm gida kalau yanzu nnan ummah kuwa ta tafi gidan suna"
Bayan mungama gaisawar shuru nayi,idan nace banajin yunwa wlh nayi ƙarya,jikina karkarwa yake kaman an jonamin lantarki,kunya nake ji na roƙeta abinci,amma haka na daure na tambaya.
"Uhm.....Shareefah yunwa nakeji kunada abinci dan Allah"
Zaro ido tayi tana tafe kirji,da alama ta kulada yanda jikina yake karkarwa ne.
"Nashiga uku Sumaimah ji yanda jikinki yaje karkarwa,bankula ba saida kikayi magana nagani. Abinci babu yawa yara sun cinye,amma barina kawo miki sauran kici,inyaso saina yimiki wani abun ko É—an wake ne"
Tana gama faÉ—in hakan ta tashi da sauri ta kawomin,tuwon shinkafa ne da miyar taushe.
Malmala biyu ce,saboda yunwar danake ji nan da nan na cinyeshi,kai abinci rahama nan da nan naji jina da ganina sun dawo waral.
Tashi nayi ina tayata muna jefah ɗan waken dayake da yawa tayi harda na gidan,zance muke wanda yawanci rabinsa na islamiyyarmu ne,yanda take bani labarin ƙawayenmu zasuyi aure,wata ƙwallah ce ta zubomin nayi saurin gogewa,uhmm su zasu auri wanda suke so suma suna sonsu.
Shareefah ta kulada yanda yanayina ya sanja,ta buɗe baki zatayi magana kenan Hamisu yashigo ƙanin Shareefan.
"Anty Shareefah gacan Æ´an sanda zasu tafi da baban Anty Sumaimah caji office"
"Me ubana kuma? Toh mekuma yayi za'a kaishi caji office"
Shareefah ce ta kalli hamisun cikeda damuwa,musamman ganin yanda yanayin ƙawar tata ya sanja.
"Hamisu mai yafaru,anya kuwa kaji daidai?"
"Wlh shi naji ana cewa,wai wannan ƴar da aka bashi a caca ce take jawo,ta zubarwa matar gidan man suyar ƙosai ta cinye ƙosan kuma,sannan ta ƙone ɗakin inna rammah. Amma abinda yasa aka kamashi yanzun wai wani yaro ta bulawa kai da dutsi,yanzu haka an tafi asibiti dashi kaman bazayyi rai ba,shine da batakai ɗauri ba aka kama Babanku sai yayi biyan kuɗin magani"
Duk maganar dayake ban fahimce shi,wacce Æ´a aka bashi a sanadin caca kuma,bayan ni daya bayar wata kuma aka kawo masa? Shareefah na kallah wacce iyah ita kaÉ—aice nasan zata bani amsar wannan tambayar,dan daga ganin yanayinta ya nuna tasan kwanan zancen.
"Wacce Æ´a yake magana akai ne Shareefah?"
Shuru tayi da bazata bani amsa ba,can kuma saita kwashe abinda ya faru ta faɗamin,yanda baba yayiwa ɗan fulani wayo dan ya auri ƴarsa,ƙarshe kuma rishe ya juye dashi......wai ni meyasa irin wannan abubuwan suke faruwa da garinmu ne,kodan muna lungu shiyasa abubuwan ashsha sukayi yawa kai. Cikin garin Kwalin ma haka suke fama da irin waɗannan abubuwan?.
Jijjiga ni Shareefah tayi,tana zaton koh suman tsaye nayi,habadai wannan abun yasakani suman tsaye? Ai naga wanda ya fishi ma.
ÆŠaÉ—É—aya nake jefah É—an waken a bakina,É—azu yabani sha'awa sosai,amma yanzu ya fita akaina sam,saboda abinda yafaru.
Tundaga lokacin kuma zancen namu yakoma na Deejah,sabuwar ƙanwar tawa,wani abun nayi dariyah wani na jijjiga kai,ance dai mugunta babu kyau,amma wlh banji tausayinsu ba sam,suma ji yanda naji inda daɗi.
Idan an kwana biyu zanje gidan nima na ganta,yanda ake bani labarin kam batada maraba da aljana.
Ganin duhu yafara yasa na tashi zan tafi,har sannan umman Shareefah bata dawo ba.
"Toh Shareefah barina tafi gida nikam duhu ya fara"
"To shikenan Sumaimah kici gaba da haƙuri komai zai zai zama tarihi,karkiyimata wanke wanken gobe,kiyi zaman ki,zan aiko miki da abin karyawa Inshaallah,to wai shi meyasa bazai dunga baki abinci bane,ba zamansa kike bane?"
"Bamu kai kan wannan ba tukunna,amma kuma a yanda na kula kaman yanada sauƙin kai"
"Eh toh hakane,kaman yanda kika ce zan dunga kawo miki abincin har sai lokacin da taga gurbinki kuka daidai ta,shima kuma dan Allah Sumaimah ki dunga gwada dabararki irin ta mata akansa,idan kinga kuma abin bazai gyaruba sai a san nayi"
Kallonta nake da tana maganar,shin ana samun ƙawa irinta kuwa yanzu,nikam duk da banyi sa'ar mijiba amma ƙawa kam mashaallah kawai zance.
Rungumeta nayi ƙyam ina mayar da kukan dayake idona,saboda godiyar danake son yimata ma bazai isa ba.
Bayan munyi sallama hanyar gidannawa na kama,É—azu Shareefah tace ko zanje caji office nace mata bazani ba. A tambayar danayi iyah gidnasu kawai na tambaya,koda na tambaya ma nai zanje na iyo,nace masa me? A matsayina dai na Æ´ar sa ina fatan Allah ya rage masa nauyin ruwan daya jawowa kansa,har ya jawowa wasu ma.
Lokacin dana isa gidan wasu masallatan ma ana ƙiran sallah. Kaman kullum gaji tana ta fama da yaranta,nidai bance mata na dawo na wuce ƙofarmu.
Alwalar magriba nayi na shiga ɗaki,riƙeta zanyi ba lallai na fito ba sai gobe. Ta wani lokacin gwara gidannan,koba komai mutum zai samu nutsuwa da daddare.
Bayan nayi isha fitowa nayi zan shiga banɗaki,goje nagani da wasu baƙaƙen kaya ya fito daga cikin ɗakinsa,wata hula yasaka a kansa itama baƙa irin kayan jikinnasa,yana rataye da wata baƙar jaka.
Bai kulada ni ba saboda yanda na É—auke numfashina har ya wuce,ban taba ganinsa da irin waÉ—annan kayan ba,inda banga yanayin jikinsa ba da kuma kayan,bazance shine ba.
Ina kuma zaije da darennan sanye da waÉ—annan kayan,rai na dai bai kwanta da lamarinba na shige banÉ—akina.

__***__

[Goje a Mahangar gani]
Chapter 25 · 0% Book details