← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 47

Sashe 24

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tunda ƴan gidan sukaga Deejah ta ƙona ɗakin rammah kowa yake masifar tsoronta,komai tayi babu wanda yake cewa uffan a wunin ranar..
Da dare yayi ɗakin yara ammi ta nuna mata,kaman bazata shiga ba kuma sai ta nufi ɗakin,shigarta keda wuyah sukaga yaran ɗakin kowa yana fitowa da gudu,da suna ihu wasu kuma suna matsar ƙwallah.
Matan gidan duk wadda da yaranta a ɗakin fitowa suka yi,jin ihun yara yaƙi ci yaƙi cinyewa.
Asiyah ce tayi ƙarfin halin faɗin abinda ya faru,tunda ita da ɗab girmanta,dan zasuyi shekaru ɗaya da Deejah.
"Muna kwance kawai ji mukayi ta fara dukanmu,wai duk mu fita daga ɗakin mu koma na iyayenmu,ba kowa yaƙi ajiyeta a ɗakinsa ba,itama bazata kwana da kowa ba,kuwa wai duk wanda yasake shiga ɗakin saita vabbakeshi da ransa..
Shuru sukayi suna sauraran Asiyah,yayinda kowa yakama hannun ɗansa yana rarrashinsa,kowa ta abinda yake faɗa ya shige ƙofarsa.
Washagari da safe kamar kullum hayaniya ta kaure ko ina,itadai rammah ranar a gidnasu ta kwana,saboda anyi ta bata baki ta zauna tace sai uwaisu ya rufa mata É—aki kafin ta dawo,yanzu dole zaije ko ina fallan kwano yake ya nemo yazo ya rufamata É—akin..
Fitowa tayi tana mitstsika ido,jikinta duƙu duƙu yanda ta kwanta haka ta tashi.
Ƙofar su ammin tashigo ana zuzzubawa yara koko zasu tafi makaranta.
Tana zuwa batayiwa kowa magana ba ta ɗauki ɗan botikin kokon ta kafa a bakinta,ƙwatt ƙwatt saida taga bayansa ta ajiye tana gyara baki.
Yaran da suke zaune a gaban ammi suna jira a saka musu,ganin abinda ya faru suka fara kuka wasu harda burburwa. Sakin baki ammi tayi ludayin garwayawar a hannunta tana kallonta.
"Innar ubaidu wai baki gama saka sukarin bane,ki miƙomin nasamu nasha na tafi gonar can yaukam na dubo,zamu mai taki"
"Uhmm koko kam ai ya ƙare"
"Ke wannan wanne zancen shashanci ne,idan kunyi abincin siyarwa ku hanani yau kam ai nina saya da kuÉ—i na koh"
"Ehh nima danace maka ya ƙare ai bani na shanye da ƴaƴana ba koh? Ƴar ka ce ta shanye"
"Wacce ƴar tawa wai,ya faɗa yana banƙada labulen ɗakin"
Da Deejah suka haɗa ido tana suɗe bokitin kunun,dariya tayi masa irin ta aljanu,da haƙoranta kamar tsitstsige.
"Na shanye baba,na shanyen kunu,aradu ga zaki kamar an saka zuma,wanda wanccan babannawa yake bani babu suga haka,ashe bayyi ƙaryaba daya ce a cikin gari daɗi kukeji,ko kazar gidannan dana ci jiya tafi zomayen jeji daɗi ,ai nikam naji daɗi na tunda na dawo nan da zama"
Wani irin rammm gaban uwaisu ya buga,shida yake cewa yau zai maidata wajen ubanta yabashi haƙuri,shine zatace wai bazata koma ba anan zata zauna,in shi ina zama da aljana gida ɗaya,kokon da za'a rabawa yaran gidan harda shi,ta kafa kai ta kwankwaɗeshi,da wanne tukunn zaiji? Ga gyaran ɗakin ramma ma zaizo yayi.
Jefarda bokitin tayi can gefe,barass kuwa ya rabe biyu,dama yaji jiki sosai.
Hanyar waje ta nufah tana goge hannunta a jikin kayannata,jinin kazar jiyama yana jikin kayan.Wato haka takeyi shiyasa inta zo kusan mutum warin dauÉ—a ya dameshi.
Tana fita daga ƙofar Ammi ta kaɗe zaninta ta tashi,kallon uwaisu tayi tareda cewa.
"Inka fita ka siyomin bakitin roba a waje,a gaban idon ka ta fasamin nawa"
Tunzurowa yayi jin abinda tace.
"Mai kike nufi kenan,komai tayi nizan biya,saboda nine nayi ko?"
"In bakaine kayi bama ai ta dalilinka tazo gidan tayi,tunanin ka kenan ni zan dunga É—aukar asara,saboda nice nayi cacar aka kawomin ita?"
Buuu ya kaɗe rigarsa yayi hanyar waje,da Rabi yaci karo a hanyar mashiga matar ƙaninsa umaru.
Kuka take ta girmanta,hannunta ɗauke da matacin ƙosan ta. Saida tayi kukan ta matse kafin tafara magana cikin masifah.
"Wlh bazan yardaba,uban me akemin a gidan dazanyi haƙuri,ba'a ɗaukemin sabulu ba,magani kokuma ishashshen abinci,nazo na samo kuɗin jarin da taimakon ƴan uwana ina sana'a,kuma azo a nakasa ni wlh sai an biyani,in ba haka ba wlh ɗan sanda zan ƙira"
Tsayawa uwaisu yayi yana kallonta tana masifah tana kuka,ta inda take shiga batanan take fita ba,buÉ—e baki yayi zai tambayeta yaji wata matar tana faÉ—amasa abinda ya faru.
"Waccar ƴar taka da tazo jiyace tana suyar ƙosai tashigo ƙofar,batayi wata-wata ba ta dira akan suyar ƙosanta,wanda ta tara a cikin matacin duk ta cinyeshi,a garin ɗiban ƙosan kuma ta zubar mata da man suyar wanda yake kan wutah"
Runtse ido uwaisu yayi yana maimaito jawabin,iyah jiya kawai aka kawota amma tayi asarar da baisan adadinta ba,wannan wace irin masifah ce,tunda yake ko Æ´aÆ´an sa basu taba yimasa abinda tayi ba. Shin ta inama zai fara,gashi tafita waje,yasan a can ma dole sai tayi wani abun. Cikin sanyin jiki ya fita wajen,jikinsa ya haÉ—a gumi shirkif,duk da sanyin safiyar da ake.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[16]

[Sumaimah a mahangar gani]
Chapter 24 · 0% Book details