← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 47

Sashe 10

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tarin bola ce tsiri guda kaman zata dabo sama,da alama duk faÉ—in birnin garin anan suke tara tarkashen sharar.
A can cikin bolar saika kula ga hango motsin mutane ledodi sun lullubesu,suna nan kwance har yanzu basu tashi daga suma ko baccin wahala ba.
Malam audu ne yafara buÉ—e idonsa tareda ture ledar da take kansa,waya sani ma kota kashi ce.
Tashi yayi daƙyar ya zauna yana nishi,saboda tsamin da jikinsa yayi.
Gabas ya kalla kana da yamma,mai kuma suke a tsakiyar bola da ranar Allah.
Zaro ido yayi lokacin daya tuno izayar da suka sha a jiya a gidan dasuke aikin.
Gefensa ya kalla inda gaji ke kwance shame shame akan wasu tsummokara,saikace mahaukaciyah.
Ƙoƙartawa yayi yakai hannunsa ya kwaɗa mata duka a kunkuminta,aikuwa ta saki azababben ihu tana wangale baki.
"Wayyo wayyo kunkumina ku taimakeni jama'a zai cire"
"Ke dallah tashi mubar wajennan idan zamu iya tashi,waÉ—ancan dangin fir'aunan bayan gari suka kawomu cikin bola"
"Bola kuma wacce iri"
Itama ta yunƙura tana kallon tsummokaran da take kai"
Motsin Atika da sukaji a gefensu ne ya sakasu waiwayawa,kuma gaji ta fasa faÉ—in abinda yazo bakinta.
Kuka take tanan kururuwa kaman a cikin bacci,da alama abinda yafaru jiyanne yake dawo mata.
Jijjigata gaji tayi cikin baƙin ciki,dan koma mai yafaru ai ita ta jawo musu,da yanzu sun gama aikace aikacen gidan suna karyawa da lafiyayyen abinci.
"Shegiyar yarinya mai É—uwawun bin maza,ai gashinan abinda kika jawo mata,in sonsa kike tun farko da ki faÉ—amin mana asan surkullen da za'ayi,amma daga ke har ubannaki dayake garorine ku kagu jimanaye kunga kuÉ—i,sai karba kawai kuke bakwa tunanin mai ya faru. Ban tashi sanin mai yake faruwa ba sai ranar dazan sha duka tukunna.
Sai ku tashi mu tafi ai .......ahhh......."
Shuru tayi tana jujjuya kunkumi,dan dama sojan kunkuminnata yayi ta sambaɗawa kulƙensa.
Hararar malam audu tayi dayayi mata sannu,yunƙurawa tayi ta shi kana ta tashi sauran yaran wanda suke baccinsu hankali kwance.
Bayan sun tashi a wajen tafiya suka farayi zuwa tasha,kowa sai komaÉ—ewa yake yana tafi kaman horon cikin film É—in mayu.
Duk inda suka wuce kallon su ake,amma ko a jikinsu,tsamin da ƙashushuwansu suke ma ya isa.
Sa'ar da sukayi daga inda suka zubar dasu bashida nisa da tasha,saidai kuma ba a nan gizo yake saƙar ba kuɗin motar komawa garinnasu ne aiki.
Tun safe suke tashar har yamma,ganin bazasu samu mota ba yasa suka samu wani waje a tashar suka zauna.
Hayam hayam kowa sai baza hamma yake kaman zaici babu,idonsu yayi zuru.
"Yanzu kana gani zamu mutu bazaka nemo mana abinda zamuci ba,huhulahu kawai"
"Wai nikam gaji meyasa tunda kika shi a cikin bolar nan ni kike sauƙewa tujara,ya isheki fah haka,wlh zan sake mangareki ba ruwana da ciwukan da suke jikinka"
"Hehehe to ko sun duka ƙwalƙwalwarka ne take faɗa maka zaka iya dukana iyeee,kalleka fah kaima a doddoken kake ba iya ni kaɗai ba,ƴan ƙafafunka ma daƙyar kake ɗagasu sai kace lagwani. Kaff danginku haka kuke sai kace ƴaƴan kunika,zama dakai yasa duk ƴaƴana haka suke ƙafafu kaman liƙo cikin kuwa kaman randa,ni ba abinna zagesu ba kaima haka kake. Shiyasa nake mamakin ya akayi goje yakeda ƙira da ƙarfi,ubansa da uwarsa ba haka suke ba,har Addu'a nake ko ƴaƴana zasu iyoshi,na huta da aikin kashinsu da yawa,yaro in ka haifeshi bazayyi tafiya ba sai ya shekara uku tukunna wani abin ma..........."
"Dan Allah gaji kiyi shuru haka,dan Allah ku bar faÉ—annan sai munje gida,kowa sai kallon ku yake"
Kaman tayiwa dutsi magana ko kallonta basuyi ba,wata harara malam audu ke yiwa gaji kaman idonsa ya fito,dan yaji zafin wannan wankin babban bargon da tayi masa a tasha.
"Hmmm ke yanzu har zakice ma danasanin aure na kikeyi,daɗinta ma mu gidanmu ba mayu bane bama tanɗe kuruwar mutane,kowa yayiwa wannan ubannaki shaidar ko tsuntsune ya gifta da kan gidanku sai ya tanɗe kuruwarsa. Bandama ƙaddara data haɗani take,kaff abokaina da ƴan uwana babu wanda yayi na'am da aure na dake,nima kaina bansaniba ko tanɗeni kikayi"
"Hhhhhh narasa mai zan tanÉ—a inma maitarce sai kuruwarka,ko ban tanÉ—e ta bama a tanÉ—en take,dan daga ganinka yanda kake haka ma kuruwar taka take"
Tashi atika tayi tabar wajen,kowa sai kallonsu yake amma su babu ruwansu,ina zatakai wannan abin kunyar,wai dama haka auren yakene,kowa na ganin hanjin kowa,shiyasa fah ta tsani aurenma ita a rayuwarta,tafiso kawai a hole in holewar tazo a wuce wajen.
Tana cikin tunaninne taji muryar wani É—an garinsu. Juyowa tayi suka haÉ—a ido da tasi'u,shima da yace yana sonta,kayan gwari yake kawowa daga garinnasu zuwa nan,dama sana'arsa kenan.
"Lahhh tasi'u kaine"
"Ehh nine atika mai kike anan wajen ga jikinki duk ciwo?"
Inda inda tafara na ƙaryar dazata yimasa,can kuwa wani abu ya faɗo mata a rai.
"Uhmm dama gida zamu tafi to shine jiya barayi suka shiga mana gida,bayan sun ƙwace komai kuma suka yimana duka"
"Innalillahi garin ya haka,in su malam É—in suke,dama tafiya gida zanyi ko zakuzo mu tafi kawai,saidai zamuyi dare a hanya saboda motar tawa batada gudu"
"Babu komai hakanma mun gode,barina ƙirasu toh"
Wajen iyayennata ta koma,zuwa yanzu sun daina faÉ—an kowa ya karyar da kai yana nishi na wahala da yunwa.
Lokacin data faɗamusu yanda sukayi da tasi'un ba ƙaramin murna sukayi ba.
Biredi ya siya musu da zobo irinna É—urawar nan ganin sun fita hayyacinsu.
Kaman almajirai kuwa haka suke turawa a cikinsu,kowa so yake yayi maganin yunwarsa. Banda ruwan albarka babu abinda suke masa,kaman basune sukayi masa cin mutunci ba dayace neman auren atika,a ganinsu shi ba sa'anta bane,yanzu gashinan babu kunya suke masa godiya daya taimakesu.
(Shiyasa a duniya ba'a son kaci mutuncin mutum ko ya yake kuwa,saboda Allah ne kaÉ—ai yasan ranar da zai maka rana,a lokacin da bakayi tsammani ba. Allah yasa mu dace dai.)
Daff da magriba suka kamo hanyar garinnasu,tunda suka tafi wata shida sai yau zasu koma,dama ance in daÉ—i bai kawoka gida ba wuya ai zata kawo ka.
Shuru sukayi a cikin bodin motar a tsakiyar kayan miyan da bai siyar ba,sai wulla ido suke,ga motar batada gudu ko kaÉ—an,ko yaushe zasu isa oho.
Kaman a sama sukaji muryar tasi'un yana tashinsu,abin kunya sunyi bacci duk sunyi rugu rugu da tumatir É—insa,wani abinma hadda taruhu da tattasai,gasu da É—anyen ciwo a jikinsu.
Banda mutsu mutsu da nishin azaba babu abinda suke.
Motar ba wani tudu bane da ita,amma saida sukayi dagaske kafin suka iyah fitowa,ko tsayawa yimasa kyakykyawar godiya basuyi ba suka shige gida,dan basa cikin hankalinsu.
Lokacin gari duru duru yake ana shirin ƙiran assalatu.
Inna mairo ta fito da butarta zata shiga banÉ—aki sai ganin mutane tayi sun shigo gidan,salati tafara jiki yakama karkarwa,dan tayi zaton gamo tayi,saikuma ta kula ashe su gaji ne
"Gaji kuma?"
TafaÉ—a cikeda mamaki.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[07]

Butar hannunta ta ajiye tana kallonsu,sune kuma da gaske,tayiwa kanta wannan tambayar.
"Gaji kune da asubar nan haka,mai ya faru kukayi wujiga wujiga haka?"
Bude baki tayi zatai magana ƴar ta ƙarama ta rigata,tunda su ba ciwo a jikinsu.
"Yaya ce tayi soyayya da Alhaji,shine wasu sojoji sukayiwa su baba duka suka jefarmu a bola"
Kunya ce takama su kaman zasu nutse a wajen.
Saurin wayancewa inna mairo tayi,musamman ganin yanda gaji ke kallon Æ´ar tata farida kaman zata cinyeta É—anye.
"Ohh to Allah ya tsare gaba,yanzu kuzo ku zauna,barina fito daga banÉ—aki na haÉ—amuku ruwan wanka kuyi mamatsa jikinku."
Cije baki gaji tayi,so take tayi magana amma kuma tana tsoron kar inna mairo ta hana su ruwan kaman yanda tayi niyya.
Kafin gari ya waye duk sun wanke jikimsu sun sanja kaya wanda inna mairo ta É—auko musu a sashennasu,dan ko É—akinta basu bariba tun asubar,bare su taka cikin gidan suga mai ya sauyah.
A daren tayi musu abinci mai sauƙi sukaci,hankalinsu ya dawo kansu.
Da safe kuma tasiyo musu burofen da masu shago suka buÉ—e.
Chapter 10 · 0% Book details