← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 47

Sashe 11

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gaji ce tafito daga ɗakin tana kallon gidan,babu abinda ya sauya a cikinsa,saima fess da yayi kaman bashine sansanin shirgi ba lokacin da suke nan. Ƙofarsu ta nufah domin taga mai ya sauya,tun kafin ta ƙarisa tajiyo kukan saniya,abinne yabata mamaki,saniya kuma a ƙofarsu?.
Turus tayi ganin kewayen ƙofar tata cikeda abincin saniyar da kuma kashinta,wajen sai kace kewayen dabbobi.
Cije baki tayi tareda ƙiran sunan goje da ƙarfi har ƙasan maƙoshinta.
"Gojeeeeeee!!!"
"Na'am"
Taji ya amsa a bayanta.
Wani dum ƙirjinta ya doka saboda firgici,dan batayi tsammani yana gidan ba kuma ya jita,tafaɗa ne kawai yanda zuciyarta tafara tafasa.
"Miye kike ƙwalamin wannan ƙiran kaman zaki ƙare min suna daga dawowarki iyeee"
Diriricewa tayi tana inda inda,in a lokacin bayane zata iya maida masa magana,amma yanzu gani tayi gabaɗaya ya sauya mata,jikinsa ya sake murɗewa,gashin bakinsa sun sake tsayi,ga wani uban tabon yankan wuƙa a dantsensa na dama. Ji tayi kaman wani jaki yana tunkarota"
"Uhm dama dama bakomai bane,kawai gani nayi ka maida mana ƙofar kamar kewayen dabbobi daga tafiyarmu"
"To wa yace ku tafi É—in,sanda kuke nan na tasheku na saka ta ne,ina saida kuka tafi yawon maularku tukunna,kunje kun saida musu hali sun koroku rana tsaka,mutane sun zaman zamansu zaku dawo ku damesu. In nan ba inda zanje kuma ban sanja ba,duk wanda ya damu mutane ko ya nemi neman rigima,saina yanke masa wata gaba ta jikinsa,daga ke har mijinnaki da kuma tarin tsiyar Æ´aÆ´an ku"
Muryar inna mairo yaji,hakanne ya tsaya da yiwa gaji tatass wacce take gabansa,tana jinsa amma babu dama ta rama sai yace zai bugeta kokuma yasaka ta a kewayen karnukansa.
"Kai goje kaine fah bakada gaskiya anan wajen,saboda kai kasaka musu dabba a ƙofarsu,sannu kuma tayi magana kace ba madu ba bukar. Kaje ka sunce saniyarka ka maidata inda take da,wato gefen ƙofar ka,ni banga mai zakayi da saniya ba ma"
"Kyauta tace ta farko dana samu sanadin ƙarfina da ƙwazo nah,idan na ganta tana tunamin dani jarumine,dan haka babu inda zan kaita anan zata zauna a gidannan. Tunda kinyi magana zan turo Ragarus ya ɗauketa a wajen"
Cikin tafiya ta izzah ya nufi hanyar waje,wani baƙin kare yana binsa a baya..
Sai bayan ya fice tukunna gaji ta saki wani numfashi data riƙe tun ɗazu.
"Uhhh nina manta ma da wannan basamujen yana gidan,gabaɗaya mutum sai murɗewa yake kaman wani dodo...abinnan yana cimin tuwo a ƙwaryah,kaf cikin yarana babu wanda yake ɗaga cikin plastic na ruwa saboda lalaci,amma shi kalleshi har tanki ma zai iya ɗauka. Narasa mai yakika yimasa yana yaro ya zama haka,kaima da ka sani ai da kayiwa yaranka,waɗannan masu kama da agwagin"
Oh gaji har yanzu kina nan da É—abi'arki ta zagin Æ´aÆ´an ki,koma dai ya suke ai sune naki,kuma su Allah yabaki"
"Ehh zakice haka man saboda naki jarumine,nawa kuwa Æ´aÆ´an nasan in kinshiga É—aki dariya kike musu,kin gansu kaman buta"
Kasa riƙe dariyar ta inna mairo tayi,wanda hakan ya ƙara ƙular da gaji tazo har wuyah.
"Kinga ya isa haka ni bazan biyeki ba,kujira yaxo ya daukemuku saniyar ku gyara muhallinku ku koma"
"Mee kashin saniyar tasa na wata da watanni mu zamu gyara masa,zancen banza ma kenan,jakunan ku kuka maidamu keda shi komai,yanda kuke da iko da gidannan fah muma haka mukeda iko dashi"
Jijjiga kai inna Mairo tayi cikeda takaici,ta dawo ai za'a cigaba daga inda aka tsayah.
"Nina fara gajiyah da mitarki gaji,in sun dauke saniyar ku jirashi yazo ya gyara muku wajen,kuce sai ya tattare kashin tunda saniyarsa ce tayi"
Yawu gaji ta haɗiye muƙutt,saboda tasan inna Mairo gatse tayi mata,hakan bazai taba faruwa ba.

__***__

A zaune take a gaban wuta ta haɗa gumi sharkaff tana suyar awara,gabadaya hankalinta yana wajen,buƙatar ta ta gama soye uban taragon awarar dayake gabanta.
Dama sana'arta ce tun tale-tale kowa yasan ta da ita.
Atika ce ta shigo ƙofar da sauri daga wajen inna Mairo take,kana ganin yanda take zumuɗi kasan gulma ce take cinta a rai.
ÆŠaga kai gaji tayi ta kalleta tareda mikamata wata awarar wacce ta suyah.
"Hungo dan Allah atika zubawa farida Ta ɗari biyu ta kaiwa wani a waje,sannan kema kizo ki kintsa ki tafi wajen tallen ki,kuma maza ki hanzarta kada a gama siyan na kowa a bar naki yayi kwantai mana. Kince nayi miki da ƙwai nayi miki,amma tun ɗazu sai yada kai kike kinƙi tafiyah"
"Ohh gaji zan tafi dai,yaushe ma ranar tayine wai,wani abu fah nazo dashi nake son na faÉ—amiki. Wai kiji ashe Goje aure zayyi?"
Tsayawa ta juya awarar tayi tareda juyowa tana kallon Atika,alamu duk sun nuna bata yarda da abinda tace É—in ba"
"Ke bana son ƙarya,kaff garinnan wacece zata auri wannan dodon,in zakiyi ƙarya ma kiyi wacce kunne zai yarda da ita"
"Wlh gaji da gaske nake,kuma gobe nema ɗaurin auren,gashinan inna Mairo ta gyara ƙofar gojen,kuma yanzunan aka kawo mata saƙo,kayane a ciki sabi na mata ta siyah wai na Amaryar ne"
"Ke Æ´ar nan,Æ´ar gidan wanne shashan ubanne zai bawa goje Æ´ar sa,kalan ya danneta sai Æ´aÆ´an hanjinta sun fito nan take?"
"Uhm ai bakiji ma abinda naji bane jiya a wajen talle,har nunamin itama akayi,gata kyakykyawa da itah,ƴar gidan Mijin su inna rammah ce fah ƙawarki,wai a wajen caca dasukayi da goje ya cinyeshi,shine da bashida kuɗi yabashi ita"
Sakin baki gaji tayi tana kallon atika kaman ta samu TV.
"Duk yaushe haka ta faru a garin bansani ba uhm,barina gama suyar awarar nan zanje gidan naji komai ai"
"Ko kuma ki bari sai da daddare ba,kinga babu wanda zaisan kinje,ni labarin naji wai ƙawar indo ce ma nan maƙwantanmu"
"Wai tagamu da ƙaddara,muma da muke gida ɗaya dashi muke ganin takanmu balle ita mai zama dashi? Amma kuwa Mairo bata kyauta ba,duk ana wanann zancen bata faɗawa malam ba,saboda sun rainashi basa ganinsa a uban goje koh? Bari kuwa ya dawo da faɗamasa yanda ake ciki,duk wacce za'ayi ma ayi"
TafaÉ—a tana cigaba da suyar ta.

___***___

[Sumaimah a mahangar gani]
Chapter 11 · 0% Book details