← Book details Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Sanadin Caca Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Har na gama aikina na yau ko yaushe a gidan da safe,Ƙwalƙwalwata ta gagara barin Tunanomin abinda gojen yacemin,tabbas kam yanzu na yarda ba daidai yake da sauran mutane ba,wai a hakan ma yanda nake tunanin zayyi min bai yimin ba.
Na ƙara tabbatarwa bazan taba samun matsugunni a wajensa ba ballantana nayi wani tasiri a cikinta,amma kuma ta wani wajen a zuciyata yana cemin wataƙila tunda har ya yarda na taba kayansa zan iya samun nasara koda watarana ne. Duk da cewar ayyukan daya bani mutum ko ƴar sa ne bazai saka ba ballantana kuma matarsa,koda yake mai yasa hakan zai dameni,nasan dama bazan samu wannan matsayin ba,ga kuma.....
Firgit nayi na dawo daga duniyar tunanin jin an wullomin abu a jikina,É—aga ido nayi caraf sai a cikin na goje,wanda yake min kallo mai haÉ—e da harara.
Saurin sauƙe idona nayi,ananne naga ashe makulli ya wullomin,na dakinsa ne kenan,na faɗa a raina.
"Kije kewayen can saniya ta tana ciki,daga yau kulada ita yana hannunki,akwai abincin ta a gefen wajen,sannan ki cikamin randa ta kullum da ruwa,ki gyaramin É—aki waÉ—ancan yaran sun wargaza shi,amma ki tabbatar komai yana muhallinsa,naga kin iya wanki akwai kayana suma ki wanke su"
"Toh shikenan"
Har yakama hanyar fita waje sai kuma ya dawo,.
"Ko É—ayane ya kuskure vakiyi ba.......saikinyi É—iban ruwa sau ashirin kina yiwa gidannan ban ruwa,idan kuma ya wuce É—aya baki cikaba sai na rufeki a É—aki da su durwa,basai na faÉ—amiki abinda zasuyi ba kinsan menene"
Yana cikin maganar ne Æ´aÆ´an gaji suka shigo gidan da gudu sun dawo cin É—umame daga makaranta,gudu suke basu kulada wanda yake gabansu ba,aikuwa suka bangajeshi zasu wuce basuma kulaba.
Har sun kusa isa ƙofarsu ya daka musu tsawa.
"Kaiiii.....dukku ku dawo nan ku zube"
Wata karkarwa suke amma ba bakin magana,su haɗune,ƴar babbar itace mai bin atika,sai kuma ƙannenta biyu maza ɗaya mace,ƙaninta ne gaji take goyo ta yayeshi.
"Dan Allah yayah goje kayi......"
Kallon da yayi matane tayi shuru bata ƙarisa ba.
"Jeki ƙofata ki ɗaukomin bokitin danake zama,dama tunda kuka dawo babu wanda na saita a cikinku koh,ita kanta uwartaku dama na kula ta mantani har maganata take ina jiyota daga ɗakina. Ku fara tsallen ƙwado kuna zagaya gidannan,kuga ƴan iska koh.

Samun waje yayi ya zauna yana kallonsu suna kewaya gidan,banda ihu babu abinda suke,abinka da yara har tausayinsu ya kamani.
Bakiti na É—auka bayan gama yimasa sharar É—akin da kuma tsakar wajen,kayan da za'a wanke na zakuÉ—o a É—akinnasa masu É—an banzan datti,duk sun rine ga hamami kaman zan yi amai..
Ta gabansa na wuce na nufi hnayar waje É—ebo ruwan,haka kawai sainaji gidan yamin duhu rana É—aya,ashe gaji nafila ce akansa. Tunda nazo gidan yaune ya taba kaiwa har zuwa yanzu yana gidan..
Dana kawo bakin ƙofar gidan tsayawa nayi ina kallon wajen,nasan mutane zasuyi ta kallona suna maganganu akai,shiko kunya bayaji ace matarsa zata ɗebo ruwa,ko yara mata basa ɗiban ruwa balle matan aure,hmmm nice ma nake mutunta auren,shi mutumma baya mutuntawa ballantana wani aure a wajensa.
Tafiya nake kaina a ƙasa na nufi wajen ɗiban ruwan,Allah ya taimakeni ma babu nisa daga gidan..
Ban taba tunanin fitata tafarko a gidan É—iban ruwa zanje ba.
Sau uku nayi randar tasa ta cika,saniyar dayake faÉ—a itama na kai mata É—aya,saina sake É—ebo wasu guda biyu na wankin kayansa,nima saina haÉ—a da nawa ma na wanke..
Duk ɗiban ruwan danake ta gabansa nake wucewa,har sannan izaya yake yiwa yaran gaji bai gama ba,tabb lallai gaji tana tsoron goje,duk abinda yake shiru taƙi yin magana,yanda take da ƴaƴan nan kaman rayuwarta amma tayi shuru?
"Kutashi ku tafi,gobema ku sake tafiyah ta rashin ladabi,kuje ƙofar ku ku ƙiramin atika yanzunnan"
Yana cewa ya sallamesu da gudu suka shige ƙofar tasu suna kuka.
Can kaman bayan mintuna Kursiyyah ƴar babbar tafito daga ƙofar tana matsar hawaye.
"Yayah goje wai inji gaji batanan bata kwana a gida ba"
Dariyar gefen baki yayi yana jijjiga kai.
ÆŠaga murya yayi yanda gajin zatajishi.
"Ke gaji,wato ni zakiyiwa iya shege koh,makaho kika mayarni komai,yarinyar ba ita nagani cikin dare tashigo gidaba?. Kinsan Allah kafin na ƙirga Uku kota fito kokuma nazo da kaina na ɗauketa,abin kuma bazayyi muku kyau ba"
Ƙirgen zai fara,ganin abin zai baci nida kwainane cikin rawar murya nace.
"Uhmm....bata ƙofar inna gaji"
Wani kallo da yatsomin da É—azu nasamu ya manta da shafina.
"Tana ina toh,ohh daga zuwanki gidan kema har an fara munafurci dake ko?"
"Ahah ahah wlh ba haka bane,kawai ina kwance ne da daddare tace na buÉ—e mata shine......"
Bai bari na ƙarisa wanke kaina ba ya buɗe muryarsa yana ƙiran atika.
"Ke Atika wlh in baki fito daga É—akinnan ba idan nazo saina yayyaga ki"
Yana gama magana kiriff saiga Atika a waje tana rarraba ido,duk da tana ƙoƙarin boyewa amma kana ganin rawar da jikinta yake kasan tsoron karonnata dashi take.
Da hannunsa ya nuna mata gabansa taje ta tsugunna.
Sunkuyar dakai tayi takasa haÉ—a ido dashi.
"Uban me kukaje yi keda Sageer A asibiti jiyah?. Wato ciki kukayi tare saboda ku ga tantirai shine kuka zubar koh,kowa a wajen sai faÉ—a yake cewar ke Æ´ar gidanmuce,saboda ki jawo min raini a gari koh. Ku a hakan har shegune gu da zaku iya kashe rai,ko ni bana É—aukan rai sai mutum yamin laifi,shi cikin da kika yi fadamin wane laifi yayi."
"Wayyo dan Allah yayah goje kayi....."
"Shuru kada ki kuskura ki faramin wannan Kalmar da banaso É—in. Kinsan mandotary ne sai kin Kwashi naki kason,shima abokin shan shagalinnaki yana can wajen yarana suna morewa,ke kuma anan zan miki naki a gida.
Ke wakike kujera koh a sunan na yaran manzo(kursiyyah)je ki ɗaukomin wani cable na birkin keke yanan a maƙale a gefen ɗakina"
Jijjiga kai Atika tayi tana kuka jin abinda za'a É—auko,da alama dama kaman tasan karo. Ni da bani za'a duka bama nima karkarwar nake,wankin nake da sauri ina gurzarsa kar a haÉ—a dani.
Wacce aka aika ɗin ta tafi saigata da dawo kuwa,miƙa masa tayi yana karba tabar wajen,ƙofarsu ta shiga,da alama taje faɗawa uwarta abinda yake faruwa ne.
Mummurɗa shi yayi yai masa tuka,iya ƙarfinsa ya zage ya tsula mata a cinyah,wani ihu ta kurma wanda nasan ana jiyota a maƙwantansu,innalillahi yanda nake zatonsa ashe ya fi haka.
Tsula mata yake tana burburwa saida yayi mata Goma kafin ya dakata,nishi take tana maida ajiyar zuciya kafin ta tashi ta zauna,tana kaiwa hannun ta bangarori da dama na jikinta,inda duk zafin dukan yake ratsata.
"Kinsan dukan danayi miki na menene koh?"
"Jijjiga kai tayi alamar ba ta saniba"
Ohh baki ma san mai kikayimin ba,zaton ki dan kin sheqe ayar kine kaÉ—ai zan bata lokaci na wajen yimiki haka,kinada wannan darajar,ai ba sheqe ayah ba in kinaso kije kasata ma bai dameni ba,amma gonata da kika shiga shiyasa nake miki hukunci saboda karki sake shiga.
Meyasa kukaje asibiti kukace cikina ne a jikinki,wani na turoku bana son a sani kar asirina ya tonu. Koba haka kukace ba keda bunsurunnaki?"
"Eh.....eh haka muka ce"
"Meyasa to kuka ambaci sunana a sharholiyarku,wato saboda kun rainani koh,kin taba ganin nayi irin wannan ƙarƙantaccen aikin?"
"Ahah baka taba,sunƙi zubar mana da cikinne wai sai mun kawo shaidu,shine mukace naka ne,kace kuma idan kazo abin bazayyi kyau ba. Wlh ba hakan muke nufi ba,kawaidai mun faɗa ne dan suyi mana aikin"
Wata dariyah yasake yi ta gefen baki,kana ya sosa ƙeyarsa da kan cable ɗin..
"Lallai yarinyar nan kin dakeni da mamakinki,yanzu da badan yarona yazo ya faɗamin ba saboda ya jiku,saidai ayi ta faɗan na miki ciki a cikin gari,a zubarmin da mutunci. Ni bansani ba ashe so kike na miki ciki,toh shikenan bazan miki ba ni nafi ƙarfin haka,amma in hakan kikeso zan saka a sake yimiki wani,idan kikaje zubarwa kice goje ne yasaka ayimin,shine kuma,ya turo yace ya zubarmin....barinaje na dawo na kaiki cikin maza biyar su yayyagaki,wannan da kikayi ba iskanci bane ai"
Oh dama wannan laifin tayimasa shiyasa yake jibgarta,nifah nayi zaton ma bayaso ta dunga iskanci ne,tabbb lallai Atika ma tanada kasada sosai.
Wani ihu tafara tana haÉ—a hannaye,roqonsa take bilhaqqqi,amma saima ya rufe ido.
"Dan Allah dan ya rasulullahi Yaya goje kayi haƙuri,wlh bazan ƙaraba na tuba,gaji kizo kI ceceni wayyo gaji."
Tunda ake ƙwallon ball da ƴaƴan nata bata yi ko tari ba sai yanzu ta fito,haba a matsayinta na uwa kuma tana jin kukansu dole abin yayi mata zafi.
Da goje suka haÉ—a ido lokacin data fito É—in,kana ganin fuskarta kasan in ranta dubu ne to duk ya baci.
"Amma dai goje tunda ka daketa tabaka haƙuri ai shikenan zance ya wuce ko"
"A tunanin ki? Har yanzu banji muryar kaina tace na barta haka ba,kee tashi kije ranar can ki zauna"
Filin tsakar gidan ya nuna mata wanda yayi zafi zau da rana,ki saka gwiwoyinki a wajen ki tsaya haka,karki tashi har sai nazo na ce hakan. Ban gama dake ba tukunna,zanje ba sallami wancan abokin aikinnaki ne"
Har zai fita ya kalli gaji ya kalleni,wani dumm naji mai kuma nayi yanzu.
"Ban yarda ta tashi ba kokuma abata ƙwayar abinci ko ruwa,idan kika bata...naji labari saina sakaki a ɗaki da karnuka sun yayyagaki. Ke kuma idan ta bata abinci kokuma ta tashi a wajen baki faɗamin ba,nasamu labarin ke zan yiwa abinda na faɗa zanyi mata"
Ya ƙarisa maganar yana tabbatar min,ɗaga kai na fara ba tsayawa har ya fita ban dainaba.
Shanyar kayan dana wanke nake,sai ji nayi gaji takama kafaɗata ta jefar dani ƙasa,tohh ni kuma mai nayi,wato yakama dukan ƴaƴan ta tashaqa bari ta huce akaina ni marar galihu.
Kallonta nake da mamakin mai kuma nayi ni,ƙasar da take bakina nake sharewa,saboda yanda na kifu a bakin.
"Nikuma gaji mai nayi miki"
Yau ko inna ma bance ba,dan na kula matar batada darajar daza'a mutuntun tata,kuma ƴaƴan ta ma ai haka suke ƙiranta.
"Ohh baki ma san mai kikayimin ba koh? Nakula hadda wani sanja murya ma kike,dan kinga mijinki yayiwa Æ´aÆ´ana fata fata shine hakan yamiki daÉ—i koh?"
"Taya za'a duka wani mutum yaji daɗi,indai bashine marar imani ba,kuma dai naga kina gani wanda yayi dukan nima ba ƙyaleni yayi,bare kice nina zigashi"
"Zigo? Kima zigashin mana,kekam ai a tafin hannuna kike in shi ya gagareni,nasha neman maganin tanƙwasashi abu ya gagara,saboda asiri baya kamashi,amma kekam ina ba irin jikinsa ne dake ba koh. Wato saboda ke ga munafuka hadda faɗamasa atika a ɗakin mairo ta buya koh,ke a dole zakiyi gwaninta a wajen wadda bai ɗaukeki mutum bama ballantana kuma matarsa,saboda kallon kuɗin caca yake miki,ko saniyar daya ciyo a kalankuwa tafiki daraja a wajensa,ganinki kike mace amma keba mace bace,wacce namiji yakasa ɗaga ido yakalla za'a ƙira mace,kuma batun Atika yanzu zan dauketa a wajennan,inkin isa ki faɗa ki gani. Abinci kuma zanga wanda zai sake baki a gidannan,aiki kuma babu fashi saikinyishi"
Maganganu taci gaba da gasa min masu zafi,haushine ya turnuƙeni zuciyata tana zafi,ina na ɗebi iya inda zan iya ɗauka,dolene na fesar mata da sauran.
Kallonta nake tana ƙoƙarin isa inda atikan take.
"Hmmm wai gaji saboda kina matsayin matar ƙanin baban mijina,matsayin uwata aka baki ne,ke baki san in kinkai mutum bango ki dakata bane? Harda zaki ƙirani ba mace ba,shiyasa ai naga ƴarki da take kasa darajarta a waje kowa ya ɗauka kaman karya za'a ƙirata da mace koh,kokuma ke da bakisan soyayyar miji ba yanacan gidan karuwai a can yake wuni,ke bakida aiki sai dafawa ki ciyar masa da ƴaƴa za'a ƙiraki da macen. In kincika macen kema da ki hanashi zuwa wancan ƙazamin gidan mana.Ai gwanda ni ba mata yake biba ya ƙyaleni,ra'ayine bayayi,kekuwa fah yanason matan amma mai yasa ya tsallakeki.
Sannan dakike cewa wai inna isa na faÉ—amasa zatonki idan kin É—auketa a wajen zanyi shuru ne? Wlh saina faÉ—a,haka kawai ki ceceta nayi shuru ya gano ya fatattakani bai dameki ba ko,nina aiketa yawon sharholiyar komai.
Abinci kuma kada ki bayar,nima kuwa bazan sake miki komai na gidannan ba,inkin ban abinci nayi miki,in baki bani ba nima bazanyi ba,inji ce ni saida mai nayi aiki"
Ina gama faÉ—in haka nakama hanyar É—akina da sauri,saboda kada ta biyoni ta fatattaka ni kaman yanda ta naga tana huci,cike kuma da mamakin irin furucin dana yi.
Haba ai dole nayi,ko damo aka matsa ai dole yayi cizo,wanka zanyi na kwanta,nasan dole goje zai dawo basai dare ba,saboda ya ajiye atika a tsakar gidan. In yaso saina tambaye shi naje gidan su Shareefah,nasan zan samu abinda zanci a gidan.
Chapter 22 · 0% Book details