← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 24

Sashe 5

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama iyaka lips ya tura kofar parlorn ya shiga, wata kyakyawar matashiyar yarinya ce ta amsa tana me Miƙewa tsaye
"sannu da zuwa big bro"
"Asma'u ya kike?"
"Lafiya ƙalau big bro"
Murad da shima ya miƙe ya kara so ya miƙa mishi hannu yana cewa
"an tashi lafiya Yaya?"
"Alhamdulillah Ammi fa?"
"tana sama ta haura yin walaha"

Duba time yayi ya gyaÉ—a kai sbd almost 10 sun bata lokaci a holdup na garin Abuja sannan da nisa tsakaninsu da gidan iyayen nashi be ce komai ba ya nufi saman.

Se a lokacin Murad ya kalli Aysher hannu ya É—aga mata
"Æ´ar bororo ashe tare kuke da yaya?"
Murmushin sanayya ta sakar mai tana gaishe shi da fulatanci ya amsa da Hausa, ta gaida Asma'u da taji Abban ya faÉ—a itama cikin murmushi ta amsa da fulatancin da ta dage take koyo.

"Ya Murad ina kuka samo ta? Ko da ita kuka dawo?"
Asma'un ta faÉ—a tana sake kallon Aysher da irin kyaunta Dukda har yanzu ba wani girma ne tayi ba don bata da girman jiki, kyau ne dae da gashi masha Allah.
"Ɗiyar Big bro ce ƴar wajen marigayi Ya Isma'il shine Big bro ya ɗauko ta riƙo"
Wani tsalle Asma'un ta daka ta dire
"yeeeyyy yanzu ne zan koyi fulatanci da tushe tunda daga Alhj har Ammi da Hajiya sun ƙi koyamin"

Ita dae Aysher se kallon yadda Asma'un ke murna take, a shekaru zata iya cewa Asma'un nan tayi ishirin amma tana abunta kaman Æ´ar yarinya, kamu hannun Aysher tayi tace
"É—iyarmu zo zauna kina ta tsaye nan fa gidan kakanninki ne!"

Da Hausa tayi maganan se Aysher ta É—an yi murmushi ba tare da ta fahimta ba seda taga tana nuna mata kujera ta zauna
"wani zama zata yi auta? Kin san Big bro sarai karki kaita ta gaida Ammi da Hajiya zauna kiyi ta zuba mata surutu"
Uhmm ta faɗa tana Miƙewa ta rike hannun Aysher suka haura sama, banda kamshi babu abunda gidan ke fitarwa komai kal kal cike da kyau da tsari, ɗakin Ammi suka shiga da sallama.

Tana zaune kan sallaya yana zaune daga gabanta ya tankwashe kafafu ba wani hira suke ba tunda suka gaisa suke zaune haka, Asma'u na shigowa tace
"Ammi kallo É—iyarmu so masha Allah, Namesake É—inki ce ma"
Kallon wa ya tambaye ki da Emran ya mata yasa tayi shiru, hannu Ammi ta miƙa mata cikin harshen fulatanci tace
"zo nan É—iyata, matso"
Zuwa tayi ta kama hannun matar tana yaba kirkin su lallai Abba da matarshi kam nasu kaÉ—an ne har gwara Abban ma.

Gaishe da Ammi tayi Ammi ta amsa cikin kulawa tana mata gaisuwar mahaifinta ta dinga yi mishi Adu'a Aysher na amsawa.

"I will transfer some token to ur account, anjima ki É—auke ta ki samar mata gurl stuffs, make sure u get anything in be yi ba just give me a call"
Cikin murna Asma'u ta amsa don ta san zata samu kuÉ—i, Yayansu be iya aika da kuÉ—i kaÉ—an ba sam.

Ammi tace
"Ki kaita su gaisa da Hajiyarku.."

A hankali Emran yace
"Ammi ta fara karyawa pls"
Ya faÉ—i hakan ne sanin a kauye zuwa yanzu sede abincin rana, shi karan kanshi aure ne ya sabar mishi karyawa a makare da yake gida ko seven baya kaiwa be karya ba.

Kallonshi Ammi tayi ya fuske yana danna wayarshi bata ce komai ba har Asma'u ta fice da Aysher
"yanzu a haka zaka iya riƙe marainiya?"
Ta faɗa tana kallonshi, kanshi ƙasa ya amsa
"Ammi in shaa Allah zan yi kokarin ganin ta koyi girki sbd ta dinga dafawa kanta"

"kai kuma fa? Haka zaka ke zama da yunwa sbd wani tsari naku na banza?"
Shiru yayi ya ma yi mamakin yadda ta iya maganar don ya santa in abunda ya shafe shi ne sede Hajiya ita bata saka kanta sam, yawanci in ze zo sede su gaisa su yi ta zama shiru in ya gaji ya miƙe ya fice.

"Ammi bara na isa wurin Hajiya"
Girgiza kai tayi tace
"a gaishe ta"
Miƙewa yayi ya fice ta bishi da kallo.

A kan carpet ya samu Aysher tana cin jollof Rice da aka yi shi da nama zuku zuku, yayi washar se kamshi yake, Asma'u na zaune tana danna waya yayinda Murad ke kallon Tv
"Murad"
Ta Kira sunan yana dan tsayawa hannunshi É—aya cikin aljihu
"I will send some token to ur account u should find a very good school within Abuja on monday ka kai yarinyar nan, pls make sure the school is standard nd good"

"Ok sir, in shaa Allah"
Juyawa yayi da nufin tafiya part din Hajiya da sauri Aysher ta saki cokalin ta miƙe don binshi, Asma'u tayi hanzarin katse ta
"zauna Aysher ki ci abincinki ba yanzu zaki tafi ba"
Zama tayi, tsoro take kar ta mishi laifi ta lura magana na mishi wahala, shiyasa yake ta sha ma kowa kamshi yake magana É—aiÉ—ai kaman me kirge...

Bayan ta gama Asma'u ta sake janta sama zuwa É—akinta da ya sha kyale kyale komai pink su wallsticker ne su waye ne babu abunda babu, tura ta bayi tayi ta sake wanka ta bata towel bayan ta fito, ta ajiye mata manta ta shafa ta bata turare ta nunnuna mata inda zata fesa bayan ta gama ta ajiye mata wani dogon rigar atmfaarta da yayi mata kaÉ—an amma tana matukar son atamphar shiyasa take ta ajiyar shi, sakawa tayi masha Allah, da yake beda breast curve irin flay din nan ne se ya mata kyau be Mata wani yawa ba, dankwalin Asma'u ta É—aura mata ta bata gyale bata iya yafawa ba sun saba yawo haka se gyalen ke ta faÉ—uwa tana rikowa amma masha Allah tayi kyau abunta.

Gyalen Egyptian Abaya me walwalin dake jikinta Asma'u ta warware ta yafa a kanta ta zari car key É—in ta, wayanta IPhone 15 pro max dake chargy ta zare tana dagawa fuskanshi ya kunnu zaro idanu tayi tana kallon yawan kudin da Big bro ya saka mata, kai ta gyaÉ—a tace.
"Ah lallai Big bro an yi É—iya"

Fitowa suka yi zuwa É—akin Ammi bata nan, kila ta sauka se suka sauka kawai zuwa kasa, anan suka sameta tana kallon sunnah Tv sallama suka mata tana maimaitawa Asma'u su shiga wurin Hajiya fa kan su bar gidan.

Ɗaya building ɗin suka nufa Aysher bata da magana yayinda Asma'u ke da surutu sede bata iya fulatanci ba hakan ne yasa dole suke tafiyar shiru shiru, Da Sallama suka shiga parlorn wadda shima a tsare yake gwanin kyau da burgewa, wata kyakyawar farar mace ce zaune bisa carpet ta miƙe kafafunta tana ta aikin mita da alama da Abba take sbd ganinshi da Aysher tayi a kwance kan three seater dake facing matar tsawon shi yayima kujerar yawa don haka kafafunshi ya miƙe su a chan saman kujeran ya zubawa matar idanu se kallonta yake, sallamar su ce ya katse ta wadda hakan ya saka shi shima lumshe idanu.

A ƙasa Aysher ta zube tana kwasar gaisuwa matar ma na da fara'a da son mutane a take ta sake da ita ta fara mata gaisuwar mahaifinta, daga nan Asma'u ta miƙe
"Hajiya bari muje sayayya"
"Toh Allah y tsare se kun dawo"
Kan su amsa wayar Emran ta É—auki tsuwwa, jin wayar wurin aiki ne ysa ya buÉ—e idanu ya É—aga ya kara a kunne, mintuna biyu kan ya sauko da kafafunshi yana furta
"subhallah! On my way pls do the needful, arrange everything in order..."
Yana sauke wayan ya dubi Hajiya
"Hajiya ina da emergency bari naje"
Hajiya tace
"hala lamarin babba ne bokan turai?"
"Accident ne wai rodi ya shiga har cikin left abdominal artery na matar she needs urgent surgery i hope she lives..."
Yana kai nan yayi saurin ficewa tana mishi Adu'a.

Fitowa suka yi, a hankali Aysher ta tambayi Asma'u
"Aunty Asma'u aikin me Abba ke yi?"

Tunani Asma'u ta tafi kan tace
"wai Alhajinmu?"
Girgiza kai Aysher tayi
"A'a Abbana!"
Dariya Asma'u ta saka sossai....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuÉ—i ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faÉ—akantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰

                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaÉ—ayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

FREE PAGE 4

"Wai Big bro?"
Kai Aysher ta dage daidai suna shiga hadaddiyar SUV lighter brown wadda ya kasance motar Asma'un ce, bayan sun zauna tana yiwa motar key tace
"Ai Big bro babban surgeon ne da ba Nigeria kaɗai ba har ƙasar waje suna matukar ji dashi, duk wani harka da ya shafi tsaga mutum musamman a ciki to ya kware anan, na san Dukda ruga kike kila ba zaki rasa jin CITY CLINIC ba nan ne asibitin shi baya zuwa ko ina banda kasashen waje in kana bukatar aikinshi kayi booking appointment ka zo asibitin shi ya maka aiki, kai ko a Abuja babu asibitin da yake musu aiki, kuma kin san me?"
Chapter 5 · 0% Book details