← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 24

Sashe 11

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaÉ—ayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis  marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta  zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar  mai gida ko saurayi  kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai  sauki ke ma ki je ki nemi  na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo

FREE PAGE 7

"Naina? Ya subhallah! Are u out of ur sense me wannan?"
Ya faɗa yana shiga cikin parlorn, Asma'u da ta kara so wurin tayi saurin duƙawa tana taɓo Ayshern jin tayi shiru kaman wacce ta suma ko wani abu taji Nainan na cewa
"Yes, am out my sense tunda idanunka sun rufe, yarinya ba gidan ta ba na ubanta ba muzo mu tsaya muna danna door Bell sama da mintuna biyar har ka koma ka É—auko keys naka daga car da ka bari kan ta wani zo ta buÉ—e kuma ta tsaya akan hanya, akan dalilin me? Tana da gadon gidan ne ko da kuÉ—in babanta aka haÉ—a aka gina?"

Juyawa tayi kan Aysher da Asma'u ta É—ago ta, tana aika mata wani banzan kallo tace
"Mayya kawai"
Daga haka ta ja tsaki tayi wucewarta
Dafe goshinshi yayi ya ɗan murza kan ya ja tsaki, idanunshi akan Aysher da ta share hawayen fuskanta ya ɗan kalli wuyanta da duk Damammiyar nonon ya ɓata ya ɗauke kai yace
"Je ki wanke jikinki"

Asma'u haushi ne ya zo mata har wuya, shikenan abunda ze ce? Ji fa maganganun da matarshi ta gama faÉ—a, dama sun san ba iya tsawatar mata yake ba amma kuma ai wannan wulakanci ne, cikin Muryar kuka Aysher tace

"Kayi haƙuri"
Kan ta juya ta nufi É—akin ta, tausayinta ne ya kama Asma'u, ita ya kamata a ba hakuri amma shi take bai wa.

ÆŠauke idanunshi yayi daga kallonta bayan ta rufe kofar ya sauke kan nonon dake zube yace
"Ammi ne ta aiko ki dashi?"

Ta san yadda yake matukar so, kuma duk sadda ze shiga gida se ya sha na Alhaji idan Ammi tayi, kusan abunda kaÉ—ai yake sha a kofar Ammi kenan don na Hajiya baya mishi daaÉ—in na Ammi.

"Aysher ce tayi"

Sake kallon Nonon yayi se ya nufi dining inda yaga kwanoni.

Asma'u kuma ta soma gyara wurin, bubbude kulolin yayi, baze iya cewa ga sadda yaga kuloli haka akan dining ɗin gidanshi ba, kai be ma taɓa gani ba sbd abubuwan da yake dafawa daga kwai, doya, dankali se ɗan spaghetti su kuma daga tukunya se plate ne, amarcinsu ma ba a Nigeria suka ci ba shiyasa ba'a aiko musu da abinci ba, sannan Asma'u ma baze ce ta taɓa zuwa gidan nashi tayi ko mintuna goma bane ze iya kirga sau nawa tazo amma yanzu yadda ya gantan nan ya san ta jima kuma me yiwuwa ita tayi girkin.

Dama yunwa yake ji banda coffee daya sha a office tun safe be ci komai ba gashi yanzu almost to 3, don yana sauƙa Juma'a Naina ta kirashi akan motar ta ya tsaya shine ya biya ya ɗauko ta suka barwa machanic motar.

Zama yayi yana jiran Asma'u, bayan ta gama gyara wurin tazo ta soma zuba mishi abincin, a ranta tana raya eh ai mune kake yiwa muzurai, idan kaganmu a wuri ko Hajiya sede tayi serving naka amma idan bama nan kana iya shiga kitchen ka girka ka kaiwa wata katuwa har kan gado, kaman ta ja tsaki amma ta san halin shi baya so kwata kwata a ja mishi tsaki nace Toh wanzami baya son jarfa akwai wadda yskai shi jan tsaki kuwa? Ai ko tsaka ya sara mishi.

Nonon ta zuba mai a wani bowl me garai garai ta tura mishi ta zauna ta cigaba da cin abincinta, a nan ne ta gaishe shi ya amsa yana cin abincin da cokali.

"Tun yaushe kike nan?"
"Tun 12:30 nazo, na kawowa Aysher ɗinkunanta shine ta roƙi na koya mata anfani da abubuwan kitchen nan"

Kai ya gyaÉ—a, tuwon ya ture Dukda yayi daaÉ—i sossai ya janyo bowl din ya fara shan furar, wow ko na Ammi se haka ko da shike baze yi mamaki ba Fulanin ruga ce.

"Aysher kam lafiya? Duk zumudin shan Nonon kuma ya tafi ne?"
Ta faɗa tana Miƙewa bayan ta gama cin abincin jin shiru shiru Ayshern bata fito ba.

Ya shanye wadda ta saka mishi har ya kara be ce mata komai ba har ta wuce ɗakin Ayshern, a kwance ta sameta sanye da plain riga Onion Colour har ƙasa, daidai cikinta ya kama se ya sake daga kasa.

"Aysher kwanciya kika yi? Abincin fa?"

"He'i am Aunty Asmy(ya isheni)"

"wani irin ya isheki me kika ci da ze ishe ki? Tashi oya mu wuce ki ci abinci"
Duk yadda ta so ƙi haka Asma'u ta sakata a gaba se tace tana tsoron ta sake laifi bazata fita ba se duk sun shige.

Taɓe baki Asma'u tayi ta fice taje ta zuba mata abincin ta sake zuba mata furar yana kallonta be ce komai ba ta wuce zuwa ɗakin Ayshern.

Basu suka fito ba se dab magarib da Asma'u zata wuce, kaman kar ta tafi haka Aysher taji don sun sha hira har class na fulatanci suka yi, ita kuma Asma'u ta koya mata assignments dinta na biology da physics, har mota ta raka ta, dubawa tayi ta É—auko choculates ta mika mata tace
"É—iyarmu a sha wannan kuma kar ayi kuka"
Dariya Aysher ta saki itama Asma'u tayi dariya tana cewa
"ko kefa da kin yi wani kicin kicin da fuska, yauwa ga Big bro din nan ma"

Ta faÉ—a tana kallon shi yana tahowa da alama yayi alwala don gyara hannun tsadaddiyar shadda dake jikinshi yake.

"Dama tafiya zaki yi ba sallama?"
Ya faÉ—a yana kallon Asma'un.

"Big bro na kira line naka be shiga ba, ɗiyarmu kuma na tsoron matar Abbanta ta ƙi zuwa ta maka magana"

Kallon Aysher yayi da kyawawan idanunshi masu girma da suke a lumshe, ta bata fuska sbd abunda Asma'u ke cewa kaman zata yi kuka, ya maida kallonshi kan Asma'u yace
"ke kuma da yake gidan baƙon ki ne ko?"
Ya ƙarasa yana mika mata bunch din 1k yace
"Ki gaida su Ammi"

Tunda ya faɗi hakan ta san yau kila be samu ya shiga gidan bane, godiya ta mishi ya wuce abunshi. Aysher na riƙe da choculates ɗin ta har Asma'u ta fice kan ta dawo ta shige ɗakinta.

Washegari da wuri ta tashi sbd dokin yin girki, dama haka take inde zata yi girki tayi ta É—oki kenan, kitchen ta wuce bayan tayi brush tana nazarin abunda zata girka, tas ta bubbude lockers din ta ja baya har da sa hannu a haba tana gyara glass dinta da ya karawa fuskarta kyau.

Cikin sassanyar muryarta tace
"Ina son kunu amma ba kamu, ko nayi Basise ne?"
Basise wani nauyin kunu ne da mutanen yola ko Taraba ke yi da danyen shinkafa na tuwo, kai ta gyaÉ—a cike da gamsuwa ta dibi gyaÉ—a markadadde daga gani ta san markaden yola ne sbd sune suke yinshi yayi tililis mai ya kwanta me yawa a samanshi kaman kayi ta lasa kuma duk jimawar da ze yi baya lalacewa sbd wannan mai kuma an soya gyaÉ—ar sama sama.

Tacewa tayi ta zuba a tukunya, a wurin kunna gas din kuwa seda aka yi da gaske sbd tsoro irin nata, bayan ta kunna ta ɗaura tukunyar taje ta dibi shinkafa rabin cup ta wanke ta ajiye, tsamiya ta jiƙa a cup kan ta fara tunanin mahaɗar kunun nata, nan ta yanke yin ƙosai, wake ta diba ta surfe ta wanke ta haɗa da atturugu da albasa ta sa a buchimix blender din da Antynta ta tabbatar mata komai yana nikawa, a take ta markade yayi tilis ta juye a roba, da gudu ta koma wurin gyadarta ganin ya kusa zuba ta juye shinkafar ta tsaya tayi ta motsawa na mintuna kan ta ajiye ludayin ta koma ta buga kosan sossai.

Tana yi tana dawowa ta duba kunun seda shinkafar ya nuna tilis ta kashe gas ɗin kan ta zuba ruwan tsamiyarta ta ta kara juyawa ta zuba sugar ta sauke, a wani madaidaicin jug me garai garai ta juye sbd shi baya son flask ze dafu sossai yayi kauri shiyasa ta barshi a jug, komawa tayi ta fara suyan ƙosan cikin annashuwa take komai.
Chapter 11 · 0% Book details