← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Principal da suka taho da manyan malaman makarantar ya faÉ—a, dama a ka'idar makarantar malamai basa tafiya se sun tabbatar da babu dalibin da ya rage a makarantar, kuma se sun yi zagaye sun gama tabbatar da komai intact kan principal ke sallamansu.

Da idanunshi da gabaɗaya suka birkice ya kallesu gabaɗayansu, se kuma ya juya da hannunshi wadda ke free ya nuna su Maryam da har yanzu zaune take a ƙasa mufida da Amina na sangame a tsaye

"you should make sure among them babu wacce ta bar makarantar nan, and you all also"
Yayi maganan kaman yana cikin asibitinshi ne da ya san kowa na karkashin ikonshi, ba neman izini ya basu ba umarni da gargadi ne ke tafe cikin Muryar shi, be sake cewa komai ba ya juya yana riƙe da hannunta gudun kar ta faɗi suka nufi inda ya ajiye motan shi, mazauninshi ya buɗe wato driver seat ya zaunar da ita, ya miƙa hannunshi ya ɗauko savage ya soma goge mata jinin fuskanta da har ya diddiga a uniform ɗinta, ruwa ya sa a tafin hannunshi ya wanke mata fuskan ya fiddo fari kal din hankey ya sa mata a hannunta me lafiya

"share fuskan"

A hankali ta share, duk gashin gaban goshinta ya sake mammanewa, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani Brown cover na glass me azababben kyau ya buÉ—e, se ga rantsatsen glass kwance a ciki frame É—in Light peach ne da fari fari yayi matukar kyau ya fiddo ya sanya mata a ido, lokaci É—aya fuskanshi ya bayyana mata tar seda ta tsorata ganin yadda fuskar nan tashi ke a É—aure, Dukda yadda yake ji ya ga kyaun da glass É—in yayi mata dama kuma ya raya hakan sbd a wani shopping da suka fita da Naina ya ga frame É—in É—auke da lence É—in shi sede ba medicated ba, be bari Naina ta ga sadda ya saya ba sbd ya san fitinarta, asibitin ya kai da yake ranar da ya kaita asibiti tana mp ya ga number É—in lens din nata so kawai faÉ—a musu yayi ga abunda yake so a yanka a sa a frame É—in.

A yau da zasu taho ya tsaya asibitin ya karɓa ya sa a aljihu shine be cire ba se yanzu.

"Why??"
Ya tambaya yana kallonta da idanunshin nan da be ɓoye zafin da zuciyarshi ke ciki ba.

Muryarta na rawa idanunta na sake cika da hawaye tace
"Kayi haƙuri Abba, tsoro na ji... Ina tsoron kar daga zuwana in fara baka matsala da ciwon kai, sannan su ɗin sun fi ƙarfina in ka duba tazarar matsayi dake tsakanin....."

"Enough pls!"
Ya faÉ—a da É—an tsawa, da sauri ta matsa baya hawayen da suka cika idanunta suka soma gangara, hannunshi ya sa ya murza goshinshi tare da sakin dogon tsaki me sauti.

Ji yake kaman ya mammaketa itama ko ze huce kaÉ—an.
"Me kike nufi? Da nace zan zama tamkar mahaifi a gare ki na karɓi amanar ki kina tunanin akwai wani wadda ze iya sake ɗaga miki yatsa in kyale? Karki kuskura ki sake haɗa matsayin ki da na yaran nan saboda ko ta ina basu kai ki ba bare su kamo ki har su zarta ki"

Cije lip dinshi na kasa yayi.
"Next time irin haka ta faru baki faɗamin ba har na gane ke zan soma sassaɓawa.. Mu je"
Ya juya, da sauri ta fito ta rufe motar jikinta har rawan tsoro yake yadda yake faÉ—an kaman ze maretan itama.

"Show me the principal's office"
Yace yana kallonta, da yatsa tayi saurin nuna mishi arean yayi gaba ta bishi a baya idanunta cike da tsoron abunda ze faru.

Kaman yadda ya faÉ—a É—in kuwa suna nan zazzaune suna jiranshi don tambayar duniya sun yiwa su Maryam babu wacce ta iya cewa komai, tsoro ne da razani cike da idanunsu, rashin gaskiya baro baro ya bayyana a fuskokinsu.

"Ta ina zamu fara? Ku zan yi ƙara ko iyayensu?"
Yayi maganan daga tsaye ba tare da ya zauna ba cikin harshen turanci.

"Yallaɓai da dae ka zauna mun ji Duka sides of the story sbd har yanzu mu bamu san Meke faruwa ba, su kuma basu ce komai ba"
V.p ya faÉ—a cike da girmamawa da suke dashi ga guardians din students nasu.

Zama yayi HM ya ɗauko mai ruwan sanyi a frigde ɗin Principal ɗin ya bashi, karɓa yayi ya sha sossai kan ya ajiye, a natse ya faɗa musu duk abunda ya faru ya kuma fiddo video din a matsayin shaida, gabaɗayansu sun girgiza sam basu san abu haka na faruwa a cikin makarantar ba, hakuri suka soma bashi a take yace be san shi ba, ya birkice musu da kyar ya hakura gobe a dawo in yaso za'a kira iyayensu se a haɗu gabaɗaya.

Daga makarantar asibiti ya nufa da ita, Dr Safwan ya kira wanda shine yake kula da duk abunda ya shafi harkar ƙashi a asibitin ya tabbatar mai yana office kai tsaye nan suka yada zango, da sauri ya miƙe tsaye ganin shugabansu ne da kanshi a cikin office ɗin nashi yau Dukda ya kan yi ziyarar bazata sbd masu wasa da aiki amma Dukda haka ya ɗan tsorata kaɗan don ya san prof Emran bashi da sauƙi.

"Sir ai da ka kira ni se in sameka ka zo nan da kan ka?"

"Dr daughter na ce ta samu É—an problem a hannu nake so ka duba mata"
Yayi maganan yana zama.

Daga tsayen da take ta gaishe da Dr Safwan É—in tana kallon kwarangwal dake jejjere daban daban a kan desk É—in nashi.
Amsawa yayi yana zagayawa ya isa gareta
"mu ga hannun?"

Miƙa mishi tayi ya duba, Dukda yayi tunanin gaucewar ƙashin ne amma sbd gudun laifi yasa ya kaita wurin xray yayi mata cikin minti biyar ya fito ya duba, aiko dae gocewar ne ze yi gyara.

"Zaki É—an daure don ze miki zafi"

Kanta ta gyaÉ—a duk tsoro ya cika ranta, runtse idanu tayi da karfi jin ya fara kokarin gyarawa seda kuwa tayi kuka, likitan na murmushi yace
"babba dake É—an wannan kike yiwa kuka?"

"Allah ba É—a bane Dr."
Bata san ta faɗi hakan ba ma, tana kallon hannun  a lokaci ɗaya tana share hawayen fuskanta, har ya zagaye da farin bandage bayan ya shafa wani abu kaman mai, kallon Abban nata tayi idanunshi na kan wayanshi, be ɗago ba seda Dr Safwan yace
"ranka ya dade an gama, ba wani abu in shaa Allah"

Tsam ya miƙe yana mika mishi hannu
"thank you Dr"
Yana faÉ—an haka ya juya ya fice tabi bayanshi, office nashi ya shiga ta bishi anan ya fidda First aid yayi mata dressing na goshinta, in ya kawo Cotton me É—auke da spirit ya É—an manna tace "shhhh" se ya dankara mata Harara haka zata tsaya sbd tsoro har suka gama.

Lokacin har an yi la'asar seda yaje yayi sallah a masallacin asibitin kan ya dawo suka tafi, yunwa take ji kaman taci babu, tana Allah allah ya tsaya ya saya musu don ta san kila yanzu kam gidanshi suka nufa ba gidan Alhj ba, kaman kuwa ya ji ya tsaya restuarant ya saya musu abinci, har sun bar wurin ma Naina ta kirashi, da Bluetooth na motan ya amsa cikin Muryar shin nan yace

"ya aka yi ne?"
"Ƙalau hun, ina kayi haka tunda muka dawo baka shiga ko cikin gida ba"

"nace ya aka yi?"
Ya sake maimaita maganan shi na fari ba tare da ya bata amsar tambayar tata ba.

"Eyyaaa in zaka dawo yanzu pls baby na craving KFC kitchen ka biya ka samo min"

Sun kusa isa ma a sadda tayi kiran amma be ce komai ba bayan Ok, ya juya akalar motan É—an kallonshi Aysher tayi yunwa take ji wlh, gashi yanzu yamma ya soman nan holdup na garin in ya rikesu taya zasu koma har ta ci abinci ta cire wannan uniform da take ji ya takurata, baki ta É—an turo tana sake kallonshi se suka haÉ—a idanu...

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuÉ—i ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faÉ—akantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰

                          🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 14

*Albishirinku💃 Toh gobe Free Page ze ƙare in shaa Allahu wacce bata saya ba kuma tana son jin yadda zata kaya a gidan Abba se ta garzayo ta saya*

"Raki kam kin ƙware a kai amma baki iya kwatan kanki a faɗa ba, ɗauki abincin ki ci"
Ya faÉ—a a fuske kaman ba shi yayi maganan ba.
Murmushi ta saki tana mamakin hallayyar Abban nata, kaman me gani har hanji, juyawa tayi ta ɗauko, tint ne motar kuma ba zata iya hakuri har su koma ba ga holdups ya fara, abincinta take ci hankalin ta kwance sbd ko ta inda take ma Abban baya kallo se waya da ya kan amsa, kan su je KFC ta gama ledar na ajiye kan kafafunta, seda ya buɗe motan ya fita kan ya miƙa hannu ya ɗauki ledan ya rufe motar tana kallonshi ya cillar a bin kan yayi ciki, wani murmushin ta kuma saki.

Babu wanda ya sake magana har suka iso gida, shi ya kwashi ledojin don tayi niyyar É—auka ya hanata, da sallama ta shiga parlorn Naina tayi saurin tasowa sede ganin Aysher ne yasa ta dakata tana kallonta sama da kasa, ita har ga Allah ta ma mance da wanzuwar yarinyar

"Ina yini Aunty Naina? Kun dawo lafiya?"
Ta faÉ—a cikin girmamawa.
Chapter 22 · 0% Book details