← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 24

Sashe 23

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki ta É—an ja kan tace
"lfy" shima sbd zura mata idanu da Emran yayi ne, ledojin ta karɓa don tana ji kaman ana yasa a cikinta, be zauna ba yabi bayan Aysher don shiga ɗakinshi ya watsa ruwa kan Magrib, daidai zata shiga ɗaki yace

"Yau 27 in case kin ji wani ciwo makamancin na wanchan watan don't seat alone by yourself in pain, hope am clear?".

Da sauri ta amsa kanta ƙasa ta kuma shige daki lokaci ɗaya, a jikin kofa ta tsaya ita har ta ma mance wlh cikin dabara ta zare uniform din ta ta shiga wanka sauri sauri sbd sallahn da bata yi ba, Sharp Sharp ta fito tayi rama Sallar da ake binta anan ta kwanta sbd ta gaji sossai, bata wani jima ba aka yi Magrib ta miƙe ta gabatar ta ɗan yi karatun alqur'ani yau ko malaminta kila ya zo ya gaji da zama ya tafi be ganta ba, bayan tayi isha ta miƙe ta ɗan saka turare kan ta zura kayan bacci, farin doguwar riga wacce tsawon ta daidai sharabarta be ida isa idon sawu ba ta kwanta...

Washegari da safe seda ta shiga bayin ta ga uniform ɗin ta a bucket bazata iya wankewa ba sbd hannunta kuma bata da wani a gidan yana gidan Ammi, alwala tayi ta zo tayi Sallar asuba sbd yunwar da take ji ta haɗa tea ta sha da biscuit, bayan ta gama taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin riga A shape na atampha da ya mugun amsar ta, bazata iya dauri ba ko gashin bata sake taje shi ba sbd hannunta ta ɗauko gyale da ya shiga da kayan ta yafa daga kanta, zama tayi tana tunanin abunda ka iya faruwa a makaranta yau sbd ta lura Abba bashi da sauƙi sam idan ranshi ya ɓaci...

Jiya sossai ya tuna mata da baffanta, duk sanyinshi a kan yaranshi shi wuta ne, Dukda be san komai ba ya kare ta ya bata goyon baya, hannunta ta sa ta shafa glasses din da yayi mata kyau a ido sossai tana ɗan murmushi lallai Abba na da taste me kyau kaman ya san zata buƙata a lokacin ya taho dashi shi da be taɓa ma zuwa makarantar ba ma...

Kanta ta sunkuyar tuna abunda ya faÉ—a na karshe kan ta shiga É—aki, ko date É—in watanta be mance ba, kunyar hakan ya lullube ta...

Knocking da aka yi ne ya sakata saurin Miƙewa taje ta buɗe kofan, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihun three quater fari sol dake jikinshi ya hadata da baƙar shirt marar nauyi.
"Ina kwana Abba"

Tayi saurin faɗa tana ɗan duƙawa, hannunta ya kalla yace
"Lafiya ya jiki?"

"Da sauƙi Babu komai"

Yana kallon goshinta yace
"kije kitchen ki É—auki abinci, where is ur uniform kika sa personal?"

"Na jiya ya ɓaci kuma ba zan iya wankewa ba, sauran kuma suna gidan Ammi"
Ta faÉ—a cikin sanyin muryarta.

Kai ya gyaÉ—a ya juya ya wuce, fita tayi zuwa kitchen É—in, doya ce fari ya dafa da faÉ—i fadi yayi egg sauce.
"Abban nan na nan kaman hawainiya, babu kalar da baya iya zama"

Tayi maganan a fili tana zuba abincin, a nan kitchen ɗin ta zauna ta ci ta koshi kan ta fito parlor tana rike da ruwan faro, se gashi shima ya fito a shirye cikin grey suit da farin ƴar ciki, ba karamin kyau yyi ba, hannunshi riƙe da briefcase ɗayan na ɗan gyara bakin nectie ɗin shi yace
"mu je"

Bayanshi ta bi, yanzu wannan wai har wasan kasa fa yayi da baffanta, to ya aka yi baffanta ya fishi tsufa? Dukda ba wai baffan tsoho bane sede bazaka haÉ—a shi da Abba ba, komai nashi daban, kai hatta murjewan skin ko Murad dake matashi me jini baze nuna mishi komai ba, da wannan tunani suka mota, ya mata wuta suka fice, be tsaya ko ina ba se harabar makarantar tasu kai tsaye suka dangana da office na principal.

Shi da mahaifin Amina suka samu se wasu authorities na makarantar, a hankali ta kai idanunta kan fuskanshi ya murtuke fuskan alamar ba wasa, hannu ya miƙa musu daya bayan ɗaya kan ya zauna itama ta zauna nan ƙasan rug din kaman yadda Amina ke zaune, mahaifin Mufida da ita ne suka shigo tana sanye da uniform, kaman yadda Amina ke sanye da uniform saɓanin Aysher, daga karshe mahaifin Maryam ne suka shigo a tare, babban ɗan siyasa ne da kowa ya sani me mukami don dasu ake damawa a ƙasar, renon da yayiwa yaranshi shine be san faɗuwa ba a komai yana so su kasance masu nasara hakan ysa yaran basu damu da wa zasu taka ba wurin kaiwa ga nasarar tasu wanda dae dae yake da faɗuwa warwas.

Da Adu'a aka fara kan aka baiwa Aysher damar faÉ—an duk abunda ya faru, turancinta be nuna ba kaman na su se ta kasa magana, kallon Abban tayi ya gyaÉ—a mata kai, kokarin soma magana tayi amma da É—ari-É—ari kuma É—aÉ—É—aya take fidda kalaman gudun kwafsi, ta kuma yi kokari sossai wadda wasu a ciki ke ganin rigima da iyayi ne yasa take maganan a haka, Maryam V.p ya kalla yace

"Maryam Usman an yi haka?"

Kallon mahaifinta tayi a tsorace ta gyaÉ—a kai.

"Mufida, Amina Meyasa kuka musgunawa Aisha? Ta muku wani abu ne?"
Principal ya tmbya
Suka girgiza kai
Tsawa v.p academic ya daka musu
"baku da baki ne ana magana kuna kallon mutane?"

"Bata mana komai ba"

Mahaifin Mufida ne yace
"Ashe ke shashace? Yar uwar ki mace mufida ita kika ciwa zarafi? Shine da na tambaye ki kika ce baki san dalilin nema na da makaranta suke ba? Zaki yi bayani"

Mahaifin Amina ma faÉ—a ya rufe ta dashi sossai kaman ze daketa, shi dae Abba be ce komai ba banda kallonsu da yake.

Mahaifin Maryam yace
"toh tunda dae abu ya riga ya faru faÉ—a ko maida zance bashi da amfani ai yara ne, duk shiriritarsu be kamata ana kaiwa zuci ba bare har a kai ga saka hannu jikin Æ´ar da ba'a san zafinta ba"

Kallon shi Emran yayi se ya É—an murmusa yace
"daaÉ—in abun Æ´a ai bata fi Æ´a ba, tunda kuma babu wanda ze ci kashi a cikinsu ai zancen yara be taso ba, yanzu dae ba wannan ba ina jiran jin an kwatarwa tawa É—iyar hakkin ta"
Ya faÉ—a yana directing maganan to principal.

"Bisa laifin da aka same su dashi a gaskiya idan ita bata hakura ba, to hukuncin Maryam shine kora daga makaranta su kuma mufida da Amina za'a basu suspension na sati uku uku"

"saboda kawai faÉ—an yara? Akan hakan zaku kore ta? Kun ma san wanene ni kuwa da kuke zancen korin Æ´a ta daga makaranta?"

"Ko waye kai baka fi karfin doka tayi aiki a kanka ba, penalties din ma yayi sauƙi idan da ta nine we are going to court and they could definately pay a fine or even end up in jail depending yadda shari'a tazo"

Kallon Dr Emran kawai Alhj usman ke yi, yadda yake gayamishi magana kai tsaye yayi matukar bashi mamaki, be gama mamaki ba seda ya ga principal yayi printing expulsion letter yayi signing aka bawa Maryam da ta soma kuka, mufida da Amina kuwa aka basu suspension, ita dae Aisha in ba don mugun kallon da Abban ya mata ba ta so tace ta yafe musu a barsu a makarantarsu tunda ita ta zo ta same su.

Mahaifin Maryam se faÉ—a yake harda in ya ga dama bazata yi karatu a Nigeria ba ma, makarantar banza makarantar wofi.

Emran dae murmushi ya mishi wanda kai tsaye yake nufin wannan matsalar ka ce...

Murɗawar da mararta yayi ne yasa tayi saurin duƙar da kai tana runtse ido, to fa wannan abu haka ze ta mata? A take gumi ya soma tsatsafo mata a Goshi, ko hakurin da malaman da kuma iyayen mufida da Amina suka yi ta basu ita ba ji take ba, ta de san mahaifin Maryam ya jima da ficewa kuma itama ta bi bayanshi.

Idanunshi ya sakar mata na mintuna kan Tsam ya miƙe
"Allah ya kiyaye gaba, Aysher?"

ÆŠagowa tayi idanunta har sun chanza kala
"mu je" ya faɗa chan ƙasan makoshi.

Sallama yayiwa malaman suna ta kara bashi hakuri shi kam hankalin shi na kanta, a dudduke ta isa motan ta haÉ—a kai da gwiwa.

"Sorry"
Ya faɗa cikin kulawa yana tada motar be tsaya ko ina ba se asibiti, Dr Hafsa ya kira tun kan su isa, a office ɗin shi tayi mata allura, kaman wanchan karon shi ya fita ya nema mata pad, da ya dawo tayi bacci zama suka yi da Dr Hafsa yana tambayarta yadda za'a yi ta samu sauƙi sbd be kamata kowani wata ta sha wannan wahalar ba.

Bayani ta mishi mata kala kala ne, kila in tayi aure ta daena kila kuma in ta haihu, amma saukinta a daena wannan allura tayi ta amfani da lipton me zafi da kayan kamshi da kuma lemon sannan ta koyi amfani da ruwan zafi a mararta daga ta soma jin alama, ya tabbatar mata in ta farka ze tura ta se tayi mata duk bayanin da ya kamata tare da mata godiya, Miƙewa tayi ta fice tana mamakin shi ita bata san haka boss ɗin nasu yake ba sam, ji shi so simple and caring.

Da ta farka yau ma a bayi ta gyara Kanta Allah ma ya sa bata ɓaci ba tukuna, abinci ta gani kan table ta ɗauka ta ci, ta sake kwanciya idanunta na zagaye office ɗin, zuwa yanzu har ta san komai na kan office ɗin sbd yawan zuwa, knocking da aka yi ya sakata Miƙewa taje ta buɗe, Dr Hafsa ce.

Cikin girmamawa ta gaisheta don ko ba'a faɗa ba Dr Hafsa zata iya haifar ta, dubata tayi ta bata shawarwari masu yawa kan ta fice Aisha na mata godiya, se after asr ya dawo da alama duk ya gaji, sannu ta mishi se kuma ta miƙe Tsam ganin ya zauna a cikin kujerun taje wurin frigde ta ɗauko mai ruwa da cup daga kan frigde din.
Chapter 23 · 0% Book details