← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 24

Sashe 12

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iskar bakin shi yake hurawa wadda ke fitowa da zufa sbd gudun da yake yi na motsa jiki, wuyanshi maƙale da karamin towel, daga kanshi head Phone ne me kyau, riga marar hannu ne jikinsa wadda ya fidda murdaddun damatsansa alamar be ɗauki motsa jiki da wasa ba, dogon wandon Puma ne jikinshi se rufaffun takalma duka baƙake, sun yi nasarar fito da kyakyawar skin ɗin sa fari kal, kwantaccen sajenshi se digar zufa suke har cikin tattausan gashin kansa  duk da haka wani masifaffen kamshi yake fitarwa..

Tsagaita jogging É—in yayi ya buÉ—e parlorn ya shiga, ko kan ya kai tsakiya ya tsaya chak yana nazarin kamshin da ya cike parlorn wadda babu tantama daga kitchen yake fitowa, ko ba'a faÉ—a ba ya san Aysher ce a kitchen nan don in Kaga Naina a kitchen É—aukar cup ne ko plate se kuma in babu ruwa se a frigde na kitchen.

Har kaman ze wuce zuwa ɗakinshi ya watsa ruwa se kuma ya karkata ya nufi kitchen ɗin, daga bakin kofa ya ja birki ya tsura mata mayun idanunshi yana mamaki ganin yadda take aiki hankali kwance fuskanta cike da annashuwa wadda ze iya cewa banda jiya zuwan Asma'u se kuma yau be taɓa ganin hakan a fuskanta ba.

Riga da wando baby pink na Cotton ne a jikinta, kanta babu dankwali se gashinta da ta kama, fuskarta fayau se murmushi take tana kwashe abunda yafi kyautata zaton ƙosai ne.

Ita kuwa tana cikin aikinta ta soma jin sassanyar kamshi wadda a wurin mutum ɗaya tak ta sanshi na ratsa kofofin hancinta, yatsina fuska tayi to ko don bata san yan birni sossai bane take tunanin shine kaɗai me irin wannan turare? Oho ta taɓe baki tana cigaba da aikinta a hankali taji inuwar mutum gefen ta a razane ta daka tsalle hakan yasa mai fallatsuwa a hannunta, ihu ta tsala tana yarfe hannun idanunta dake nuna firgici zube a kanshi.

Da hanzari ya riƙo hannun yana cewa
"Subhallah! Me hakan? Baki da hankali ne?"

Hawaye ta fara wani na koran wani bata iya ta sake buɗe baki da niyyar magana ba, duba hannun yayi har ya soma tashi sbd jar fatar ta, gishiri ya ɗauka ya zuba mata a wurin yana sake kallon hannun, ya kalleta se Shagwaɓe fuska take..

"Next time idan kin tsorata Naji ko da wasa kin yi ihu i will deal with you, baki san Allah ake ambato ba in an tsorata?"
Yadda ya sauke maganan da natsuwa cikin husky masculine voice nashi yasa ta kau da kai daga kallonshi tace
"in sha Allah zan kiyaye, ina kwana Abba?"

Ya ɗan yi shiru cikin natsuwar shi da kamalar da be ɓoye kanshi ba daga dabi'arshi yace
"Lafiya, me kike yi?"

Se lokacin ta kula da gas dake kunne har man ya fara konewa Allah ma ya sa ta gama se ta kai hannu ta kashe tace
"girki nake"

"wa ya koya miki?"
Ya tsinci kanshi da tambayarta Dukda ya tashi a gidansu yaga kannenshi na girki sede zaman kasashen Turai da É—abi'ar matarshi yasa yake ganin kowace yarinya ba lalle ta iya girki ba barin ma wannan da bata wuce 16 ba.

Murmushi me sauti tayi wadda baze ce ya taɓa ganin tayi ba tace
"Nene na mana, ai ni tun ina da shekara bakwai take bani girki, ni dae na en gayun nan ne ban iya ba"

Murmushi shima yyi wadda iyaka lebenshi don shi ba ma'abocin dariya bane, murmushin ma ba ko yaushe zaka iya katarin gani a fuskarsa ba, ya kai hannu ya ɗauki kosan ɗaya ya kai baki, lumshe idanunshi yayi ya buɗe yana taunawa a hankali ita kuwa duk ta saki baki da hanci da ido tana kallonshi tana jira yayi compliment, ɗan kallonta yayi se ya yamutsa fuska kaman be yi daaɗi ba, yayi gaba yana taɓe baki ya buɗe jug din ya kalli kunun kan ya juya ya fara tafiya har ya kai kofa ya dakata yace

"lemme fresh up"
Ya fice yana murmushi.

Da gudu taje ta É—auki kosan É—aya ta sa a baki tana jujjuya idanu..
"Wallahi yayi daaÉ—i Abbaaa"
Ta faÉ—a kaman zata yi kuka.

Hannunta ta duba seda ya tashi dama jikinta bashi da kyau sam akan irin abubuwan nan, a kula ta sa ta kai dining, ta kai jug É—in ta lura kaman a birni ya zama dole ka kai abinci dining in ka gama ne oho!

Dawowa kitchen É—in tayi ta tattare komai ta É—auraye abubuwan da tayi anfani dasu, ta kintsa komai a mazauninshi ta fito kenan da niyyan zuwa É—akinta don yi wanka se gashi ya fito, kamshin shi ya cika parlorn gabaÉ—aya kananun kaya ne sanye a jikinshi wadda suka matukar amsarshi, yana tafiya cikin natsuwar shi da tsantsar kamala, dining ya nufa ya zauna.

Har tayi kaman zata wuce se ta dawo, zuwa tayi kan dining É—in ta fara zuzzuba mishi, bayan ta gama ta tura mai, cokali ya É—auka ya dibi kunun da tunda ya gani yake son sha sbd abunda yake kauna ne yana shirin kaiwa baki yaji an yi sama da cokalin.....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuÉ—i ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faÉ—akantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰

                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaÉ—ayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo

FREE PAGE 8

"What sort of Nonsense is this?"
Ya dakawa Naina tsawa yana kaucewa kunun ya zube a ƙasa instead of jikinshi.
Aysher kam kallon Naina kawai take dake sanye da karamar sky blue nighty da ko cinyarta be gama rufewa ba, yana da tsiririn hannu gashin da babu tantama na doki ne Dukda yadda aka gyara shi aka kalkaleshi don ya zama kaman na mutum hakan be hana shi bayyana ba rabi a zube a kirjinta rabi a bayanta..

"Emran please! Ni kake faÉ—awa haka? Why are you eating this? Yaushe ma ka fara cin irin waennan regular foods É—in kai dake da kyankyami ba ko wani hannu ne ze dafa ya baka ka ci ba?"

Danne fushinshi yake kokarin yi kaman yadda ya saba, tafin hannunshi da ya jike da zufa Dukda Acn parlorn da komai ya kai ya murza goshinshi ya ja tsaki, a lokaci É—aya ya É—an ciza harshenshi he looks so cute and charming da fushin..

Shi karan kanshi ya san ba abincin kowa yake iya ci ba but this girl from day one da ya soma ganinta ya tabbatar ko me ta bashi he will not hesitate kuma ya san saboda yana iya cin komai da ya fito daga gidan Isma'il babu tantama ne, so why all the fuss?

"Naina leave my sight, just go"
Ya bata umarni yana me zama ya ɗauki sabon cokali ya bar na ƙasan ya fara shan kununshi, kaman ta makuro shi don haushi juyawa tayi ga Aysher dake tsaye cikin tsoro ta buga mata banzan Harara kan ta wuce kaman iska, kallonshi Aysher tayi cikin mamakin yadda baya tsawaita fushi idan ta fahimce shi, sannan da yayi ta magana gwara yayi shiru, kitchen ta koma ta ɗauko mop ta zo ta gyara wurin kan ta wuce daki be ce mata komai ba.

Bayan tayi wanka ta fito ta zo ta ci nata a nan parlorn tana kallo, har ta gama babu wadda ya fito, Miƙewa tayi ta fito tsakar gidan ta fara ɗan zagaye anan ta ga wani karamin hanya me ɗauke da furanni daban daban masu kyau, hanyar tabi tana mamakin nan ɗin kuma ina ne? A hankali ta bayyana cikin wani lambu me masifaffen kyau bata san sadda ta buɗe baki tana karewa kyaun wurin kallo ba.
Chapter 12 · 0% Book details