← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa tayi ta fito tana shirin yiwa Asma'u knocking se gata ta fito
"É—iyarmu ya aka yi ne?"

Cikin jin daaÉ—in yadda Asma'un ta koma mata kaman da ta ce
"Aunty Asmy ko kin kira Abba kin ji sun isa lafiya?"

Murmushi Asma'u ta saki tace
"sun isa lafiya ya kira Ammi, anjima se in kirashi ku gaisa tunda har kin fara kewar su"
Dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba.

"Yauwa ya jikinki? Me yake damun ki daman?"
Asma'u ta faÉ—a suna sauka downstairs
"ciwon ciki, wlh na É—auka mutuwa zan yi ai duk son da kika koya min na choculates na hakura dashi na rage sbd Abba ya ce shine ya janyo"

Dariya Asma'u tayi sossai tana cewa
"Allah sarki sannu ko, ba zaki mutu ba in shaa Allah se buruka sun cika, amma dama yana miki ne shan choculates ɗin ya ƙara shi?"

"Ban taɓa yi ba ma se wannan"
Ta faÉ—a tana jin kunya, da mamaki Asma'u da har ta fara zuba musu abinci ta kalleta lallai tayi delay, parlor suka dawo suka ci abincin a tare suna hira bayan isha suka yi wurin Hajiya ta fi Ammi sakewa da hira anan suka yi ta hirar ruga da abubuwan cikinta wanda duk suka yi kewa.

Misalin karfe tara na dare wayan Hajiya yayi ringing ta É—aga da sallama se kuma fuskanta ya washe da fara'a tana ambaton sunan Emran
"Alhamdulillah kun sauƙa lafiya dae kam?"

Ta É—an yi shiru kan tace
"masha Allah, ina Nainan ina mata sannu da hanya"

Shiru ta É—an yi se ta sake cewa
"gasu nan ma muna ta hira dasu"

"Asma'u karɓi"
Ta faɗa tana miƙawa Asma'un waya.

A ladabce ta gaishe shi, bayan nan ta É—an yi shiru se kuma lokaci lokaci take cewa to ko in shaa Allahu.
Se kuma ta kalli Aysher don kaman tambayarta yayi.

"Gata nan, dama dazu ta gama tambayata ko mun yi waya kun sauƙa lafiya!"
Ta faɗa tana miƙa mata wayar.

Karɓa tayi cikin yanayin sanyin ta ta saka wayan a kunne tare da sallama, shima ya amsa ba tare da ta bari yayi magana ba ta fara gaisheshi
"Alhamdulillah"
Shine amsar da ya bata se kuma ya É—aura da
"Ga Asma'u nan duk abunda kike buƙata ki faɗa mata zata kirani ta sanarmin, na manta da safe ban baki pocket money ba na sanya mata a account ɗin ta zata cire ta baki, ayi karatu a kuma kula"

Kanta na ƙasa kaman tana gabanshi tace
"in shaa Allahu, Na gode Allah ya saka da alkhairi Abba ya bada sa'ar abunda aka je nema"

Chan ƙasa ya amsa da Ameen tare da yanke wayar, saukewa tayi ta bi da kallo se ta saki ɗan murmushi kan ta miƙawa Hajiya da suka cigaba da hirarsu da Asma'u.

Ganin tana ta hamma ne ga gobe akwai school yasa suka yiwa hajiyar sallama suka nufi part É—in Ammi, a hankali Asma'u tace
"Ni kam É—iyarmu ko kin san idan wannan jinin ya É—auke akwai wankan da ake yi nashi na daban?"

Kanta ta É—an sunkuyar kan tace
"Eh Aunty Asma'u an koyar damu a cikin fiqhu"

"Kinga faÉ—amin yadda ake in ma kin mance wani wuri se in tuna miki don fa Abbanki yace in tabbatar kin iya yadda addini ya koyar"

"innalillahi....Abban ne yace hakan?"
Tayi maganan kaman zata saki kuka wadda ya saka Asma'u kwashewa da dariya, tana ta kwaɓe fuska wai ita kunya ta faɗawa Asma'u yadda ake yin daki daki ta kuwa iya ɗin babu wani kuskure.

"Masha Allah kin yi kokari, yanzu je ki kwanta sbd school kar ki makara Abbanki yace baya son hirar banza da wofi"

Murmushi kawai tayi tace
"Toh se da safe"

"Allah ya bamu alkhairi"

Haka ta cigaba da rayuwa a gidan, zata iya cewa gidan ya fi mata chan gidan sau dubu saboda tana samun yin hira da mutane kuma a sake take babu me mata kallon kyara ko tsangwama se ma janyota jiki, Ammi kullum se ta bata kudin break Dukda ta faɗa mata Abba ya bata kuma suna nan bata kashewa sossai se tace ta kara, idan weekend ne ba zuwa makaranta ta kan raka Asma'u unguwa in zata fita irin wurin Ƙawayenta ko Saloon ko kuma kasuwa, ta fannin girki sossai take sake koyan irin na zamani a gidan sbd in har tana nan bata taɓa zama a yi girki ba ita, tana nan ciki ta kan tambaye su abunda bata sani ba ko bata gane ba.

Ta fannin assignments ma bata wani shan wahala Aunty Asmyn ke koya mata in aka basu, ga Ya Murad da kullum dare tare suke hiransu ya kan kuma sayo musu kayan makulashe su rage dare dashi, bata daddara ba ko in ce ta mance ne oho choculates kam suna sha kaman ba gobe da Asma'u don ita ma gwanar zaƙi ce.

A kwana a tashi seda ta shafe sati uku curr a gidan, har kuma lokacin Su Abban basu dawo ba kuma bata sake waya dashi ba tun wayan da suka yi randa suka isa, yau ya kama Litinin cikin sauri sauri ta sauko sbd letti da ta ɗan yi wurin shiri ta isa gaban dining ta duƙa ta gaida Ammi, fuskanta a sake ta amsa ta tana cewa
"jiya ba kin biye wa Asma'u kuka raba dare kuna hira ba gata chan tana bacci suna hutu ke kin makara zaki je a zane ki a banza"

Kanta ta duƙar tana ɗan murmushi ba tare da tace komai ba
"tashi maza ki ci abinci ki samu ki wuce"

Sharp Sharp ta ci farin doya da kuli da aka yi wadda yaji man hannu da albasa tana ci tana haɗawa da tea bayan ta gama ta miƙe tana rataya school bag tace
"Ammi na tafi"

"Allah ya tsare se kin dawo"

Da gudu gudu ta fice ta shiga mota tana gaida driver É—in su ya amsa kaman kullum kan suka fice zuwa makarantar.

Yau ake fidda sakamakon kuri'a da aka yi na face of the school, so bayan an yi period uku na farko ba'a sake komawa aji har a tashi, za'a tafi students hall a sanar a kuma É—auki gwarzuwan hotuna da uniform É—inta yadda za'a wanke su manya manya a manna a halls da gaban gate din makarantar.

Bata wani ci abun kirki ba a break sbd har lokacin tana jin cikinta a cike yake daman doya ba dae riƙe ciki ba, kai tsaye daga cafteria hannunta rike da Fanta na gwangwani da ta saya bata ma bude ba aka buga seniors suka fara koran yara zuwa students hall, zama suka yiyyi, malamai biyu ne a stage din mace da namiji, bayan sun zauna suka sake Miƙewa suka miƙa musu gaisuwa, suka amsa Muryar namijin radau sbd shine yake riƙe da mic ɗin, bayan ya basu umarnin zama suka zauna.

Cikin harshen turanci ya fara magana
"kaman yadda kuka sani kuma muka saba, duk farkon session muna yin wannan gasa ta face of school, wannan shekarar ma bata sauya zani ba ranar Juma'a an yi zaɓe mun tara kuri'u na duka Junior and senior section kaman yadda kuka sani babu wanda makaranta ta cire a wannana gaasa ko ɗan js1 ne yaci lallai lallai shi ko ita za'a ba wa, Toh dae Alhamdulillah mun samu mun kirga kuri'u a weekend yau a yanzu kuma zaku ji sakamako"

Kowa sai ya juya ya kalli Maryam dake ta kanainaya Allah kaɗai ya san kuɗin da tayi ta kwasa daga ɗakin daddynta tana zuwa tana kashewa ɗalibai don ta saye su su zaɓe ta, ta saka buri da hope ɗin ta akan wannan karon ma ita ce zata ci babu tantama har ta gama ba za'a tsige hoton ta a fuskan makarantar ba, se murmushi take.

Kashe wutan hall ɗin aka yi aka bar dim Light se na stage kawai, gyaran murya malamar da ta karɓa tayi ta sake gaishe da ɗalibai kan tace
"So the one with the hightest vote among the selected students of year is....!"
Se ta É—an yi shiru kan da karfi tace
"Aysher Isma'il!!!!"

Sowaa me karfi hall ɗin ya ɗauka a sadda spot Light ya dallare Aysher dake zaune rike da Fanta a hannunta, ita har ga Allah tsorata ma tayi hakan yasa manyan idanunta kara girma da haske se sheki suke yi, Maryam Usman da taji abun kaman sauƙar aradu tayi saurin Miƙewa tsaye tana dafe kirji nasara abu ne me matukar muhimmanci a gareta kaman yadda mahaifinta kan kwaɗaitar mata a koyaushe a komai a kuma ko ina ta kasance me kwato nasara ko ta halin yaya, bata san ta rikice ba seda kawarta mufida Umar ta janyota ta zaunar da ita
"natsu mana baki ga kowa kallonki yake ba?"

Murya na rawa tace
"yarinyar nan tayi nasarar karya min record Mufida I'm screwed daddy ya samu labari kam na gama kaÉ—ewa!"

"Aysher Isma'il come over" da Aunty Doris ke ta maimaitawa ne yasa ta Miƙewa tana sake damke fantar hannunta, hantar cikinta se kaɗawa yake in ta tuna Maryam daga gefe, har ga Allah abunda yasa take bari suke mata abunda suka yi niyya banbancin matsayi ne, su ƴaƴan masu dashi ne ita kuma ba ƴar kowa ba.

Kunna wutan hall É—in aka yi dallllll a sadda ta hau stage É—in, Allah ya sa ma ita É—in me tsabta ce uniform É—inta kal kal gashi sabo don kwata kwata wata na biyu kenan suke ciki a makarantar don suna shirin 2nd C.A test ne kuma ba ya wuce sati tsakaninshi da revision se exams da compilation, kayanta ya sha karin guga, gashinta dake gyare sbd Saloon da suka je da weekend da Aunty Asmeey se sheki yake gyaran da aka mata wannan karon raba gashin gida biyu aka yi se aka kwantar akan goshinta ya koma baya, yayi lublub tun tana kunyar zuwa makarantar haka har ta saba.

Murmushin da malaman suke mata da kuma sowar É—aliban ya bata kwarin gwiwar sakin murmushi me kyau wadda ya bayyana dimples É—inta duk biyu da fararen hakwaran ta farare suka bayyana, nan me hoton ya matso ya fara É—aukarta kala kala se murmushi take saki.
Chapter 20 · 0% Book details