← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 24

Sashe 3

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naina Adam shine sunanta ita ɗin cikakkiyar ƴar kasuwa ce da ta samu shedar kamallah digiri har biyu a harkar kasuwanci, hakan ya bata damar jan ragamar kanfanunnukan mahaifinta da ya kasance hamshakin attajiri a Arewacin Nijeriya, ƙaninta be zaɓi kasuwanci ba kuma su biyu ne kadai Allah ya bashi hakan yasa ta jajirce take kuma kai akan duk wani al'amari na companies ɗin su na *Adams industries* ita ɗin tana da son a san ita wata ce, kaman yadda Allah yayi ta me kyau tana son komai nata ya kasance me kyau kuma na daban ne hakan yasa a koyaushe in ta tuna Emran mai yaƙi take aure se taji kanta yayi sama, kaman duk duniya ba na biyunta.

Naina bata da son mutane ko jansu a jiki a ganinta kowa yayi rayuwarshi yafi, ta tsani talaka bare wani suna wai talauci, ita kanta kawai ta sani se family ɗin ta, sam bata son ganin wani ya raɓe su har familyn mijinta kuwa.

har Nameer ya ajiyeta kofan gida bata daena kananun mita ba ita babban haushin ta yadda yarinyar zata zauna dasu dindindin, ko da ta shiga gidan direct bangarenta tayi ta wuce bayi ta soma da cire kayan nan a cewar ta ya kwashi ƙarnin nono ta zube su cikin laundry bag dake bayin ta isa chan inda aka keɓe don wanka seda ta fara sakin shower ya jiƙe daga kanta har kafafunta a cewarta ɗauraye datti kan ta isa ga jaccuzi ta haɗa ruwa ta shiga tana relaxing, ta jima sossai kan tayi wanka a bayin tayi ta kwalkwale kwalkwalenta su skin care routine da dae sauransu kan ta fito ta sa karamar shirt da wando ta haye gado don baccin huce gajiya..

Tunda suka doshi cikin Layin take ta aikin kallon irin ɓarin kuɗaɗe da aka yi a gidajen da suke zagaye da Layin, babu gidan da zaka kirashi tsoho don kowanne fentinshi na kyalli da ɗaukar idanu, fari tas ɗin gidan da fence ɗin shi be cika tsai ba zagaye da electric wire sbd tsaro gabanshi ɗauke da wasu irin flower masu ɗauke hankali da kawatuwa, gate ɗin shi Black da yaji ado da gold taga Murad yayi horn kaman mintuna biyu taga gate din ya zuge da kanshi a hankali ya siɗaɗa motar ciki, baki sake galala take kallon gidan.

Idan suka shiga birnin yola da Baffanta ta kan ce mishi waenda suke gidajen birni sun ji daaÉ—i kuma suna aljannar duniya bata san akwai inda ya take waenchan da take santi ba, gidan ba dublex bane flat ne da yake kaman an rakubeshi a dunkule a gefen fankacecen tsakar gidan da yaji ado da flowers daban daban, motoci basu wuci shidda bane a parking lot É—in sede kowanne ka kalla ka san mota ce da ta amsa sunanta, dubanta Murad yayi ganin yadda take ta kallon cikin gidan da take ta hangen glass yafi ginin dake jiki ta waje yawa, irin glass me garai garai da kana iya hangar wadda ke waje ko yake ciki..

"Aisha zan tafi"
"Ina zaki tafi?"
Ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausar ta, yana mata alama yadda zata gane da kyau..
"Babanmu ni da Ya Emran yana jirana akwai takaddu da zan kai mishi"
"useni ta accam ha É—o wala mo mi andi, yiwu saare mai bana ha (Ayya karka barni a nan babu wadda na sani, kalli fa gidan kaman a mafarki)"
Ta faÉ—a idanunta na yin rau rau sam be gane ba shi kam, sede ya fahimci a tsorace take.
"Matar Yaya na ciki, muje in raka ki parlor zaku zauna tare"
Yana maganar ne yana alama da hannu sbd ta fahimta, kai ta gyaÉ—a Dukda ta kula matar Æ´ar wulakanci ce, ko da shi ke ba ita kadai ba har mijinta ma É—an wulakanci ne wannan Murad din ne kawai me kirki, da in ya san baze iya kula da ita ba Meyasa be barta a rugar su ba, tana tunanin ne tana turo É—an karamin bakin ta Red dashi sharrr.
Seda Murad ya buÉ—e mata kofa ta shiga rungume da kullin kayanta kan ya juya ya koma da sauri sauri sbd Alhajinsu dake ta kiran shi.

Tsayuwa tayi tana kallon farare sol ɗin sofas ɗin daga gani ba karamin taushi zasu yi ba, komai na parlorn daga fari se lighter Brown wadda ma kaɗan kaɗan ne mixture ɗin, dan kadan gefen gini da aka yi ado dashi se na carpert kaɗan, se na wasu vanity trays parlorn ba wani hayaniya, sallama tayi tayi shiru tun tana tsaye har ta gaji a hankali ta ɗosana ɗuwawunta kan kujerar ai da gudu ta miƙe jin suna shirin burmawa da ita tsabar laushinsu, gefe ta koma ta zauna daga ƙasan farin tiles ɗin tare da zabga tagumi.

Wasa wasa tun tana saƙe-saƙenta har ta koma shiru a hankali ta juye zuwa abun tausayi sbd yunwar da ya fara sasakar cikinta tun safe banda madarar shanu tafasasshe da tasha bata ci komai ba gashi tayi amai, bata ji motsin kowa ba bare ta nemi agaji gashi har duhu ya fara rufuwa bata yi ko sallahr la'asar ba, hawaye ta fara akai akai tana sharewa sbd yadda suke zuba cike da tausayin kanta, me yafi mutuwa ciwo da firgici? Da yanzu suna chan da Baffanta da Nene da kuma zayyad(ƙaninta) suna hirarrakinsu da tsokanar juna cikin raha.

A hankali ta kai kwance akan tiles ɗin da sanyin shi ke ratsa har cikin ƙashinta, jikinta na ɗaukar rawa, tafi awanni biyu cikin wannan hali kan a hankali ta soma jin sassanyar kamshi me ratsa zuciya da sanya natsuwa, kamshin da ta riga ta san me shi a yinin yau kawai sbd yadda yake da masifaffen daaɗi yana shiga hancin ta wadda yayi sanadiyar ƙara murɗawar cikinta da babu komai ciki, sam be kula da mutum a wurin ba sbd rashin hasken parlorn Ƴan kwayayen lantarkin masu kyau dake kunne wutar su ba farare bane wasu kaman Orange kaman Red haka dae wutar ya bada wani colour me duhu duhu haske haske.

Tuntuɓe yaji yayi da kullin kaya chakk ya dakata a saninshi dae a nan kan hanyar babu abunda ze iya cin karo dashi, maida idanunshi yayi kan wurin se yaga kaman mutum a kwance a takure, da sauri ya miƙa hannunshi ya kunna fararen hasken wadda a take ya haske parlorn tarrr kaman rana oily eyes ɗin shi zube a kanta...
"Aysher" ya furta sunan yana duƙawa ganganta
"Ya Salaam"
Ya kara faÉ—a da deep husky voice nashi
"Me kike yi a nan? Don't tell me tunda kika shigo anan kike zaune?"

Hawaye kawai ta sake farawa bata iya ta amsa shi ba, haka kuma bata iya kallonshi ba hannunshi taji a goshinta da sauri ya janye yana sake ambaton Allah, Ranshi gabaÉ—aya yayi baki kirin, amma Naina bata da hankali yanzu amanar da ya É—auko kenan take wulakantawa tun daga yanzu a yau É—in nan?.

"Ni kam zan koma Nene ABBA"
Ta faÉ—a cikin karyayyiyar muryarta wadda ya saka shi lumshe idanunshi ya buÉ—e, tana reffering din shi da Abba ne sbd haka Baffansu ke kiranshi a gabansu, ko da Nene ze yi hirarshi ya kan ce Abban yaran nan kaza ko kin san me Abban yara yace? Haka dae so Zayyad da su kan haÉ—u haka yake kiranshi shiyasa itama ta kira da hakan.

Kallonta kawai yayi be bata amsa ba se ta kara sautin kukanta, dafe goshinshi yayi da tafin hannunshi ya ɗan murza kan ya miƙe tsaye yasa hannu ya dauki kullin kayanta, ɗayan hannunshi kuma ya sanya ya kama nata ya miƙar da ita sbd magana da baze iya yi ba, kaman rakumi da akala haka take binshi suka kutsa cikin gidan zuwa wani parlor se wasu kofofi da dining da aka rufe wurin da labulaye masu haske, komai royals ne anan kam golden da milk da suka haske parlorn, wani kofa daga farko ya buɗe suka shiga ciki, Brown set na Italian bed ne hade da wardrobe din shi da rabi madubi, dressing mirror da shoe rag, a tsakiyar ɗakin ya saki hannunta ya nufi wardrobe ya jefa kayanta ya dawo ya tsaya gabanta duk ya cika mata ido da faɗin kafaɗunshi, tsawon shi da idanun shi masu kaifi dake kanta, so yake yace taje tayi wanka kan ya nemo mata abinci da magani amma maganar na mishi matukar wahala.

Tsaki yaja ya juya ya nufi toilet seda ya buÉ—e kofa kan ya kalleta ya yafito ta da hannu, a hankali ta fara takowa har ta iso ya wuce ciki ta bishi, da kallo ta bi bayin lallai kam wannan wai makewayi? Ta ayyana a ranta Dukda zafin zazzabin da take ji baki galala take karewa bayin kallo
"Hey!".
Ya faÉ—a bayan ya É—auko bucket don ya san ba iya shiga jaccuzi zata yi ba, ba kuma iya anfani da shower zata yi ba,
"This..." Ya nuna blue
"ruwan sanyi ne, but if you turn to this.." Ya mayar Red
"ruwan zafi ne, ki haÉ—a kiyi taking shower i will be right back"

Daga haka ya fice, ta ƙarasa bakin tap ɗin ta mayar ruwan sanyi tare da sa hannunta se taji sanyi ƙalau, ta mayar jan se taga ruwan zafi na zuba har da turirin hayaƙi dariya ta saki ta ma mance tana jin zazzabi ta fara kalle kalle a fili ta furta
"ko daga ina ake dafa ruwan a sako shi a tiyon nan kuma?"
Bata da me bata amsa haka ta surka tayi wanka ta mayar da kayan da ta cire abunta ta fito a ƙasa ta zauna tana nazarin yadda zata yi sallah se gashi ya buɗe kofa ya shigo da sallama iyakarsa kan lips ɗin shi..

"Abba ina so nayi sallah ban san inda ake kallo ba"
Ta faÉ—a cikin harshen fulatanci, É—an kallon kayan sakin da ta sake mayarwa jikinta yayi ya É—auke kai, ba tare da yayi magana ba ya je wardrobe ya buÉ—e ya fiddo sallaya ya shimfida daga É—an gefen É—akin yana fuskantar gabas ya dawo inda ya ajiye ledojin da ya shigo dashi,
Chapter 3 · 0% Book details