← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shukoki ne masu kyau da tsari gabaÉ—aya wurin, kasanshi shimfide da carpet grass, yadda flowers dake wurin suka kawata wurin da kalolinsu kama daga ja, kore, dorawa se taji kaman ta fita daga Kasar ne gabaÉ—aya, takawa tayi kaÉ—an idanunta ya gane mata kwantaccen ruwa a cikin wani farin kwami me kalar sararin samaniya, daga gabanshi wani gado ne har guda biyu, gefe chan kuma kujeru ne masu taushi da tebur a tsakiyarshi.

Wurin yayi matukar burgeta ainun, shawagi tayi tayi a wurin tana kallon itacuwa da aka shuka suke fitar da Æ´aÆ´ayensu masu burgewa, guiva da yayi yellow kato ta tsinka ta wanke ta soma ci tana ta aikin murmushi, ta jima a wurin sossai don seda taji ana kiran azahar kan ta koma ciki don yin sallah.

Shi kuwa yana tashi daga dining É—akin Naina yayi, tana lumtse cikin wata lumtsatsiyar cushion nata na É—akin dake maroon hannunta rike da waya tana dannawa, Bakinta chewing gum ne tana taunawa a hankali, fusge wayar yayi ya wullar kan gadonta yana aika mata wani irin kallo yace
"Naina whats wrong with you? Menene ya hau kanki?"

Kallonshi take tana jin hawaye na cika idanunta ta miƙe tsaye ta nuna shi
"this... You, kaine ke damuna! Emran taya bazan tsani yarinyar nan ba ma for goodness sake? Akan yarinyar nan kuma a gabanta kake ta danganta ni da sunaye kala kala, harda mahaukaciya ka kirani, akan wannan kazama Æ´ar rugan.."

Idanunshi ya lumshe da karfi se ya buÉ—e a kanta yana shafa kwantaccen sajenshi kaman wadda ya rasa abun yi se ya taune lip din shi ya saki..

"Taya ba zan dangantaki da irin waenchan sunaye ba? Come back to ur right sense mana! I told u time without number in ba zaki iya taimakona a kanta ba ki fita harkarta, yarinyar nan bata miki komai ba kina aibatata son ranki ina guje miki randa zata iya ramawa bcs zuciya bata da kashi, that time zaki san cewa na gargade ki akan zub da girman ki, yarinya kuma bazata bar gidan nan ba se aure... Shine kaÉ—ai abunda ze fidda ta so pls take a chill pill"

Hawaye ta soma zubarwa wani na bin wani, cikin Muryar kuka tace
"Emran ka daena so na, did you hate me this much?"

Rikitattun idanunshi ya zuba mata, she knows baya son kuka, kukan ma daga macen da yake so sannan kuma shine silar zubar hawayen, amma Meyasa ta kasa fahimtar shi?

Ganin tana shirin kaiwa ƙasan tiles da kukan da ya kwace mata yasa yayi hanzarin janyota jikinsa, kuka take tayi kaman an mata wani abun a zo a gani.

"Please stop it Naina, ki daena bana so"

"abunda kake so kenan Emran, kana dae sane da cewa bani da wani farin ciki a cikin zuri'arka se naka, yanzu kaima ka fara tsanata ko don ban haihu bane? Ko sbd ban haihu bane yasa bani da power a gidana?"

Ajiyar zuciya me karfi ya sauke, hakane ya rasa me yasa family dinshi basa son ta ba kuma sa janta a jiki, amma shi kam yana son kayarshi kuma ai ya san haihuwa na Allah ne tunda dukkansu lafiyansu ƙalau.

"Ban tsaneki ba Naina, ba zan iya tsanarki ba ke fa sirrina ce taya zan fara tsanar sirrina huhnn?"

Haka ya lalace a rarrashinta sede duk yadda ta fito mishi inde kan maganar Aysher ne ze kauce sbd babu dalilin da ze sa ya biye mata ya butulcewa abokinshi tun na yaranta, bata huce ba seda ya amince zasu tafi New York a mata IVF, zasu gwada sa'arsu akan hakan kuma su gani.

Fitowa yayi daga ɗakinta bayan ya tura ta bayi tayi wanka, alwala yayi sbd azahar da ake ta kira ya fice, bayan ya dawo ɗakinshi ya wuce sbd baya jin fita a lokacin har ya kwanta ya lumshe ido se ya tuna ƙunan da tayi dazu, Miƙewa yayi ya duba ointment ya fito ya mata knocking, jin shiru yasa ya tura bata ciki, ya duba kitchen bata nan, fitowa yayi ya fara dube dube a tsakar gidan nan ma bata nan, kuma ya san ba iya fita zata yi ba, garden ya nufa tun daga nesa ya hango ta a kujerar dake bakin ruwan riƙe da alqur'ani tana karantawa cikin sanyin murya da natsuwa.

Ajiyar zuciya ya sauke kan ya nufeta ko sau É—aya be É—auke idanu daga kallonta ba, tana sanye da doguwar riga sky blue and White se É—an baby hijab shima sky blue ya mata kyau sossai barin ma da garin yayi lublub alamar hadari hadari.

Karatunta take a natse idan tayi tayi se ta rufe qur'ani tayi da kai, ta sake komawa farko ta haÉ—a, tana cikin bitarta se haddar ya gudu mata, shiru tayi tana son tunawa se ta É—auko se ta chanza ayar zuwa wani chan daban, a hankali taji sautin shi yana É—aga mata, waiwayowa tayi se suka haÉ—a idanu, karamin murmushi tayi kan tace
"Na gode"

Be ce komai ba ya zauna a ɗaya kujerar dake facing nata, se ta gyara zamanta tana maida dukkan kafafunta dake maƙale a saman kujeran ƙasa.

Ganin tayi shiru yasa yace
"ƙarasa haddarki"

Cigaba da karatun tayi shi kuwa yana dannar waya, idan tayi ɓata kuma ze gyara mata har ta kamallah.

"Muga hannun?"
Yayi magana kaman me tambayarta.

Qur'anin ta ajiye akan cinyarta ta wara hannunta cikin rashin fahimtar shi, shi kuwa ointment ɗin ya buɗe ya ɗan matse a hannunshi na dama ya ajiye se ya miƙa mata tafin hannunshi na hagu.

Zara zaran yatsunshi dake ɗauke da zoben azurfa me kyalli ta kalla, kan cikin ɗan faɗuwar gaba da ya risketa ta ɗaura tafin hannunta na dama bisa tattausan tafin hannun nasa, a tare suka lumshe idanu suka buɗe, yatsunta ya zubawa idanu yayinda ita kuwa idanunta ke bisa kwantaccen sajenshi da ya matukar ƙawata fuskarshi ya mugun amsarshi.

A hankali ya shafa mata ointment ɗin bisa ɗan ƙunar kan ya saki hannun ya ja da baya, daidai lokacin aka kira la'asar, dukkansu Miƙewa suka yi sede ita taja ta tsaya shi kuma ya fice daga wurin..

Bayan tayi sallah ta chanza hijab zuwa dogo kan ta fito zuwa ɗan hut ɗin da suke karatu ciki, a shimfide yake da tattausar darduma da tuntu irin na gidan sarauta, daidai malamin ya shigo ta zauna ta bashi hadda ya kara mata, suka yi hadith da take kan ya mata sallama ya tafi, ɗaki ta koma tana tunanin abunda zata girka musu da dare don matar gidan kam taga fitan ta tun suna karatu cikin wani rantsatsen paper lace da aka mata dinkin doguwar riga, karamin gyale a kafaɗarta se gashinta da ta zubo shi har baya wadda na ƙari ne.

Tunawa da taga bishiyar zogale a garden din yasa ta maida karamin hijab ɗin ta tayi waje, cirowa tayi Allah ma ya sa bashi da tsawo da se ta nemi abin cirewar, kitchen ta dawo ta dibi shinkafa ta ɓarza ta wanke ta ciro dankwalelen kaza daga frigde, a tsanake ta haɗa dambunta me rai Allah ma ya sa ta iya anfani da steamer sbd dakkere da suka yi a ciki ranar da Asma'u, a hankali kamshin ke ratsa kitchen ɗin, bayan ta gama ta zuba a foodflask se ta fara yiwa kazar nan haɗin gashi irin na tukunya wadda ba'a raba asalin Fulani dashi idan har a ruga yake, sam bata wani san anfani da oven ba don haka a tukunyar ƙasa tayi gashinta dake ta zuba kamshi ta saka a kula daban, tattare kitchen ɗin tayi ta wanke abubuwan da ta ɓata kan ta kai abincin dining area.

Komawa ɗaki tayi ta gabatar da Magrib da aka kira, karatunta ta ɗan yi bita har aka kira Isha tayi sallah da azkar kan ta fito don ɗiban abinci, har tayi serving kanta ta zauna a dining ɗin se gashi nan ya shigo parlorn bakinshi ɗauke da sallama iyaka lips ɗin shi, bayanshi Naina ce riƙe da leda me tambarin gidan abinci.

Dukkansu Dining É—in suka kalla sbd motsi da tayi na kokarin tashi ta koma É—aki don gujewa haddasa rikici a tsakaninsu, plate É—in hannunta ya É—an kalla kan ya kalli dining É—in, Naina tayi saurin cewa
"Kaga na biya Fav restuarant É—inka na samar maka favorite food naka gwara ka ci tun da zafin shi"

A hankali yace
"I think am not eating that.."

"Toh me zaka ci? Da safe ma fa wani jagwalgwalo kaci"

Murmushi yayi yace
"ke kika ɗauke shi haka Babe, but trust me yana riƙe ciki sossai ba abunda ya kai abincin gargajiya gamsarwa".

Daga haka ya isa dining É—in ya buÉ—e flaskes É—in don tuni ta tsufa a É—akinta bayan tace musu sannu da dawowa.

Har mamakin yadda yarinyar nan ta iya girki yake, ze iya cewa kusan sabon abu ne a wurinshi kuma ba sabo ba tunda ba yau ya fara zuwa ruga ba yana kallo ana aurar da yara a 12/13yrs kuma su yi girki na ban mamaki kai ko mahaifiyarta ze iya tuna a sadda Isma'il ya aure ta bata wuce 14 ba ake ta cewa ma ta tsufa a gidansu idan tayi girki duk yaje ya dinga yabon girkin kenan.

Naina da ta biyo shi ta zauna ta fidda abincinta daga leda ta fara ci, shi kam zuba dambun yayi da kazan dayawa ya zauna ya ci sossai, shi ze iya cewa zuwan Aysher ai albarka ne a gareshi, idan yaci irin wannan dama se a gidansu to gidansun ba kullum yake samun zuwa ba sbd aiki da kan mishi yawa.

Har suka gama Naina kam bata daena aikawa abincin shi Harara ba, shi kam yayi nak yayi hamdala kan suka wuce dakunansu, wanka yayi ya shirya kwanciya ya kwanta, be damu da duba Naina ba don ya san idan tana da wani bukata zata zo ko kuma shi idan yana bukatarta ya je amma ba kwana suke É—aki guda ba.
Chapter 13 · 0% Book details