← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman ze kira Nainan se ya tuna yadda tayi biris dashi da safe akan Aysher, ya rasa me ke damunta wannan dae kam kai tsaye za'a ce rashin tausayi da imani, me Aysher tayi mata da zafi da hatta ciwo ma ba za'a É—aga mai kafa ba?

Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga muryarta da alama tayi kuka ta gaishe shi
"Me ya faru?"
Ya tambaya.
"Babu, Yaya ya jikin Aysher din? Is It serious?"

Muryanta yayi sanyi dayawa kaman ba Asma'u ba, ba don ya yarda da babu komai ba kai ko kiranshi da yaya da tayi ya nuna akwai damuwa yace
"taji sauƙi...."

Ɗayan hannunshi cikin aljihu ya nufi gaban kujeran da take ya tsaya yana kallonta ya ƙara da cewa
"bacci ma take"
Ajiyar zuciyar da har seda yaji ta sauke kan tace
"Allah ya bata lafiya"
Daga haka suka yanke wayan.

Kan ya sauke hannunshi kiran Naufal ya shigo dagawa yayi kan yayi magana Naufal ya fara jero mishi tambayoyi

"babban yaya ya jikin Preetty? Maami ke ce min bata ji daaÉ—i ba naje gidan ma ban samu kowa ba, is it serious? An bata gado ne? In zo asibitin ne?

Idanunshi da ya lumshe ya ware yana É—an murmushi yace
"taji sauƙi, we are heading home now"
"Toh zan jiraku Yaya"
Daga haka ya sauke wayan, wayan ya ɗan bi da kallo na seconds kaman wayan ya zama baƙon shi kan ya kalleta.

"Aysher"
Ya kira sunan yana É—an bubbuga jikin kujerar, da alama tana da nauyin bacci. Seda ya kira sau uku kan ta farka, da sauri ta zauna tana gyara rigan jikinta, uncomfortable take jinta barin ma da ta zauna kasancewar ta jima a kwance tana jin yadda jini ke fita mata se taji gabaÉ—aya ta takure.

"muje gida"
Yana kai nan ya koma ya tattari abunda ze tattara kan ya nufi kofa tana tsaye rike da ledar ta ya buɗe ta bi bayanshi suka fice,  bata ga ya sawa kofan kwado ko key ba hakan yasa tayi ta juyawa tana kallon kofan kar dae mancewa yayi, gyara gyalen ta tayi tana kallo ya danna wani abu kaman kofa suka tsaya gaban abun tana daga bayanshi na mintuna kan abun ya dare biyu, shi ya shiga tabi bayanshi cikin tsoron da ya kama ta ta fara kalle kallen cikin elevator ɗin.

Danna wani arrow da ya nuna ƙasa taga yayi, se taga abu ya rufu ya fara motsi da sauri ta rufe idanunta jin jiri na kwasarta baya tayi ta sake dawowa gaba se goshinta ya bugi bayanshi, karamin ƙara ta saki shi kuma yayi hanzarin Juyowa yana riƙe hannunta ganin tayi baya a tsorace zata faɗi.

"Yi haƙuri jiri nake gani"
Ta faÉ—a cikin diriricewa sbd idanu da ya É—an tsura mata.

Hannunta da be saki ba ya É—aura akan wani handle dake gefe da gefe alama na rikewa ne se ta damke ta sake runtse ido jin da gaske jiri take ji.

Har ya tsaya be daena observing É—inta da ido ba, kofan na buÉ—uwa yace
"muje"
Se ta buÉ—e ido ta shiga gaba ganin ya bata hanya, kaman zata kife take tafiya, ga jiri ga kunya sbd gani take kaman kowa ita yake kallo.

Seda yaga zata bi wani hanya kan ya shiga gabanta a tare suka fito ma'aikatan na ta mishi se da safe, motan shi da ya É—aga a sadda ta fita yaje mall ya sama mata kaya da abinci ya nufa parking lot da nashi ne na musamman ya buÉ—e ya shiga, tana É—an kallon kayatuwar harabar asibitin itama ta buÉ—e gaba ta shiga, a hankali ya ja suka fice daga asibitin se a lokacin ta tuna kayan baccinta dake shanye a office nashi kuma harda inner wear dinta da ta cire, runtse idanunta tayi gashi ba halin ta ce su koma kuma bata da zarrar da zata iya ce mishi gobe ya kawo mata, ina ma ta isa? Amma kuma ya ze yi gobe idan ya je ya gani..

Da wannan sake sake suka isa gida, ita ta soma shiga parlorn se taga Naufal da Naina suna zaune suna kallon Tv lokaci lokaci suna É—an hira, dama shi mutumin ta ne ta kan sake mishi su yi hira.

"boɗɗi..! Noi a ɓeɗɗi matugo?" (Ya kika kara ji da jiki?)
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye ba tare da ya amsa sallamar da tayi ba.

"Alhamdulillah wodi dama(da sauƙi)
Ina yini?"
Ta haɗa gabaɗaya sbd ta samu ta wuce ganin Naina da irin kallon da take mata na sama da ƙasa.

"Zauna mana!"
Ya faɗa, a ɗan darare ta zauna a ƙasa tana kau da idanunta daga deadly look da Naina ke mata..

Wani irin abu ne ya tsayawa Naina a wuya yanzu wannan yarinya har she's worth of wearing thomb Brown? Sabon desinge ma da ko ita ta saya ne bata saka ba amma wannan ƴar kauyen ta riga ta sakawa, yanzu ma wai tare suke da mijinta tun safe? Tsaki me karfi taja ganin yadda duk Naufal ya ruɗe a kanta, ga Emran ma da ya shigo se ya samu wuri ya zauna, Miƙewa tayi ta bar parlorn ba tare da ta ko kula gaisuwar da Ayshern ke mata ba.

Naufal ne ya gaida yayan nasu ya amsa mishi yana tambayar su Ammi sbd be shiga ba yau, amsa mishi yayi da suna lafiya suna yiwa Aysher ma sannu da jiki.

Miƙewa yayi yace bari yayi wanka ya shige.

Kaɗan kaɗan take amsa mishi sbd zama da tayi da dare tayi nazari akan chanzawar Asma'u a jiya, ta fara tsoron abunda Naufal ze iya cewa sbd kowa ya zauna da Asma'u ko bata fita fili ta faɗa ba zaka san akwai soyayyar Naufal a ranta gashi shi kuma inda ya dosa daban, sam bazata so ya lalata kyakyawar alaƙarsu ba sbd da ita ne kawai take zama taji daaɗi duk garin na Abuja da ta tsinci kanta ciki babu zato bare tsammani.

Ganin yadda take amsa mishi ne yasa yace
"ko har yanzu jikin ne?"

Kai ta gyaÉ—a tace
"Ina so ne in É—an kwanta"

"Toh Allah ya qara sauƙi, zan shigo gobe in duba ki"

Girgiza kai tayi
"Ai gobe zan je school ne"

"har zaki iya zuwa school? Ki huta mana samu ki ƙara samun karfin jikin?"

Nan ma girgiza kai tayi
"Ai da sauƙi in shaa Allah zan iya zuwa"

"to shikenan ko zuwa dare zan shigo, me zan kawo miki? Baki bukatar komai?"

Girgiza kai tayi ba tare da tayi magana ba
"sai gobe É—in"
Tana kai nan ta nufi É—akinta, da kallo ya bita har ta shige, yarinyar is just a damsel ya ayyana yana murmushi a bayyane.

Har aka kira la'asar kan Emran ya fito sanye da kananun kaya da alamun yayi wanka ya chanza a tare suka fice masallaci da Naufal, bayan sun dawo be shiga ba ya tafi shi kuma ya dauki mota yaje nema musu abunda zasu ci, har se bayan Magrib ya shigo don ya ratsa wurin friend É—in shi Sufyan sbd kwana biyu sede suyi waya sam basu samu time na juna ba.

Kai tsaye knock ya mata don ya bata nata ya kuma duba jikinta, buɗewa tayi har lokacin rigan ne jikinta ta gaishe shi ya tambaye ta jiki ta amsa a kunyace, diary milk dake hannunta ya bi da kallo a sadda take karɓan abincin, kaman baze yi magana ba chan ƙasa ƙasa sbd gajiya da yake ji yayi ga kasala dake rufe dashi tun safiyar yace
"Hey in ba so kike duk wata duniya su san kina period ba to ki rage shan wannan zaƙin"
Ya karashe yana nuna choculate É—in ta idanu...

Ina ƙasa ya buɗe ta shiga..kasa ta sunne kanta be jira amsarta ba ya juya ya tafi gab ze shiga ɗakin Naina ya ɗan saki murmushi da shi kaɗai ya san dalilin abunshi kan ya buɗe kofan ya shiga.

Tana kwance a kan gadonta hannunta na É—aure a kan goshinta jin motsin shi be sa ta É—aga kai ta kalleshi ba
"Babe"
Ya faɗa chan ƙasa
A hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi, yana zama gefen ta ya riƙe hannunta yana ɗan shafa bayan a hankali yace
"whats ur problem?"

"Ka daena ɓata bakinka wurin tambayata kaima ka san matsalolina biyu ne daga na wannan shegiyar yarinyar se na haihuwa"

Idanunshi ya lumshe ya sake buÉ—ewa
"Meyasa? Meyasa burin ki ko yaushe ki ɓata min rai Naina? Sau nawa zan gayamiki muhimmancin Isma'il a wurina ne? Why zaki sheganta mishi ƴar da ya haifa ta hanyar aure da sunna?"

Ganin Ranshi ya ɓaci ne yasa ta miƙe zaune se ta takwashe kafa ta kife kanta a kirjin shi
"Am sorry... Ka sanni ban iya ɓoye so ko ƙi ba Emran ban san Meyasa a ko yaushe na kalleta se in ji kaman zan mutu ba"

Sbd sanin yana da bukatarta ne kawai ya sa ya soma shafa bayanta
"hakan babu kyau, bata miki komai ba fa hasali ma tsoron ki take ji ki daure ko ba zaki so ta ba karki ƙi ta, and ban ji daaɗin abunda kika yi ba yau ciwo ai ya wuce gaban wasa kuma kema baki fi karfi Allah ya jarabceki da ciwo ba kina tunanin ita zata iya ganinki ta kyale ki ne? She's just a little girl with a pure heart pls Naina drop all ur dramas i beg u"

Shiru tayi bata iya ta ce mishi komai ba, abincin da ya kawo musu ya sakata É—auko plates da sauransu suka ci a É—akin nata, tana É—an mishi hirar success din ta a company É—in su da kuma business trip da take son zuwa chan Thailand, se a sannan ya faÉ—a mata tafiyar su ma ya gama komai its next week monday, sossai tayi farin ciki kila bazata dawo ba se da ciki.
Chapter 18 · 0% Book details