← Book details Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Rubutu A Kan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ze koma Naina tace
"Kayi mantuwa ne?"

Girgiza kai yayi ba tare da ya tsaya ba hakan yasa ta bishi, daga parlor ta tsaya tana kallonshi har ya tura kofar Aysher ya shiga bayan knocking da yayi har sau uku...

"Ya ilahil Alameen" ya faɗa kasa ƙasa yana nufan gadon da hanzari ganin tiny body ɗin ta dunkule a wuri guda, sanye take da dogon wandon bacci peach da rigar shi, baka iya ganin fuskanta sbd gashinta da ya hautsine ya baje gabaɗaya a kan fuskan gashi kuma a kife take kwance, daga kallon yadda ta kwanta ɗin da kuma yadda gabaɗaya gadon ya cukwuikuye da alama ba lafiya ba.

"Aysher! Aysher!! Ke Aisha!!!"
Ya jera kiran yana buga pillown da take kai sede bata iya ta amsa ba amma ta É—an yi motsi alamar tana jinshi, komawa yayi da sauri parlor yana kallon Naina da idanunshin nan yace
"I think yarinyar bata da lafiya please help me ki tayata kimtsawa mu tafi hospital"

Kallonshi take kawai galala kan tace
"am already late ina da meeting da board, bye"
Tana kai nan ta juya ta fice.

Lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan ya juya ya koma ɗakin hannunshi ya haɗe yana kallonta yana sauke numfashi a hankali hankali, ledojin choculates na diary milk da snacks kusan biyar a zube a gaban gadon, iska ya fesar daga bakinshi kan ya sa hannu ya lalabo wayan shi, kai Tsaye Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga ta gaishe shi cikin girmamawa

"Ki zo mana in baki da class, i need u to help Aysher bata da lafiya"

Tsurawa gaban dressing mirror da take zaune kai idanu tayi kan ta waiga ta kalli É—akin nata ajiyar zuciya ta sauke kan tace
"Yaya ina school yanzu zan shiga practical kuma a matsayin C.A yake"
Katse kiran kawai yayi ba tare da ya ce komai ba ya sake tsura mata idanu....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuÉ—i ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faÉ—akantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰

                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 10

A hankali ya isa gaban gadon ya tsuguna, hannunshi na dama yayi dropping bisa wuyanta, É—ayan hannun kuma kafaÉ—arta ya birkitota, hannun dake kafaÉ—an ya cire ya soma maida gashin kanta baya..

"Ya Salaam" ya faÉ—a cikin damuwa da alama cikin ciwon nan ta kwana ganin yadda gabaÉ—aya idanunta suka kumbure tsabar kuka kuma har yanzu hawaye take yi, dama Aysher bata iya ciwo ba se ta gigice ta gigita iyayenta da kuka da raki.

"Aysher!"
Ya kira sunan chan ƙasan makoshi, kokarin buɗe idanun take sede har lokacin hawaye ke zuba, bata ma iya kallonshi sbd idanun babu madubi.
"Me ya faru? Menene matsalar?"
Yayi maganan cikin tsantsar tausayi.

Lip É—in ta da yayi ja sharrr ta taune tana sake lankwashewa, hannunta É—aya dake marar ta ya bi da ido.
"Cikin ki ke ciwo?"
Kai ta gyaÉ—a tana sake fashewa da kuka tana kuma yarfa É—ayan hannunta.

"Me kika ci? Daena kukan nan and talk, me ya janyo ciwon?"
Cikin Muryar kuka tace
"ban sani baa Abbaa"

Sake kallon marar yayi da lokacin ta janye rigar ta É—aura tafin hannunta bisa marar tana murzawa cikin kuka, kallon fuskanta yayi a matsayin shi na likita kai tsaye ya hasaso abunda ke damunta

"period pain? Dama yana miki ne?"
Sam bata gane me yake nufi ba ta saukar da wuyanta daga tafin hannunshi ta sake kifewa, girgiza kai tayi ita kaÉ—ai ta san me take ji.

Sake juyo ta yayi
"Ki natsu mana ban son rashin hankali, keep quite and tell me dama kina ciwon mara ne yayin al'ada?"

Cikin kuka da É—an tsoro sbd da É—an tsawa haÉ—e da damuwa yayi mata maganan tace
"Ni ban sani ba, ban taɓa yi ba"

Wara idanu yayi
"baki taɓa period ba? Shekarun ki nawa?"

Numfashi taja tana yarfa hannu cikin sakin sabon kuka tace
"wayyoo baffana wayyooo Nene zan mutu, wlh mutuwa zan yi..."

Ganin gabaɗaya ta gama ficewa hayyacinta yasa ya sanya hannu ya sure ta kawai suka fito, drivernta ne ya buɗe mishi mota ya sanya ta, ya bashi umarnin tafiya kawai se gobe in taji sauƙi, da hanzari ya shiga driver seat ya ja motar suka fice.

Har gaban tamfatsetsen building na asibitin nashi da aka rubuta CITY CLINIC a chan tsolon ginin dake nan kaman skyscrapper yayi parking, da gudu security dake tsaye daga bakin enterance ɗin ya je ya buɗe mishi kofa, fitowa yayi ya buɗe bayan ya sake daukar ta ya nufi ciki se bashi hanya ake ana miƙa gaisuwa sede be kula kowa ba.

Katon floor ne dake malale da farin tile daga ka shigo enterance ɗin, chan daga gefe reception ne amma yayi nisa sossai, matattakalai har biyu ne daga nan ƙasa kana iya hangar saman sbd glass ne da shima kaman floor ne, in ka miƙa daga ƙasan akwai elevator wadda kaman har guda biyu ne daban daban, majinyata dake sanye da kayan asibitin ke ɗan kai kawo da en uwansu.

"Sir in kawo wheelchair?"
Nurse ɗin da ta iso da gudu ta faɗa, girgiza kai kawai yayi ta bishi da sauri ganin yayi elevator alhali emergency ɗin su na daga ɓangaren hagu a First floor ɗin, ita ta danna mishi ya shiga tana shakka shakka sanin halin shi ta tambaye shi wani floor?
"8"
Abunda ya faɗa kenan yana ɗan kallon fuskan Aysher dake kife a kirjin shi jikinta gabaɗaya a sake, likitoci uku ne suka shigo suma da sauri kan ya rufu, kowa so yake ya samu privilagde ɗin ogan nasu sbd mutum ne shi me kirki da sanin ya kamata, ma'aikatan shi suna matukar mutuntashi sbd shima yadda yake mutuntasu, abunda ze sa Kaga ya ɗauki tsatsauran mataki akan ma'aikaci to ba ƙarami bane, kawai dae baya son wasa da aiki in kana so ku shirya ka kasance ka san makamar aikin ka, mata kan mishi kallon marar mutunci da wulakanci sbd yadda baya basu fuskan kawo mishi wargi inda Allah ya tsare shi ma kwarjininshi baya bari mace ta fuskanceshi da wani banzan zance, ko kinyi kokarin yi yana tsura miki mayun idanunshin nan zaki rikice ki rasa abin faɗa a dole suka shafa mishi lafiya.

"Someone should call Dr Hafsa ta sameni a office na now please"
Ya faÉ—a yana kallon likitocin, a tare suka fiddo waya sede É—aya ne ya samu ya kira ta.

"Oga needs you in his office now! Its an emergency"
Yana kai nan ya sauke daidai elevatorn ya buɗe kai tsaye ya miƙa doguwar floor ɗin.

"Zaku iya komawa aikinku"
Da sauri ya wuce ya shiga katuwar office nashi me ɗauke da wasu irin office furniture na garari, misalta tsaruwa da fasalin office ɗin ɓata lokaci ne, gabaɗaya asibitin kaman a Turai ba Nijeriya ba, a kan gado dake cikin office ɗin ya shimfideta se murkususu take yi tana kuka a hankali.

Dr Hafsa da kwararriyar gynae ce ta danna door Bell yaje ya buɗe, ta shigo tana miƙa gaisuwa ya nuna mata gadon
"My daughter.. I think she's having cramps matsalar inaga this is her First period gashi ta ja shekaru"

Dr Hafsa da bata yi mamaki ba sbd ana samun irin cases ɗin wata se ta kusa twenty years ma bata fara ba, wasu kuma daga shekara goma kai har me shekara tara ma ita ta taɓa karo da ita a harkarta na gynae, isa gadon tayi ta yaye rigar na Aysher da sauri ya ɗauke kanshi ya koma kujeran shi ya zauna don ya barta tayi aikinta.

Bayan gama observing tace mishi tana zuwa, pharmacy ta wuce ta karbo allurai ta dawo, shi kam yana zaune yana ɗan aiki Dukda ya tsinci kanshi da yawan kallonta kaɗan kaɗan se ya ɗaga idanu ya kalleta, Dr Hafsa na zuwa ta haɗa injections ɗin tayi mata har lokacin jinin be sauƙa ba kawai masifar ciwon marar ne ya hautsina ta..

Seda kuwa ya taso ya taya Dr Hafsa kan aka yi allurar se hawaye take yi.

"Sir da alama this ur daughter sangartacciya ce, ji yadda take ta raki akan M.p da yanzu ta fara shi? Hmm akwai aiki kenan every month!"

Yana kallon fuskan Ayshern ya É—an yi murmushi kaÉ—an
"she's in pain ne ba raki bane, now komai ze daidaita kenan?"

Tana É—aura mata drip tace
"Yeah, in shaa Allah daga ruwan nan ya kare ina ga komai ze yi daidai dole ne ta samu irin wannan cramps sbd rashin farawa da wuri, ze iya yiwuwa ta samu wani watan ze iya kuma yiwuwa cramps ɗin na farko ne kawai, amma please ta rage shan zaƙi sbd gudun irin wannan wahala"

Kai ya gyaɗa a ƙasa ƙasa yace
"thanks"

Juyawa tayi ta fice tana mamakin ganin yadda duk ya damu, se kuma tana mamakin ta yadda Wannan É—in ta zama Æ´ar shi, gyaÉ—a kai tayi
"ze iya yiwuwa don prof ba karamin yaro bane kawai jikinshi ne Allah ya halliceshi me kyau, sannan ma family ɗin shi da abunda ya shafe shi to him are confidential don baya taɓa magana akan family, ko matarshi bana tunanin akwai wadda ya santa"

Ta ida maganar tana zama a kujeranta.
"Amma fa yarinyar tashi kyakyawa ce shi ta biyo ga dukkan alama"

Ni dae nace aiki ya sameki Dr Hafsa.
Chapter 16 · 0% Book details