← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce, "A na kan shirin tafiya kenan, zai yiwu ma cikin satin nan don na ce ma su Dad bana son in fara labour kafin a kai ni"Ya ce, "Aiki ki ke so a yi miki?"

"'Ni na fi son aiki in samu baby ba tare da na wahala ba Shatima ya ce,

"To Allah sauke ki lafiya Ta ce,

"Amin Ya ce,

"To ya za a yi da kayan gadon can na
waje?"Ta ce,

"Ni na san ya za a yi da shine? In akwai gurin da za ka ajiye ta ka ajiye kawai"

Ya ce,

"In ba dakin Salma zan kai ba, ba ni da gurin da zan aje"

Ta ce,

"Ni fa ba abin da zan yi da shi"

Salma tana juye shinkafa a kula don ranar mai

da yaji take son ci, sai ta ga maigadi da Shatima suna shigo da kayan gado. Ba ta ce komai ba, suka shiga da su dayan dakin suka jujjingine har da sif. Ta yi musu
sannu, Baba maigadi ne kawai ya amsa. Yana fita

Shatima ya kalle ta, "Kayan Amna ne kada ki Bannata musu"

Salma ba ta iya amsa masa ba, domin dai ta san
duk cikinsu babu wacce za ta yarda a kai mata ajiyar kayan kishiya. Wata zuciyar ta ce Ki ka sani ko don ba ki da kaya a dakin ne, da kina da shi ba zai zo ya cire naki ya sa ba

Sai ta amince da hakan, kuma ta ji ta sauke haushin da ta ji. Wannan shine ya sa kullum Salma take da kyakkyawar zuciya, don tana da kyautata wa kowa zato.

Duk da Shatima ya yi iya kokarinshi don kada

Amna ta fita wata Kasa da sunan haihuwa sai dai hakan

ya ci tura don ya yi kokarin kai ta asibiti dan ya hada baki da likitan ya kara a kan lokacin da ake tsammanin haihuwarta. Sun je an samu nasarar yin hoton, kuma an Kara kamar yanda aka sa. Nufinshi kafin su yi shirin tafiya ta haihu.

Amma sai dabarar tashi ta tada musu da hankali, har ma ta sa suka soma haramar tafiyar. Amna ce ta yi mugun daga hankalinta tunda ta ga takardar hoton, kusan wata daya da kwanaki ya Karu a kan dukkan hotunanta na baya. Cikin damuwa ta kira mahaitinta ta sanar da shi, ya ce lallai ta shirya su tafi a
cikin satin nan maimakon na sama.

Dole Shatima ya sa ido suka aiko aka dauke ta suka tafi. Abin da bai sani ba ma iyayenta suna shake da shi, domin nasu ganin ya kamata ya dauki uzuri gurin aikinshi su tafi tare. Amna ce ta ke nuna musu cewa, aikin babu damar hakan. Ya shiga mugun tashin

hankali da damuwa. Aliya ce ta rungume shi tana lallashi tare da ba shi magana. Hakan ya sa shi son kasancewa tare da ita a 'yan kwanakin nan.

Sati uku da tafiyar su Amna aka ciro santalelen yaro mai kyau kama da ubansa, mahaifin Amna da kanshi ya kira Shatima yana masa albishir da samun karuwar. Murna sosai Shatima ya yi tare da kiran nasa

mahaifan ya sanar musu. Nan da nan labarin haihuwar ya watsu a dangi. Hajiya aka shiga shirya kayan barka.

Shatima yana kwance a kan katifarsa ranar dakin Salma yake. Kwanaki uku kenan da haihuwar,

amma maijegon ta ki daga layinsa. Ya san tana fushi ne tunda suka tafi sau daya ya kira ta, shi ma Aliya ta matsa masa. Ya tura mata sako yana mai rokon alfarmarta cewa ta daga, sannan ya sake kira. Ta dauki

wayar ta yi shiru duk da tana jin sallamar da yake dokawa.

Ya ce, "Ki yi hakuri Honey, ko mene ne tunda mun zama iyaye bai kamata muna fushi ba. Zafin rabuwa da ke har kuka na yi, shi ya sa bana kiranki"Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ka nuna min
matsayina, kuma na gani. Sai dai kullum in tayi

Momy karyar mun yi waya kana gaida su, don kawai

kada mutuncinka ya zube amma ba ka gani"

Nan Ya yi lallashinta, da kyar ta sauko sun yi waya sosai, kuma za su dawo cikin satin da za a shiga.Ya ce, "Suna fa?"

Ta ce, "Sai satin sama"

Ya ce,A nan za a yi mishi huduba?"

Ta ce, "Dad zai masa dama ya ce mu yi maganar sunan da za a sa mishi da kai"

Don ya sake faranta mata, ya ce, "Na ba ki zabi zumata

Ta ce,Kamanninka da yaron ya sa na darsa sunanka a zuciyata, in ni zan zaba ina son a sa mishi

Muhammad Ja'atar"Ya ce,

"Yanda ki ke so haka za a yi, amma nasa za a yi taron rada suna a gidanmu can Zaria, bikin mata sai kun dawo"

Ta ce Haka ya yi"

Ya Ce.

"To a turo min hoton yaron nawa in ganshi"Ta yi dariya,

"Ka ci sa'a da na ce sai randa

鈥� muka dawo ka ganshi".

Ya ce, "Da ma ni mai sa'a ne tun daga lokacin da na mallaki zuciyarki

Ta sake sakin dariyar jin dadi sannan ta ce,

"Zan turo maka yanzu ta whatsapp"

Ya kalli yaron cike da so tsantsa da kauna, fari ne tas cikin kayan jarirai masu kalar sararin samaniya.

Tabbas yaron yana kama da shi sosai. Ya mike ya dauki jallabiyarsa ya zura.

Salma tana zaune tana assignment ta dago ta dube shi, shi ma ya kalle ta tamkar zai yi magana amma sai ya fasa. Ta maida kai ta ci gaba da rubutunta
domin inda sabo ta saba da yanda Shatima ya rikide

yanzun. Ta kula kwanakin nan yana cikin farin ciki da walwala.

Dakin Aliya ya shiga ya nuna mata hoton kyakkyawan yaronsu. Ta yi farin ciki tare da fadin,

"Yaron nan kama yake da kai sak!"

Page 13

MUN TSAYA

Tabbas yaron yana kama da shi sosai. Ya mike ya dauki jallabiyarsa ya zura.

Salma tana zaune tana assignment ta dago ta dube shi, shi ma ya kalle ta tamkar zai yi magana amma sai ya fasa. Ta maida kai ta ci gaba da rubutunta
domin inda sabo ta saba da yanda Shatima ya rikide yanzun. Ta kula kwanakin nan yana cikin farin ciki da walwala.

Dakin Aliya ya shiga ya nuna mata hoton kyakkyawan yaronsu. Ta yi farin ciki tare da fadin,

"Yaron nan kama yake da kai sak!"

Ya rungume ta tare da fadin, "HaKika kin san kama

Y谩 mike,

"Bari in gwada wa Nafisa, Aliya ta yi 'yar dariya tana sake bin hotunan da kallo. Ya fita ya barta nan tsoron zuciyarta cike da
takaici. Tunda aka yi haihuwar ta lura Shatima ya zama kamar wani soko.

Natisa kuwa da ta kalli hoton cewa ta yi, yaron mai kyau abinshi. TA shafa cikinta tare da fadin, "Ni ma

Allah ya sauke ni lafiya"Ya dora tafin hannunshi a kan nata,

"Ameen

Sweetyna. Amma da wa ki ka ga yaron yana kama?"Ta dan yatsina fuska,

"Da mamansa mana"

Ya ce,Kin duba da kyau?"Ta yi zooming din hoton,

"Ga hancin nan irin na Mamanshi"

Ya san kishin Nafisa don haka sai ya ce,

"Ni nafi ganin kamarshi da ke"

Ta kalle shi,

"Da ni kuma?"Ya ce,

"Eh mana kin san da ni ki ke kama"

Ta yi murmushi,Wai da gaske ina kama da kai?禄

Ya ce,

"Sosai ma, in na cikinki ya fito kin ga
shi ke nan mun samu

"yan biyu, don na san da mu zaiyi kama"Ta sake kallon hoton,

"Guda daya ta tura maka?"

Yace

"Suna da yawa, bude ki gansu"

Tana kallon hotunan tana fadin,

"Ka tura min hotunan a wayana

Ya ce,To kin kirata kin mata barka?"

Ta ce, Ba ni da lambarta, kira min ita da kanka Nafisa da Amna sun gaisa, inda Amna ta yi wa

Nafisa fatan sauka lafiya, bayan ta yi mata barka. Ran Shatima ya yidadi, domin kullum yana addu'a Allah ya hada kan iyalansa.

Salma ba ta san da batun haihuwar ba, sai da taga Shatima da Aliya za su je Zaria wai za tayi wa su Hajiya barka. Ta tsinci zancen ne a bakin Aliyar lokacin da ta zo daukar zanin gadonta da ta shanya a kusa da motar da suka hau, tana fada ma Nafisa.Nafisa ta Ce,

"Ku gaida su, ni na kira ta a waya ba iya zuwa zan yi ba

Salma ta kalli Shatima, sannan ta kalli Aliya tace,Anty wace ce ta haihu?"

Aliya ta kalli Shatima, ya daka mata tsawa,

Da Allah ni shiga mu je"

Ya yi baya da motar tamkar zai ture Salma,tana jin lokacin da Aliya ke fadin,

"Ba ka fada mata haihuwar Amna ba?"

Ba ta ji me ya ce ba suka wuce. Baki Salma ta

_tabe tare da fadin,

"Allah ya raya". Har zuciyarta ta ji dadin labarin. To sun dawo tana Zaria din ne ko ko?Ba wanda zai ba ta amsa don haka a fili ta ce,

"Oho"A daki ta kira Badi' atu ta ce,

"Ashe Amna ta haihu?"Badi'atuta.ce

*Kina nufin ba ki sani ba?" Salma ta ce, suna Zaria din ne?"Cikin mamaki Badi'atu ta ce,Bakya gidan ne Kin yi tafiya?

Salma ta ce,

"Hmm, ina nan wallahi, amma Yaya bai fada min ba"

Badi'atu ta cE

"Wai kun samu matsala da shine na ga rannan da ya zo na tambaye shi ke sai na ga ya hada rai, sannan ya ce kina gida. Da ko da kanshi yake min zancenki"

Salma tace

"Tun laifin da na ce miki na masa da sallah shine har yanzu bai huce ba. Ko magana da kyar yake amsa min'

Badi' atu ta Ce,

"Wai ba ki ba shi hakuri ba ne?"

Salma ta ce,Na ba shi har sau ba adadi, amma ya ki hakura

Badi'atu ta ce,

"Wai wane irin laifi ne haka mai zafi?"

Salma ta yi shiru, Badi'atu ta ce, "Kina jina?"

Salma ta Ce,

"Ina jinki, sai dai in yi miki sako ki karanta"Badi' atu ta ce,

"To ki yi min sakon"

Ta rubuta mata sako kamar haka.

"Ya neme ni ne na kasa yarda, don ina jin tsoro shine yake fushi

Badi"atu ta kira Salma ta ce,

*Ke ma kin san dole ya fusata"

Salma ta Ce,
Chapter 9 · 0% Book details