← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

芦To ai daga baya na zo na ce na yarda; kuma na bi duk wata hanya don in ba shi hakuri amma yaqi, har ma na saba da yanda ya koma min yanzu"

Badi' atu cikin tausayawa ta cE

"Sai dai in ba ki hakuri in ce ki ci gaba da addu'a da kuma yi masa biyayya tunda ni ma ba wai na yi auran ba ne bare insan ko akwai wata dabara. Hajiya kuwa bawai tana yinki ba ne bare in kai mata kara Cikin sauri Salma ta ce,

"Don Allah ki taimaka

Karki fada, ke ma na fada miki ne don in ji sanyi a raina, ba wai don ki ba ni mafita ba. Ina son in yi wa Hajiya barka ne"

Badi'atu ta ce,Bari in turo miki lambarta, amma ai maijego England ta haihu sai ta dawo za a yi suna

Salma ta ce,

"Na ji tafiyar, na za ta ta haihu sun dawo ne. to ki turo min lambar har da ta kaka

Badi'atu ta ce,To, ko kuma ki fada ma kaka din tunda na ga ita tana yinki sosai, kin ga murna da na kai mata sakonki na sallah? Ta ce, Shatima ke ce zai ci riba a cikin matanshi"

Salma ta ce,

"Allah sarki Kaka, Anty Badi'atu ba zan kai mata Kara ba, kema amana na ba ki, insha Allah ba zan taba kai Karan mijina ba har abada

Badi'atu tace

"To Allah ya ba ki ikon jurewa"

Nan suka yi bankwana. Ba a fi minti uku ba sai ga sakon lambobi sun shigo. Ta kira Kaka ta yi mata barka, Kaka ta yi ta saka mata albarka, sannan ta kira

Hajiya. Salma ba ta sha mamakin yanda Hajiya ta amsa mata ba don ta zaci abin da ya fi haka ma.

An rada wa yaro sunan mahaifinshi

Muhammad Ja"afar, walima sosai Alhaji yayi a kofar gidan, Shatima ma ya kasance a abokansa. Dan sammako suka yi shi da Aliya.

Salma ta cire duk wata damuwa ta aje ta dage da karatunta, yanzu burinta shine ta shiga islamiyya

Ta bari sai ranar da babu aiki ta same shi ko a dakinsa yake. Tunda akwai islamiyya kusa da su, kuma babu tsada in dai ya barta to za ta shiga ko a aljihunta ne duk da ya rage abin da yake ba ta, ba ta fasa adanawa ba.Gaban Salma yana faduwa ta nufi dakin Aliya.

Cikin sa'a sai ga shi ya fito sanye da jallabiya, da alamu ba fita zai yi ba don takalmin tsakar gida ne a kafarshi. Ya kalle ta har zai wuce, ta yi sauri ta rusuna ta sunkuyar da kai cikin tsananin faduwar gaba.

Ya katse mata tunani, ta ce,

"'Amma da ma Yaya ina son in roke ka ne ko za ka saka ni a islamiyya. Saboda duk na manta da karatun da na iya

Shiru tayi, ta dago ta dube shi dan ta ga yanda

ya amshi maganar. Sai ta ga yana yi mata wani kallo mai cike da tsana, za ta fassara shi ko wulakanci, sai kuma ta ga ya sa kai ya fita abinshi. Ta dan yi jim a tsugunne, sannan ta mike ta nufi dakinta.

Sati daya tsakani ya zo ya aje mata wata leda akan kujera, ta fito kicin ta yi masa sannu da aiki ya amsa, dan ta samu ma yau ya amsa mata tunda watarana ko kallo ba ta ishe shi ba.

Ya ce,Ga shi nan kayan islamiyya ne, ki shirya anjima za ki soma zuwa Cikin murna Salma ta ce

"Na gode, Allah ya Kara budi

Page 14

MUN TSAYA

Ta sunkuyar da kai cikin tsananin faduwar gaba.

Ya katse mata tunani, ta ce,

"'Amma da ma Yaya ina son inroke ka ne ko za ka saka ni a islamiyya. Saboda duk na manta da karatun da na iya Shiru tayi, ta dago ta dube shi dan ta ga yanda ya amshi maganar. Sai ta ga yana yi mata wani kallo mai cike da tsana, za ta fassara shi ko wulakanci, sai kuma ta ga ya sa kai ya fita abinshi. Ta dan yi jim a

tsugunne, sannan ta mike ta nufi dakinta.

Sati daya tsakani ya zo ya aje mata wata leda akan kujera, ta fito kicin ta yi masa sannu da aiki ya amsa, dan ta samu ma yau ya amsa mata tunda watarana ko kallo ba ta ishe shi ba.

Ya ce,Ga shi nan kayan islamiyya ne, ki shirya anjima za ki soma zuwa Cikin murna Salma ta ce

"Na gode, Allah ya

Kara budi

Ya fita ba tare- daya saurareta ba. Ranar ta soma zuwa islamiyya, har da hadda za ta dinga zuwa sati da lahadi.

Maijego Amna sun dawo ranar Shatira da

Aliya da su Hajiya suka dira Kano. Sun samu gidan tankam da mutane, har sun soma tunanin ko sunan ake

An yi musu tarba, kuma an amshi kayan barkan da suka kawo. Shatima yana jin dadin zai ga kyakkyawan danshi, Hajiya kuma tayi tam da ganin yanda aka ajebkayan barkan kamar a wulakance, domin ta zuba kudi a kan wanda ta amsa a gurin Alhaji sannan sun z0 da manyan raguna guda biyu wadanda Alhaji Musa

mahaifin Nafisa ya siya. Ita dai Hajiya suna zaune ita da Aliya da maman Nafisa a dakin mahaifiyar Amna.

Sun gaisa da mahaifiyar da sauran bakin da ke dakin.

Anty Amarya ita ce ta gabatar da su da kuma kayan da suka kawo. 'yan dakin tareda Momy tunda sukace an gode ba su sake bi ta kansu ba, kuma ba su samu damar matsar da kayan daga inda suke ba.

Amna ta nufi dakin da aka sauki Shatima

saboda lokacin da suka iso sannan take wanka. Ba su jima da tashi ba, Anty Amarya tace ta shiga dakin

Momy su gaisa da su Hajiya. Ta shiga ta rusuna tana gaida su.

Hajiya cikin son nuna itace surukarta, ta fara fadin

"Sannu 'yata, sannu da arziki. Allah ya raya mana Muhammad Ja'afaru je gurin Shatima

Amna dai ta mike, tare da fadin, "Momy bari inje gurin Shatima

Hajiya ta wage baki cikin murna, ta ce, "Ai ko dai yana can dakin ko? To ina jaririn

Momy ta kalle ta, ta yi murmushi ganin zumudin da Hajiyan ke yi, sannan tace

"yana tafe

Hajiya, za a kawo muku shi. Yanzu ake shirya shi"

Aliya tace "Ni ma shi na Kosa in gani"

Amna ta yi sallama ta shiga dakin da Shatima yake, ya aje wayarshi cikin sauri da doki ya nufi Amna suka rungume juna. Suka sumbaci bakin juna sannan suka zauna kan cinyarsa ya dora ta.

"Ina yarona ne?"

Ta sa hannu ta tallafi fuskarsa, "Ana shirya shine, ba mu dade da tashi ba ka san shigowar asubahi muka yi, sai kawai muka ci gaba da bacci"

Ya sa hannu ya shafa cikinta,

"Baby ya fito ko?"

Suka sa dariya, ya ce, "Kin kara kyau Amna"

Ta ce "Ko?"

Ya ce, "Sosai kuwa".

Aka kwankwasa Kofa, Amna ta mike da sauri don ta san Sumayya ce. Shatima shi ma ya mike tsam

ya tari Amna, ya amshi jaririn. A Kirji ya manna shi

tare da lumshe ido. Wata irin Kauna mai tsanani yakeji, da tsantsar son yaron. Kamshin jaririn ya sa shi kara
jin wani shauki, ya dago cike da matsanancin farin ciki ya kalli fuskarta.

'Amna na gode,Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, don kin gama min komai a rayuwata

Cikin jin dadi da alfahari tace, "Allah ne ya ba mu ba wayonmu ba ne"

Ya ce, "Duk da haka kin yi dawainiya da cikin,kin ba ni dan fari mai kama da ni, kuma ki ka zaba mishi sunana

Ya sa bakinsa a kunnen yaron ya yi masa kiran sallah, ya jaddada masa huduba. Sun jima har aka kawo abinci, tare suka ci cikin kulawa da Kaunar juna.

Hajiya dai ta kasa cin abinci saboda har lokacin ba taga jikanta ba.

Aliya ta ce, "Wai ni a raka ni inda yaron nan yake don shi muka zo, amma har yanzu ba mu ganshi ba"

Anty Amarya tace, "Au na manta, ina zuwa".Can ta dawo, "Suna gurin Babanshi"

Hajiya tace

"A karbo mana shi"

Aliya ta mike, "Nuna min inda yake in karbo shi'

Suka fita da Anty, Aliya ta Kwankwasa kofar.

Shatima ya ce, "Shigo". Don a zatonshi Sumayya ce.

Tana sako kai ta ga suna kicin-kicin ba shi nono, Shatima ne ma ke rike da nonon. Aliya ta yi saurin sakin fara'a tare da danne wani Kululun takaici da ya taso mata, ta ce, "Haba! Ashe kuna nan da dan muna can muna jiran gain jariri?"

Shatima ya ce.

"Au ba ku ganshi ba? Yanzun yana cin abinci"

Amna ta kalle ta, "Da ma har da ke aka zo?"Cikin mamaki Aliya ta ce,

"Ai mun gaisa kuwa lokacin da ki ka zo kuna gaisawa dasu jiya"

Amna ta kalli yaron, sanna ta ce. "Ban luraba

Yaron ya ja nono da karfi, amna ta lumshe ido tare da fadin, "Wash!"

Ya ce,

"Sannu". Ya sa hannunshi yana shafa mata baya

Aliya ta tabe haki tare da kau da kai, Amna ta kalle ta, "Zauna mana'

Ta ce Bari in je kun kawo shi, muna dakin Hajiyarku

Amna tace Momy kenan?!"

Aliya ta fice cike da jin zafinsu, amma tana zuwa dakin sai ta saki fara a, "Za ta kawo shi.

Maman su Nafisa ta ce, "To ke me ya sa baki karbo shi ba?"

Maimakon ta ce nono yake sha tunda ita mata gani, amma sai ta ce, "Ina, gani dai Qila yunwa yakeji"

Hajiya ta dan yi shiru, domin yanzu ta yarda

Zarginta wulakanci ne kawai. Ita da jikanta na fari sai an mata wulakanci zata ganshi, bayan ta fi su iko dashi ma? Gashi ita kanta uwar maijegon sai wani jin kai takeyi, taki ko da hira da su sai labarinsu suke da

"yan uwanta da kawayenta.

Aliya ta katse tunanin Hajiya da cewa,

"Dubi yanda aka bar kayan yaron can sai zama a kan akwatunan ake yi. ko magana za a yi musu su bude su gani Kan Hajiya ya sake sosuwa tace Kar wanda yayi musu magana, in mun tafi su zubar da shi
Chapter 10 · 0% Book details