← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe Anty Nafisa ma ta haihu?"

Sai da ya saka Kafa a waje sannan yace"Eh".

Gidan su Nafisa ta koma, Hajiya ta hada kayan barka ta kai. Alhajin su Shatima ya sai raguna. Ranar

barka ko in ce ranar kauri, gidan cike da dangi da yake su ma akwai zuri'a.

sunan Amna, Aliya da ke zaune kusa da maijego a bakin gado tana sauraron hirar da su Nafisa suke yi ita da yan uwanta. Nafisa ta ce,wai da sunan Mus'ab wa ta yi muku cake na ji ana ta labarin dadinsa

Ta ce, Gidan Alhaji Sani ne

Nafisa tace

"Don ni ma duk abin da ya yi ma wacca matar a sunanta ni ma fa haka zai min Aliya ta ce,

"Kar fa ki ce komai, kin dai san su suna da halinsu, wani abin da kansu za su yi Nafisa ta ce,

"Ina ruwana, dole dai ya yi min duk abin da ya yi mata"Aliya ta ce,

"Ni ban ce kar ya yi miki ba, amma kar ki ce komai

Safina tace

"Dole ya yi mata mana, don su masu kudi ne?"

Nan dai suka shiga surutu. Aliya ta ji dadin haka, domin ita ba taqi su kwabe ita da Shatima ba. Nafisa tace

"Ni ya zo mu yi maganar kayan

fitar suma, don su ma irin nata nike so'

Aliya ta ce, "Sun ko yi kyau kayan sosai"

- Nafisa tace

"Ai irinsu sak zai min".

Haka dai suka yi ta mata famfo tana hawa kamar farashi.

Salma tana son zuwa suna, amma ta san ba za a barta ba. Hanya daya ce kawai ta saka Aliya ta nemar mata izini, Ta san Aliyar za ta yi tunda tana son irin haka.

Ta riski Aliya a dakinta, tace

"Anty ina son
don Allah ki rokar min Y盲ya, ina son zuwa suna ko zai bar ni"

Ta balla mata harara, "Ke ba ki da baki ne?"

Salma ta ce, "Ai ba zai saurare ni ba ne Anty,

ke kadai yake jin maganarki ba ya miki gardama

Salma ta fada cikin son tula mata kasa.

Aliya ta saki murmushin jin dadi, ashe har

mukaminta ya kai haka? Kishiyoyinta har sun gane ita
din babba ce, gaskiya abin ya yi mata dadi. Wannan
sokuwar ma ta gane bare sauran, lallai ita ce a sama.

Cikin isa ta ce, "Shi kenan, je ki zan tambayar miki"

Salma ta ce, "Na gode"

Shatima ya zauna a bakin gadon fuskarsa dauke da murmushi, ya amshi jaririnsa daga hannun Hamida.

Ya kalli Nafisa wadda ke cin gasasshen nama a cikin faranti, ga yaji tana dangwala.

"Sannunki mai jego"

Ta ce,Sannu mijin maijego"Suka yi"yar dariya. Ya kalli yaron Babana din nan fa yana kama sosai da Jafar"

Ta kalle shi, "Wane ne Jafar?"

Shatima ya ce, "Yayanshi mana

Ta dan tabe baki, "Ni dai wannan ya fi min kama da kai"

Ya yi murmushi a ransa ya ce, Nafisa sarkin son kai. A sarari ya ce,

"'Duk su biyun suna kama da ni ne. Wannan ya nuna karfin jinina ne"

Ta yin murmushi, "Menene kuma na yin al fahari?" 鈥簃urmushi yayi Yace

"Dole in yi don duk wanda ya dube su ya san yayana ne babu bata lokacin kwatance"TaceKa, Ni lokaci yana ta tafiya amma ban ji kayi maganar kayan suna ba Yace,Kayan suna kuma?" Ta sake kallonshi,na fitar suna mana Ya ce, *Shi nazo mu yi magana. Anty Momiy ba tazo ba?" Ta ce, "eh bata zo ba Yace,zatazo takawo miki kayan ki zaba.Kala uku za ki dauka, Aliya ma a bata guda daya"Nafisa ta Ce,

"Irin kayan Amna kawai za a kawo min, ko.ba ita c猫 ta kawo mata ba?

Ya ce, a,a bansan inda suka sai kayansu ba, Nafisa ta dube shi cike da zargi. Tace Kawai dai ka ce ita ka yi mata irin nasu na masu hali, ni kuma ka yi min na daidai ni

Ya. tausasa murya da nufin. kwantar mata da hankali, ya ce, "Nafisa in na fada miki cewa.banyi,. wa

Amna kayan fitar suna ba za ki yarda?"

Ta sake hade rai, "Ba zan yarda ba gaskiya?

Ya ce, "To ban yi mata ba, kuma ita da kanta tace in barshi" Ta tura baki, "Ni dai a yi min adalci ah to!"

Ya dan daga murya don nuna jin zafinsa, *Kina sa ran zan cuce ki kenan?"Ta yi shiru.

Yace

"To na gode"

Ya mike ya kwantar da yaron a kan gadon ya yi ficewarsa. Suka yi kici6is da Mama ta fito kicin da Fulas na ruwan zafi za ta dakin mai jego.

Ta ce,

"Ba dai har ka fito ba? Ga abinci can
Hamida za ta kawo maka'

Ya ce, "Na koshi Mama. Nafisa ce ta bata min tai?

Ta ce,

"Nafisa ko?" Ta aje kayan tare da fadin,Zo nan"

Ta shiga dakin su Hamida. Ya fada mata duk yanda suka yi, ya ce,

"Mama Amna ban sai mata kaya ba, saboda ta ce kudin abincin da zan ba ta ya yi kadan kuma ba ta son a ce na kasa"

. Ya fada mata duk yanda suka yi da Amna. Mama ta Ce,

-Kai Nafisa kishi yana son ya maida ta mai hassad Ta dubi Shatima,

"Kana ji ko Baba, ka kwantar da hankalinka, shirme ne ma in tace za ta hada kanta da Amna. Abin da za a yi idan Momiyo tazo kawo Kayan, to ka zabi wanda ranka ya yi maka kuma daidai

Karfinka ka siya. Batun abinci kuwa babu takura, duk abin da Allah ya hore shi za a yi. Duka yaushe aka gama waccan sabgar? Mu ne fa iyayenka, mune masu yi. Don Allah ka kwantar da hankalinka ka ji ko?"

Ya Ce,

"Balle ma ita ma zan mata komai da yardar Allah. Na fi son ta kwantar da hankalinta Mama ta ce,

"Babu komai ka kwantar da naka,ita ma za ta kwantar da nata hankalin"

Ta so ya ci abincin, yace ya koshi.

Gidan Hajiyanshi ya wuce: Tana zaune a falo,

Ya gaishe ta, ta ce,

"Zuwan kenan?"

Ya ce,

"A'a tuni na zo, daga gurin su Nafisa nake

Ta ce,

"To ka sallame su ko?"

Ya ce,

'"'Abin da na je kenan. Anty Momiyo bata kai mata kayan ba ma"

Ta ce,

"Ni dai ka yi mata komai kamar yanda
da yi wa Amna, bana son ka yi rashin adalci tsakani,

bare wasu zantuka ma su shigo. Allah ma ba zai bar kaba

Yace

"Insha Allah bazan canza daga tarbiyyarku ba Hajiya, kuma Amna kudi na bata shi ne

Da na so da Anty Momiyo ta zo ta kawo kayan da na san ko na nawa ta dauka, sai in ba ta sauran kudin kamar daidai adadin kudin da na ba Amna

Hajiya cikin gamsuwa tace, To ka kira

Momiyo din kawai mana' Ya ce,

"To, bari in kira ta".Bayan sun gaisa ya ce,

"'Anty ashe ba ki kawo mata kayan ba?"

Ta ce,

"Kai dai bari Shatima. Autana ne ba shida lafiya, ka ganshi nan yanzun nan na gama ba shi magani ya kwakkwara amai"Shatima ya ce,

"Allah sarki. To Allah ya ba shi

"lafiya. Ya za a yi kenan?"

Tace

"Gobe insha Allahu zan zo in kawo mata" Ya ce,

"Uku za ta dauka.

"Yan nawa-nawa ne?"

Page 17

Mun tsaya

Daidai adadin kudin da na ba Amna

Hajiya cikin gamsuwa tace, To ka kira

Momiyo din kawai mana' Ya ce,

"To, bari in kira ta".

Bayan sun gaisa ya ce,

"'Anty ashe ba ki kawo mata kayan ba?"

Ta ce,

"Kai dai bari Shatima. Autana ne ba shi da lafiya, ka ganshi nan yanzun nan na gama ba shi magani ya kwakkwara amai"

Shatima ya ce,"Allah sarki. To Allah ya ba shi

"lafiya. Ya za a yi kenan?"

Tace

"Gobe insha Allahu zan zo in kawo mata" Ya ce,"Uku za ta dauka.

"Yan nawa-nawa ne?"Ta ce, -Atamfa ishirin da biyar, leshi kuma

talatin da biyar

Ya Ce,

"Ta Gauki leshi guda daya, atamta biyu.

Nawa kenan?' Tace,

"Tamanin da biyar

Shatima yace

"To a bata haka. Sai kuma ita

Aliya a bata leshi guda daya"

Ta ce, "To 'yar gidanka fa?"

Ya ce, "Barta wannan, ba lallai ta zo sunan bama. Kuma ga biyan kudin makarantarta. Gaba daya kudinki zai zama dari da goma ko?"

Ta ce, Haka Yace

"To za a dai daga min Kafa

Ta ce, Babu komai"

Bayan sun yi bankwana ya dubi Hajiya,

"Cikin dari da hamsin an cire tamanin da biyar, saura nawa?"Hajiya ta ce, "Sittin da biyar"

Ya ce, "Shine abin da zan ba su su yi girki.

Domin Amna ma dari da hamsin na ba ta

Ta ce, "Na ji kana a ba Aliya leshi, ita gudar fa?"Shatima ya ce, "Kyale ta ba dole ma ta je sunan ba fa"

Hajiya ta yatsina fuska, "Ni dai bana son a ja

- sunana a ce ni ce na hana a yi wa wani

- Shatima ya ce,Ga kudin makarantarta, sannan ta shiga islamiyya da hadda kwanan nan' Hajiya ta tabe baki tare da fadin,

Umm, ku dai ku ka sani

Ya mike, "Bari in leka gidan Munnir in wuce"

Ana gobe suna Salma ta koma gurin Aliya, don

ranar dakin Aliyar ya kwana, tace

"Don Allah Anty

kin ko tambayar min zuwa gidan sunan din?"

Aliya ta tabe baki, "Na manta sam. Amma bari dai ya dawo"

Duk da haka Salma ta tura mishi sakon cewa.

za ta je kitso da Talle a makota. Ok kawai ya turo mata.

Aliya don ta nuna ma Salma gadara, bari ta yi sai da Shatima ya dawo ya shiga dakin Salma, sannan tabiyo shi za ta tambaya mata unguwa a gabanta. Kai

tsaye ta shiga dakin Shatima yana zaune a tsakiyar katifa yana aiki a laptop. Ta zauna a bakin katifar tare da fadin,

"Sannu da dawowa Ya amsa da,

"'Sannunki. Kafin ki ji dadin zama hado min shayi"Ta ce,

"To mijina, ko kwanciya nayi ai dole in tashi in hado maka shayi".

Ya ce, "Yau dare zan raba ina aiki, don ina da aiki. Ga shi za mu yi sammakon tafiya Zaria, saboda taron suna

Ta ce,

"Yauwa, da ma na zo in maka magana ne

a kan ya kamata Salma ta je sunan nan. Fisabilillahi
Chapter 12 · 0% Book details