← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Naso Su zauna anan gabadaya

Hajiya tace,

"A'a sam ba zai yiwu ba, ga dai

abinci nan su ci, kowa ta kama gabanta

Nafisa tace

"Har ni Hajiya?"

Hajiya ta ce,

"Ai ke nan gidan ubanki ne, in zaki zauna zauna mana

Salma dai hakan ya yi mata dad矛, don tana

kewar Innarsu. Abincin ma ita ba ta ci na kirki ba saboda doki.

Ita da Aliya ya dauka don ya kai su gidajensu,

Nafisa ta ce, sai Alhaji ya zo sun gaisa.

Aliya ya soma saukewa, sannan ya nufi kofar

gidan su Salma. Cikin doki ta fito za ta dauki kayanta.

Ya yi saurin riko hannunta, "Kina ta sauri za ki rabu dani ko?"

A hankali ta kalli hannunsu, sannan ta dago ta

kalli fuskarshi. Babu ko digon son Salma a zuciyata Kalaman da suka dawo mata gar a zuciya kenan. A hankali ta zame hannunta,Cikin sauri ya sake rike hannun gam!

"Fadi abin dake ranki"

Ta Kirkiro murmushi, "Ba ni da magana"

Ya ce Ba za ki yi kewata ba?"

Ta ce,

"Ko dakina zan yi kewarshi bare kai. Ina da sabo sosai

Ta kuma janye hannunta daga nashi, tare da

Fadin, "Bari in shiga ciki'

Ya sauke ajiyar zuciya, "Ban yarda ki je ko ina ba ba tare da kin sanar da ni ba'

Ta ce, "Ni kadai kacema haka Don Anty

Aliya ban ji kace mata haka ba". Cikin shagwaba tayi maganar.

Shatima ya ce, "Ai ita ta san me ta ke yi"

Salma ta ce, "Humm, kai dai kana yinta dayawa Yace Me ya sa ki ka ce haka?"

Salma ta ce Komai ita".Ya ce,

"To shi ne ya sa ki ka ce na fi sonta?"

Tace

"To wa ka fi so a cikinsu?"

Ya ce, "Ya aka yi ki ka cire kanki?'

Ta ce,

"Yaya kenan, ai da ma ni ba na cikinsu sam"Ta yi murmushin Karfin hali sannan ta fice daga motar da sauri, tare da fadin, "daga min baya in Dauki kayana Ya ce, "A bude yake, ki daga ki dauka

Tana fito da kayan shi ma yana fitowa daga motar yana kallonta.

"'Kin cire kanki a cikin matana saboda har yanzu ba ki san so ba?"

Ta ce, "Humm, ka tafi abinka Yace" Duka kika kwaso kayanki?"Ta ce,

"Ba ka ce in dauka duka ba? Amma ka
cire wanda ka ce in ba ka ko?"

Ya ce,A gabanki na dauka, har kin manta?"

Page 6

Ta ce,"To ba za ka shiga ku gaisa da su Inna ba?"

Ya dubi jikinshi,A,a zanzo na musamman Kananan kaya na saka yanzun".Ta ce,

"Shi ke nan, amma don Allah ka kawo min Badi'atu ta kawo min kayana

Ya ce,

"In ban samu zuwa ba sai Mustapha ya kawota Ta ce, "Duk daya ne".

Salma ta yi murna da dinkunanta da Badi'atu ta kawo, sun yi kyau sosai da yake ita ma Salma Dankasa kusan Kirarsu daya da Salma din. Sai dai Salma Dankasa ta fita cika idanu.

Salma ta dubi Badi"atu ta ce,

"Anty Badi'atu nawa ne kudin dinkin?"

ido A Badi' atu ta ce, "Yaya fa ya bada

Salma ta CE Kai! Ya bada kuma shi da ba shi da kudi? nage Badi'atu ta ce,

"Ai tun lokacin da ya kawo kayan ina kai wa ana fadin kudin ya biya"

Sai da Salma ta yi wanka ta shirya, sannan suka

tafi tare da Badi'atu. Can gidan Hajiya Kaka suka nufa,

sun bar Inna cikin murna ganin yanda Salma ta yi kyau, ga shi ta waye abinta.

Da dare suka bar gidan Hajiya Kaka, Salma ta

dawo su Badi'atu suka wuce. Ta ciro kudin da ta zo dasu ta ba Inna dubu arba' in a ciki, ta rike goma. Ta ce a sai mata wani abin. Sauran da ta cire ta sa a jakarta tace gobe daurin aure zan so ace da kudi a jikina, mutum ya dan yi alheri.

Abin da ya ba Aliya mamaki, ranar daurin aure sun hadu a gidan kaka, duk kowa ya zo ya kai

gaisuwa ana zaune, Salma ta shigo ta yi kyau sosai

cikin atamfar ankon, doguwar riga. Ga dauri ta sha abin sha'awa. Ita ma ta je gaban Kaka ta durkusa har Kasa ta gaida ita.

Kaka ta ce,Wace ce wannan?"

Aliya cikin gadara da son ganin an wulakanta

Salma ta ce,

"Salma ce kaka, matar Shatima"

Kaka ta dube ta,

"Masha Allah, to Allah ya yi muku albarka dukkanku".

Salma ta bude jakarta ta ciro leda baka babba,ta mika ma Kaka da hannu biyu ta ce, "Ga shi KakaTa amsa tare da tambaya,

"Me muka samu?"Salma ta zauna gefe ba ta ce komai ba. Kaka ba

ta bari ba, ta bude ledar. Turmin zani ne da turaruka sai

"yan dari biyar guda hudu. ta kalli Salma,

"Allah ya yi

miki albarka. Ina jin ke ce za ki saka ma uwar Shatima da abin da ta yi min"

Nafisa ta mike ta fice, Aliya kuma aka yi tsuru cikin jin kunya. Dole ta shiga jerin masu cewa, "Amin"

In Kaka ta yi ma Salma addu,a, ga shi Kaka ba ta raina abin fada, kow脿 ya zo a zuri'arta sai ta nuna.

"'Kun ga abin da matar Shatima karamar ta kawo min"

Dole Aliya daga sallah ta sulale ta gudu; Salma ko da yake kanta a waye yake, tuni ta

shige cikin sa"anninta suna ta hotuna. Karyar kowa dai

ta turanci ne, kuma ita ma yanzun ta kware gurin fesoshi. Hakan ya sa wasu daga cikin dangin Shatima

sha'awarta. Sai da aka dau amare sannan Salma ta je ta sallami Kaka, ta samu Hajiya a gabanta zaune. Ta durkusa tana gaida Hajiya don ba ta ga zuwanta ba

Dole Hajiya ta amsa, ta kuma yi mata godiya don Kakar ta riga ta fada matA kuma ta bukaci Hajiyar da ta yi mata godiya a gurin Salma.

Kaka ta ce,

"Allah ya yi miki albarka, ki gaida manyan naki, ki wa 'yar uwar taki ban gajiya Da yake Yaya Hadiza tazo

Tana fitowa don ba nisa ta hau hanya. Wata mota tana ta yi mata horn t脿 yi banza, Kila ma irin mazan nan ne sun ga duhun dare. Motar ta yi gaba kadan ta tsaya, Salma ta fusata, ta ce, kila zan ji me motar nan. Ta zo za ta wuce, ta jikin motar ta ji an ce,

"Yammata ji mana". Ba ta tanka ba, amma muryar da ta ji ya sa gabanta faduwa, har ma ta waiwayo ta kalli motar,. Bata san motar ba, amma muryar irin ta Shatima ce. Ji tayi an kara cewa,

"Don ana miki magana shine za ki

share mutane?"

Ta waiwaya da sauri, tare da fadin, "Kai ina da miji? Maganar ta makale ganin Shatima. Tayi muryar shagwaba, "Haba Yaya, ka ba ni tsoro dayawa Ya ce,

"Wa ya ce ki fito titi? In wani ya taka ki

kamar yadda na yi din nan fa?"Ta ce,

"Ai na ga babu nisa ne Ya kama hannunta"Muje in kai ki gida禄. Baya ta shiga, sai ta ga ashe Munnir ke jan

motar. Ta gaida shi, sannan suka sauke ta kofar gidansu. Ya miko mata leda, "Ga shi rabonki ne

Ta amsa, ko ba ta buda ba ta san kaza ce, don taga suna ci suna hirar gidan biki.

* Tana nuna wa Innarsu hotunan da suka dauka,

Inna ta ce,

"Na ga abubuwan da Hadia ta zo da su na

rabo Salma ta ce, "Sun yi rabo sosai. To auran fa yara biyu, kuma kin san Babansu ya rasu, amma an yi

musu komai. Gaskiya zuri'arsu suna da yawa, ga zumunci"

Inna ta ce, "Gaskiya sun more, don duk zuri'ar

da ke rike da zumunci ba ta tabewa" Salma bata bada wani labari da zata bata

sunan mijinta ko na danginsa ba.

Har Hajiya da su Yaya Hadiza suka dauko

zancenta, sai ta nuna ai yanzun Hajiyar ta daina nuna mata kiyayya. Inna ta juya zancen da Salma ta kawo mata, ta ce, "Lokacin da na fita takaba ma Hadiza ta sai min turmin zani, sai su Babarku sun hado min zannuwa uku, har da hijabai daga kauye"

Salma ta ce, "Ai kuwa an gode. Ni ma na so zuwa Ya Shatima ya hana, wai sai ka ce biki?"

Inna ta ce,Gara da ya hana din, tunda lokacin duka kwananku nawa?"

Ta ce,"Mun dan jima fa Inna"Ta ce,

"Ai yanzu komai ya wuce"

Washegari za su koma gida Yaya Hadiza tazo dan -su shawarta kan kudin Salma, ita Yaya Hadiza cewa ta yi,; a canza mata kujeru tunda guda uku ne sai a siyo mata saiti. Salma tace duk yadda aka tsara, amma wa zai
Siya nawa? Hadiza ta Ce,

"Gun Lami dillaliya aka sai naki,kuma za ta siye su sai a cika a sai wasu

Salma ta ce,To motar da za ta kwaso wadancan fa?"Hadiza tace

"Ai tana da masu mota, illa dai

Ki kira mijinki ki tambaya, sai mu je gidan a zaba

Suna tsaka da hira da Hajiyarshi akan abin da ya shafi haihuwar matanshi, da kuma zuwan azumi da

sallah wanda ake kan shirinsu, sai ga kiran Salma ya shigo! Ya daga tare da sallama, ta amsa sannan ta gaida
shi. Ya amsa tare da cewa, "Ya ya dai Salma?"

Ta ce, "Da ma za mu je gidan wata mai saida kaya ne za mu duba kujera".

"Ke da wa za ku?" Ta ce,

"Yaya Hadiza" Yace

"To kar a zauna anjima za mu tafi"

Ta ce,Insha Allah

Sun je sun zaba, kuma ta amince amma da

yarjejeniyar za ta bi motar kaya don ta ga wadancan.

Sun amshi lambar juna don mai kaya ba sanin gidan tayi ba. Karfe uku tana kwance a kan tabarma a tsakar

dakin Inna, sai ta ji sallamar Yaya Auwal. Su biyu ne

suka aje buhun shinkafa karamin da buhun gero, sai
suga da kayan tea. Salma ta ce,

"Daga ina?"Sallamar Shatima ya sa ta samu amsarta. Kan
tabarmar da ta tashi daga kwance nan ya zauna kusa da

Page 7

Ita. Ya rusuna yana gaida Inna, duk da cewa a zaune yake don girmamawa.
Chapter 4 · 0% Book details