Sashe 14
Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wace Salma? Na lura rawar kai yana damunki, in kin yi wasa zan cire ki daga makarantar nan. Ina son ki sani kar ki sake ki sake janyo min wani tarkace gidan nan"
-Jikin Salma a sanyaye, cikin sanyin murya ta ce,Ka yi hakuri, insha Allahu ba zan sake ba"
Tsaki ya ja, sannan ya juya ya fita.
Sannu a hankali su Salma suka yi jarabawar
shiga S.S 2 suna gida suna hutu, sai dai islamiyya,Lokacin Shatima ya samu karin girma a gurin aikinshi inda aka maida shi ofishinsu da ke Abuja. Hakan ya sa sai bayan sati daya yake zuwa Kaduna, Nafisa ya fi tafiya da ita don ita ce ba ta zuwa ko'ina, Aliya ba ta so hakan ba, amma babu yanda za ta yi tunda ga aikinta.
Cikin haka Nafisa ta haihu, danta namiji.
Wannan karon a gidan Shatima aka sha suna, inda yaro ya ci sunan Alhajin su Shatima. Tunda ta haihu ta lashi
takobin cewa fa sai ta yi tsarin iyali, kuma sai ta koma makaranta.
Lokacin ne Shatima ya samu damar biya musu
kudin aikin hajji shi da Aliya. Da lokacin tafiya ya y矛 suka tafi, Aliya ta tsananta rokon Allah a kan haihuwa.Ta yi roko sosai, ita dai Allah ya ba ta haihuwar ya'ya maza ita ma. Da aka gama aiki ta hakuri, kuma ta
Kara kyau da yar Kiba.Lokacin tafiyar ne dai kansu tafi har aka yi dan rikici, Nafisa ta nuna damuwarta, tare da koratin yanda yake nuna Aliya ta fi kowa, shi ya sa ma zai je makka da ita. Ya ce, ba haka ba ne, duk yana sonsu don dai ita babba ce, kar ta damu duk za su je. Amna kuwa ko a
jikinta don Saudiyya ba bakuwarta ba ce. Salma kuwa
ba ta ji batun tafiyar ba har sai da suka z0 mata sallama, har Aliyar tana fadin a yafi juna.
Sun yo tsaraba, ko da Aliya ce ta yo tsarabar,don shi bai siyo komai ba tunda ba zuwanshi ne nafarko ba. Ana ta rabon tsaraba, Salma dai an ba ta wata
"yar yaloluwar riga kamar ta bacci, ita dai ta yi godiya ta amsa.
Cikin ikon Ubangiji ko wata ba a yi ba sai ga
Aliya da ciki, murna gurinta da shi kanshi Shatima ba a magana. Nan ko ta shiga kaudi da salo, Shatima kuma ya kama biye mata.
Ita Salma yanzun damuwarta daya, duk yan
ajinsu mafi yawa za su yi SSCE, ita ma ta so a biya mata, amma tana tunanin tunkarar Shatima, ga shi an
kusa bikin Badi'atu da su Hamida, da Mami kannen Nafisa. Ta sani duk harkar kudi ce shi ya sa ta kasa
tunkararshi da zancen. Zuciyarta tana yawan fada mata
cewa, ta same shi kawai ta ji abin da zai ce, amma ta
yanke shawarar sai in ya dawo dakinta za su yi
maganar.ranar da ya dawo dakin nata tana jinshi yana kallon labarai amma ta kasa yi masa magana. Sai ta yi
kamar ta tashi, sai kuma ta koma ta sauna. A karo na uku ne ta yi ta-maza ta tunkari dakin. Sanye ta ke da
kayan bacci masu dan kauri, don yanayin sanyi ne lokacin. Duk da cewa, ba wannan ne karo na farko ba da ta shiga dakin, amma bai hanata diriricewa ba,
kamar dai kowane lokaci in ta shiga.
Yana kwance tsakiyar katifar ya ware A.C duk da sayin da ake yi, amma ya rufa da bargo.
Hankalinsa kaf yana kan talabijin da yake kallo. Ya maido da kallonsa ga kofar da aka turo, ya kalli fuskar
Salma sosai, kaman mai yin nazari a kan abin da ta z0 da shi. Sannan ya sake maida kallonshi ga labaran da yake kallo. Ta rusuna gwiwa biyu a gaban katifar, sannan tace, "Ina yini Yaya?"
Ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba. Hakan
ya sa ta ji dan karfin gwiwar da ta shigo da shi ta rasa.
Jin shirun ya yi yawa yace
"Lafiya?"
Ta dago ta dube shi, har lokacin idanunsa suna kan talabijin, tace *鈥aya dama na z0 ne.
Sai kuma ta yi shiru.Ya dube ta, "Kinzo me?"
Cikin sauri ta dube shi. Ya tsare ta da idanunshi ta sake sunkuyar da kai,
"Yaya a ajinmu ne aka ce duk wanda yake son ya zana jarrabawar fita, to ya biya sake yin shiru, ga sanyin A.C din ya soma ratsa ta, har ta soma kaduwa
Ya ce, -Ke kina ajin fita ne?"
Page 19
Mun tsaya

Ta Ce "A'a.
'yan dai ajinmu ne mafiyawa an biya musu za su fitan; shine ni ma nace bari in fada
maka ko kana da halin biya min
Ya yi shiru yana kallonta yanda take kaduwa kanta a Kasa ya san sanyin A.C dinshi ne, sai ya dauki remote ya kashe, sanan ya canza harshe daga Hausa zuwa Turanci.
"Ba ni da tabbacin kin san me ki ke yi a
makaranta har da zan biya miki ki yi jarabawar fita"Ita ma cikin harshen Turanci ta ce,
"Yaya bari in debo maka dukkan sakamakon jarabawa ta ka gani,har ma da kyauttukan da na yi ta samu a lokaci daban-daban in za mu yi hutun canjin aji".
Ya daga hannu,
"Barsu, kar ki kawo min me yasa ba ki nuna min ba, tun a lokutan da ki ka same su?"Ta ce,
"Yaya ina tsoro ne kar in maka magana ka.Ya katse ta,
"In cinye ki? Ko ba haka ba ne?
kina tsorona kar ki fada min in cinye ki mana!"Cikin d盲ga murya ya ce,
"Bari in fada miki wani abu. Zan biya miki kudi ki yi jarabawa Amma ina son ki sani matsawar ki ka fadi jarabawar ko ki ka rasa darasi daya aciki, to fa kin gama karatun boko. Baza ki je jami a ta Cikin sauri ta ce,
, "Na yarda Yaya".YaCe.
"Shi kenan, ki je zan je makarantar taku Tace
"Na gode sosai da yawa Yaya"
Bai ce komai ba, ta tashi ta fita.
Suna cikin aji a zaune suna rubutu, sai ga wata ta z0 tace
"Salma A Bashir ta zo"
Tana zuwa ofishin shugaban makarantar sai taga Shatima. Sun tabbatar masa zata ci jarabawar domin duk ajin an san Kwazonta. Shatima ya biya aka ba shi takardar shaida, ita kuma aka ce ta koma aji in an tashi tazo za a yi mata hoto da sauran abin da ya rage.
Kwanci tashi lokacin jarabawa ya yi, Salma suka zana suka koma gida jiran sakamako da kuma lokacin zana jamb. Cikin wannan hutun ne bikin su Anty Badi atu da su hamida, Don haka ta tattara dukkan kokarinta ta bada shi a islamiyya da hadda.
Balle yanzun da ta ke ajin sauka.
Wata juma'a Salma tana tsaka da muraja'a sai ta ji sallamar Salma Dankasa, da murna ta tare ta suka rungume juna. Ta kalli Habiba Sulaiman ta ce,Yau
wace rana ga ki a gidanmu?"
Habiba tace
Duk suka sa dariya.Sun zauna ta ba su abinci da na sha, suka ba ta katin biki da anko na bikin Habibar ne. Salma tana juya katin ta ce,
"Ku saka ni a addu'a a bar ni zuwa wannan biki ko da rana daya ne"
Salma Dankasa ta zaro ido,Har yanzu bai daina takurawa a kan fita ba yayan nan naki?"Salma tace
"Har yanzu baya bari. Sai dai wani
lokacin ba na ganin laifinshi in na ga yanda
'yammata ke lalacewa a wannan zamanin namu. Bugu da Kari ina karanta littattafai ina Kara samun wayewar kai"Habiba ta ce,
"Dalilin Babanmu kenan da ya tattara mu yace aure. Har da Fatinmu wadda ko sakandire ba ta gama ba. Sai dai ya lura tana da janye janyen kawaye
Salma Dankasa ta ce,'
"Mu ko Babanmu yana da son karatu, kuma ba ya kawo komai a cikin ransa game da mu. Sai dai mu ma fa muna karance-karance mun san abin da zai cuce mu, don haka waye zai kai kanshi?"
Sun yini sannan suka tafi.
An kusa sati Salma tana tufka da warwara kafin ta iya tunkarar Shatima da katin biki, cingam da kuma anko. Ranar yana dakinta
tuwon shinkafa ta yi da miyar ganye Shatima yana cin duk abinda ta girka yanzun, musamman in ta yi abincin gargajiya. Domin ta koyi kalolin girki a cikin littattafan
Hausa da take karantawa.
Ranar dai ta yi karambanin gyara masa dakinsa,don kullum tana son ta gyara, amma tana jin tsoro.
Wani lokacin ma kulle dakinsa yake yi. Ta goge kayan wutar ta sa turare, sannan ta jera masa abincin. Tun kafin ya dawo sallar isha ta gama komai,
Da ya shiga dakin ya yi ta kallon ko'ina dakin yana ta kamshi da kyalli, babu kura. Ya yi wanka ya saka jallabiya ya zauna kan katifar yana cin tuwon cikin nishadi, har yana zance da zuciyarshi cewa,akwai kuwa abin da ya kai tuwo dadi? Ga labarai yana kallo abinshi.
Salma ta yi sallama tare da dan tura kofar. Ya amsa idanunsa na kan wayarsa da ke ringin. Ya daga yana waya, ta kwashe kwanukan don ya gama ci. Ta dawo ta tsuguna tana jiran ya kare wayar da Hajiyarshi suke magana a kan bikin Badi' atu.
Da ya gama ya dube ta, "Mene ne kuma, don na san ke ba a ganinki sai kina da bukata'
Fadin hakan yasa ta kasa magana. "
Yace Ina jinki"
Ta Ce,
"Da ma yaya zan tambayi zuwa bikin
'yar ajinmu ne".
鈥� Ta kai karshen zancen cikin faduwar gaba da zullumi.
Ya tsura mata ido kamar mai tuhumarta, yace,
"Wace ce " yar makarantarku?"
Ta zazzage ledar hannunta, ya bi cingam da katin da kuma kyallen da kallo. Ya sa hannu ya dauki katin ya karanta, sannan ya aje ya dauki kyallen,
"Wannan kuma fa?"
Ta ce,
"Kyallen anko ne'.?
Ya Ce,