← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don ta taya ta aiki. Ita ma Aliya 'yar wansu ce Amira tazo don ta taya ta aiki,. Haka kuma ita ma ta zo mata da

Dinkunanta, Shatima da ma shine ya kai musu kuma ya biya kamar yanda ya biya na Salma.

Salma sanye cikin riga da wando cikin irin kayan da ta siya gurin wata makociyarsu da ta kawo musu tallah. Sauran ba su siya ba, amma Salma ta zazza6a ta biya abinta.

Tana ta aikin namanta,

matsalarta cincin don gaskiya ba ta iya ba. Ga dai

kayan fulawa ya kawo musu kamar yanda Aliya da

Nafisa suka rubuta mishi, amma ba ta san yanda za ta

sarrafa shi ba. Ta san kuma in har ta tambayi Aliya baza ta fada mata gaskiya ba, Kila ma ta sa tayi Bata.

Bayan ta gama suyan naman ta nufi gurin Nafisa

domin ta jiyo tashin Kamshin cincin. Hamida ta samu a kicin din, ta ce, "Ke ce ma ki ke aikin?"

Nice sannu da zuwa

Salma tace Ina Anty?"

Hamida tace "Tana cikin dakin Yaya ta kulle kanta, wai ba ta son Kamshin cincin din nan'

Salma tace, "To fa! Ga shi nazi ta koya min yanda zan kwaba cincin da sauransu?*

Hamida tace, "Wai! Gaskiya da kyar in za tayi, don wannan ma ni na kwaba"

Salma tace, "To don Allah dan kwaba min".

Hamida tace,

"Da kamar wuya in miki, don aiki ya yi mini yawa. Sai dai ga wannan littafin na baki aronsa, zai taimaka miki gurin yin duk, irin cincin din da kike so

Salma ta amsa tare da godiya, sannan ta nufi sasanta.

Ranar idi da safe Salma ta dora abincinta na sallah da wuri, shinkafa fara ta dafa ta yi miyarta
tun jiya. Tana wanka tana ta sauri don kawarta Salma

Dankasa zata zo mata yau. Shatima ya gama shirinsa tsaf don dakin Nafisa yake. Ya kalli Nafisar tana zaune turus kan kujera tana cin nama, yace Wai ba zaki je sallar idi din bane?"

Ta ce "Ba zan je ba

Aliya ma ta ce ba za ta je ba aiki, Salma kuwa

yana shiga ya ce mata, "Zo mu je masallaci"

Babu damar musu tace to

Hijabi ta zura suka nufi motarsa, wai kuma halin kishi sai hakan ya bai wa Aliya haushi. Sun yo sallah cikin murna da farin ciki, suka nufo gida. A hanya ne take fada mishi zuwan Salma Kawarta. Ta ce,

"In da hali ya sai mata lemon roba. Ya ce jiya ya siyo

*lemuka, ya manta suna cikin but Din wannan motar hard脿 na kwali. In sun je gida zai ciro musu kowaccensu ta dauka.

Ta ce, "To mun gode".

Salma ta Ki yin kwalliya tana jiran sai Salma

Dankasa ta zo ta yi mata kwalliya, don ta iya sosai. Sha biyu da mintuna maigadi ya z0 kofar Salma ya ce tana da bakuwa mai suna Salma. Tare da maigadin suka nufi gate din, cikin doki Salma da Salma suka

rungume juna. Cikin murna suka shiga falon, Salma tace, "Ina su Anty in gaida su?"

Salma ta ce,"

"Suna sashensu, kun gaisa kafin ki wuce'

Ta shiga jera mata abinci da na sha, nama da kayan cincin. Sai da suka ci suka yi dam, sannan suka yi gaban madubi don a yi wa Salma kwalliya.

Tun kafin su gama Salma ta ga irin kyan da ta

Yi haka kuma Salma Dankasa take ta koda kwalliyar.

Salma tace, "Da bana kwalliya, amma yanzu zan koya ina yi wa kaina"

Salma da aka daura mata dankwali, ita da kanta take fadin ta hadu karshe.

Hotuna suka yi ta dauka kala-kala. Suna zama za su soma hira sai wayar Salma ta yi ruri. Da sauri ta daga ganin sunan Yaya a fuskar wayar. Ta ce, "Yaya?"

Ya ce, "Ki z0 ku gaisa da baki".

Tace.'

"A gurin Anty Nafisa?"

Ya ce, "Eh'Ta ce,

"To ga ni nan"

Ta kalli Salma Dankasa, "Zo mu je"

Ta ce, "Ina?"

Salma ta ce, "Ciki gurin su Anty sai ku gaisa da Yayana

Salma Dankasa ta yafa mayafinta sannan suka fita.

Tun kafin su shiga suka jiyo hayaniyar mutane a falon Nafisa, a ran Salma ta ce, to fa, ga shi ban ko

yafa mayafi ba. Suka shiga da sallama, Shatima ya

canza kaya daga yadin da ya saka suka je idi zuwa

shadda mai ruwan hoda mai duhu. Tana da matukar

tsada, ya yi matukar kyau, kanshi da aski yayi masa kyau. Salma a ranta ta ce su Yaya har da canza kaya? Ta shiga gurin su ta tsuguna tana gaida su.

Shatima ya cire gilashin idonsa yana kallon Salma, ya zaci ko gilashin idanunsa ne ya sa yake kallon salma ta dan kara girma, kuma ta yi kyau sosai. Sai kurum ya ji kishinta musamman da ba ta yafa mayafi ba.

Salma Dankasa ta gaida su. Ya dubi Salma,

"Wannan ce bakuwar?"

Salma ta ce, "Sunanta Salma Sadik Dankasa"

Ta kalli Salma, "Ga yayana"

Salma ta sake dubanshi tare da sake fadin,

"Sannu Yaya

Ya amsa tare da cewa,

"Kullum ina jin labarinki, yau mun hadu. Sannunki da zuwa"

Salma ta sake duban abokan su shida, da alama
akwai wadanda ba musulmi ba. Ta sake yi musu sannu.

Ta dubi gurin da Nafisa,ta ke zaune, ta ci kwalliya

Page 9

Ya dubi Salma,

"Wannan ce bakuwar?"

Salma ta ce, "Sunanta Salma Sadik Dankasa"

Ta kalli Salma, "Ga yayana"

Salma ta sake dubanshi tare da sake fadin,

"Sannu Yaya"Ya amsa tare da cewa,

"Kullum ina jin labarinki, yau mun hadu. Sannunki da zuwa"

Salma ta sake duban abokan su shida, da alama
akwai wadanda ba musulmi ba. Ta sake yi musu sannu.

Ta dubi gurin da Nafisa,ta ke zaune, ta ci kwalliya shadda mai ruwan jibi, ta yafa mayafinta kalar kayan. Ta kama hannun Salma ta ce,

"Zo ku gaisa da Antyna

Nafisa cikin jan aji ta gaisa da Salma, Salma ta

kalli Hamida wadda take kwashe kayan da su abokan na Shatima suka ci abinci, ta ce,

"Hamida ya sallah?

Kin yi kyau fa".

Hamida cikin "yar dariya ta ce,

"Na gode. Kema
kin yi kyau Salma, dube ki kamar amarya".

Suka saki dariya a tare. Ta dafa kafadar Salma Dankasa ta ce, "Ga kawata ita- ma Salma sunanta Hamida

tace,

"Sannunki fa, ni sunana

Hamida"

Salma Dankasa ta ce,

"Sannu, ya sallah?"

Salma ta ce,Lafiya

Shatima wanda idanunsa suke kansu suna burge
shi, yanda suka yi gaisuwar. Salma ta katse shi da fadin,

"Yaya zan iya tafiya?"Ya c猫,

"Eh, ku je abinku, da ma gaisuwa ce kawai"Ta dube su,

"Sai anjima, mun gode".

Wani daga ciki ya mika mata sabbin *yan dari biyu da dan yawa,

"Ga goron sallarmu".

Ta kalli Shatima tana fadin,

"Ku barshi kawai,
mun gode"

Wani daya cikin abokan yana fadin,

"Kina dai neman izimi n茅 a gurinsa kafin ki karba

Shatima ya yi dan murmushi,

"Ki karba, ai goron saliah ne*

Da hanna biyu Salma ta amshi kudin tare da rusunawa tqce

"An gode"

Ta nufi gurin Shatima ta nuna masa tare da cewa,Ka gani?'

Ya ce,Na gani, kin god'e"

Ta mika ma Nafisa

"Anty mu raba
Harara ta sakar ma Salma domin wannan kinibibin ya ishe ta, duk ta dauke hankalin Shatima ta kosa ta tita.

Shatima yace

芦Wannan naiki ne, ita ma sun bata"

Salma ta dafa kawarta tare da fadin,

"Mu je"Bayan ta dube su ta ce,

"Ku gaida gida"

Suna fita Salma Dankasa ta dubi Salma ta ce,

"Kawas wannan yayan naki ya hadu fa"

Kafin ta yi magana sai ta hango Aliya ta fito sanye da farin leshi doguwar riga, ta yafa mayafi shima fari. Salma ta ce,

"Sannu anty, ya sallah?"

Ta dube su a yatsine, ta ce,

"Lafiya"

Salma Dankasa ta ce,

"Wannan fa?"

"Duk matansa ne!"

Dankasa ta zaro ido tare da fadin,

"Salma Bash

da gaske ki ke yi? Har su nawa ne?"

Salma ta nuna dakin Amna,

"Ga dakin wata can ma ta tafi ummara

Salmar ta kai dubanta dakin sannan ta ce,

"Tabdi, kuma yaranshi nawa?"

Salma ta Ce,

"Ai auran bai shekara ba, duk kuma rana daya ya aure su

Salma ta zaro ido tare da fadin,

"Rana daya?"

Salma ta sa dariya,

"Kar ki sa ya jiyo mu, ki yi magana a hankali"

Ta ci gaba da fadin, "Rana daya wallahi"

Salma tace

"Tabdi, amma kun sha bidiri.wace.ce uwargida?" Salma ta ce, 'Wannan da ta wuce".

Dankasa ta ce, 'Tabdi,, ni mamaki ma naji, gashi gaye da shi. Ko da yake ni kaina zan yarda, in shiga jerin matansa da zai so ni

Salma ta dube ta da sauri,

"Da wasa ki ke?" Dankasa ta ce;

"Za ki min hanya?"

Salma ta ce, "Ba ruwana"鈩� Dankasa ta kai mata duka, tace Kina tsoron matansa ko? Don naga ba sa wani yinki"

Ta yi dariya,

*Ni dai ina yinsu".

Da suka koma daki suka ci gaba da hira: Salma ta kula Dankasa ta fi son a yi hirar Shatima, in kuma taci gaba da amsa: tambayoyinta akwai yiwuwar ta gane,ita ma matarsa ce don haka ta ce, "Ashe fasalin gininku iri daya ne da na matansa, wai ni uwa daya. uba dayas ku ke ne?"

Salma a ce, "Nice auta, kuma nan ya sa ni nake kula da nan din in zai yi mata ta hudu sai in koma gurin daya daga.cikin matan"Dankasa tace Iyayenku na raye? Wallahi ni nice

ba zan zauna ba, sam-sam. Ina son zama da mamana Salma ta ce, "Ni mun shaku da shine sosai, ba kin ga na nuna miki Mustapha da Badi'atu ba? Su ke binshi, amma da tazara tsakaninshi da

Mustapha Salma ta ce, "Mu canza labari, kin damu da batunsa"Ta kurbi lemun da ta dauka

"Saura kwana nawa mu koma makaranta?Dankasa tace

"Saura kwana tara Ta ci gaba da fadin,

"Ni ya min ne shi ya sa ko a dakin ina ta kallonsa, shi kuma sai ke yake kallo. Da muka shiga fa har da cire gilashin idonsa

Salma ta tashi ta nufi cikin daki, don ba ta son

zancen ya ci gaba.

Turaruka da kayan kwalliya ta dibar mata,
Chapter 6 · 0% Book details