← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce. "Ke dai bari duk na saka su aiki, ga shi yunwa ta ishe ni, kuma danwake nake son ci"

Amna ta ce Dole ki ji yunwa sha biyu fa ta gota Maman Afra tace, "Kin san mai house ya dawo jiya da yamma yanzun na dawo daga kai shi filin jirgi ya wuce Lagos"

Amna ta zaro ido,

"Kwana daya rak?" Maman Afra tace

"Don ni kadai ya zo,kuma na samar masa da nutsuwa ya tafi yana kewata Suka sa dariya, tace

"Maman Jafar a wannan zamanin mu fa ba a sanya, mata suna nan a waje birjik suna jiran wanda za su dafe mawa. Ke da mijinki kina kallo wata a waje tana mulkinsa.Domin yanzu mata ba sa jira a taya su,

Ta dauki danwaken tana fadin, "Mu je ciki

Maman Jafar, game da miji bana sanya, ban hada shi da kowa ba wallahi. Duk lokacin da ya z0 sai na bar masa wata alama wadda za ta sa in kasance a zuciyarsa kowane lokaci庐

Amna ta isa ta dafa kafadarta, *Tsaya Maman Afra, wace alama ce wannan? Ni fa dama matsala ce da ni

Ta dube ta, "Wace irin matsala ce? Kodayake mu karasa dakina

Ta kwala wa 'yar aikinta kira, "Haula!"

Yarinyar ta z0 da sauri, ta ce,

"Kawo min fulas din shayi da dafaffen kwai*

Kan gado Amna ta haye, don tace ba ra ta ci dan waken ba. Maman Afra ta zube kan kafet din Wai Maman Jafar wace matsala haka dake Amna tace

"Humm, mijinmu ne in muna tare kowane lokaci a hira da lokacin sirri sai ya dinga kira min sunan kishiya. Ko fa magana zai min sai kiji ya ce Nafisa, sannan yace au Amna? Maman Afra
abin yana damuna wallahi'

Maman Afra ta zaro ido,

"To ke kuma ki ka ce me?

Page 26

Amna ta ce, "in Na yi magana sai ya ce shi bai san ya ce ba, mantuwa ce

"Tabdi yarinya ta tsare muku Maman Jafar bacci ku ka yi ne haka! In fada miki ni nan ba ni da kishiya, amma na yi kishiyoyin waje. Da baban su Afra kwararren dan neman mata ne, ni ma farkon haduwarmu da haka ya zo na nuna mishi ni fa ina da tarbiyya, shine ya Billo da batun aure, da yake ina sonshi ban Qi ba na amince.

In fada miki anyi aure muna ta soyayya daga samun cikin Afra sai wulakanci ya shiga. Ai ko ya shiga neman matanshi har ba ya shakka in sani. Ina haihuwa Yayata ta hadi ni da wata mai saida maganin mata a Kaduna. Kafin in yi arba'in ta yi min gyara tare da shawarwari yanda ya kamata.Ranar ko da ya dawo ban da tona sirrin aure babu kyau da na ba ki labarin yanda muka kwashe kin sha dariya.

Mutum ya koma tamkar soko, ko inCe bawana, Ni ina sonsa tsakani da Allah haka bai sa na wulakanta shi ba. Cikin hikima dubara da addu'a Allah ya taimake ni ya bar duk wata macen waje,sannan in na yi magana yana karba, duk abin da nace ina so in yana da hali yana mana. Daraja da Kimata ta dawo idanunsa, Ke shawararsa wadda ba ta shafe ni ba ma sai ya kawo min ita. Ni ko in ba shi iya fahimta ta sakamakon ina karance-karance littafan Hausa ina samun kaifin basira"Amna ta tabe baki

"Ni fa duk wannan karance-karancen na Hausa bana yin su, gara English Novel, sannan wadannan abubuwan ban yarda da su ba. Ga likitoci kullum suna gargadin shaye-shaye da matse-matsen nan"

Maman Afra ta ce,

"Ina mamakin irinku"yan gayu masu karatun al'adun wasu ku bar naku.

Hikima da basira ai tanaga marubutanmu cikin hikima da basira, kuma kin san wannan matsalar da ki ke fad矛 da kina karatun da tuni kin magance ta batare da kowa ya sani ba kuma game da kayan gyaran jikin nan, sai dai in ba ki nemi ingantattu ba kuma basu baki shawara daga masu saida kayan ba. Kin san cewa ni ma na yi irin abin da ki ka yi?"Amna ta tabe baki,

"Ni fa ban iya wannan aikin, ko da aurena ban sha sosai ba, ko yanzu na fi ga dan irin na waje din nan Maman Afra ta ce,Ai wannan ba su zama a jiki in za ki dawo hanya ki dawo kawai"

Amna ta ce,Mu bar wannan zancen, ni muyi wanda nike miki

Maman Afra ta ce,

"Mun bari. Amma in kin canza shawara kina iya tuntuba ta zan kuma hada ki da ita. Don kullum ina fada ma mata sai sun gyara zasu ga daidai Amna ta ce,

"Yanzun ni ya zan magance wannan matsalar, yanzu haka fa ita tana Abuja gaba daya mu sai dai ya zo ya yi mana kwana daidai don ita Karamarmu ma da yake ya maida ta sakara, sai yayi zuwa ka ga bai kwana gurinta ba

Maman Afra ta sheke da dariya tareda fadin,

"Lallai na jinjina ma wanna Nafisar, har ta burgeni" Amna ta ce

"To mene ne abin dariya a nan.

Maimakon ki taya ni bakin ciki miji yana tare da ni,kuma yana ambatar kishiya. Akwai ranar da har kuka na yi saboda kiran sunan Nafisan, na yi wai sai ya ce min wai sun yi fada ne shine abin yake ransa

Maman Afra ta sake shekewa da dariya har da kwalla. Amna ta mike za ta tafi tana fadin,

"Tunda abin dariya ne bari kawai in tafi"

". Ta yi maganar cikin fushi.

Maman Afra ta riko ta,

"Tsaya ki ji kawata,

rainin hankalin da namiji nike yi wa dariya. Ya rasa lokacin da zai tuna sun yi fada da ita sai irin wannan lokacin mai tsada a gurinki?"

Maman Afra ta dafa kafadar Amna,

"Yi tunani da kyau ki gani. Yarinar nan tana matukar gyara jikinta, inda za ki tambayi sauran kishiyoyinki

Kila su ma yana kiran sunanta a gurinsu. Ai bai san lokacin da zai yi barin ba

Amna ta ce,

"Kin ganta ne, busasshiya. Na fita komai fa! Har na fara zargin ko ta yi masa asiri ne" ta ce,

"Ba wani asiri in fada miki isassun mata yanzun ba sa zuwa gurin bokaye, kayan gyara suke siya suna gyara jikinsu, ki ga mace birtintin amma ta isa' a gurin miji, kuma ita ma har bushewarta ta fi ku a idonshi. Shawara ta daya ku dage kawai ki gyara, amma fa tushi babu inda zai kaiki"

Ita dai Amna har ta tafi ba ta gamsu ba. Cikin dare nakuda ta kama Aliya, ranar asabar ce Shatima yana dakin Amna, Aliyar ta yi ta kiran layinshi ba a daga ba. Haka ma layin Amna tayi ta kira, wayoyin duk suna falo su kuma suna cikin daki, sam ba su ji kiran ba. Karfe biyar na asubahi Aliya ta haifo danta santalele shi ma mai kama da

Babansa. Cikin bacci Shatima ya yi mafarki wai Aliya ta haihu. Da sauri ya farka, falo ya nufa ya ciro wayarsa a caji da nufin kiranta tunda likita yace lallai tana fara nakuda a kai ta asibiti, domin ta gota lokacin da ake saka ran za ta haihu. Adadin kiran daya gani nata a wayarsa shine ya sa shi ficewa daga dakin babu shiri, ya nufi sashen Aliyar, Ya same ta tana numfarfashi a gefe ga da yana ta tsala kuka. Da alama ba ta jima da haihuwar ba. Ya kai hannu ya kama ta tare da fadin, "Tashi"Ta ce.

"Ka bani reza a cikin can in fara yanke mishi cibiya"

Ya dubo ya ba ta, ta yanke cibin, sannan ta ce ya ba ta zani. Ta nannade yaron, sannan ta ce ya kwantar da shi. Ta ce ya taimaka mata ta shiga wanka. Ya tara mata ruwan zafi ta shiga wanka, layin Amna ya kira da wayar Aliya, ba ta daga ba ya

Nufi dakin da sauri ya tashe ta, ya fada mata haihuwar Aliya.Juyi ta yi tare da fadin, Allah ya raya Ta maida kai ta kwanta.

Yace Ki tashi ki taimaka mata' Amna ta ce, "Me ni gaskiya ba zan iya zuwa wani taimako ba Ya ce, "Ita kadai fa ta haihuTa ce, "Ina asibiti ne Can ya kamata ka kai ta Ya nufi dakin Salma da sauri, ya taso ta, yace ta zo ta taimaka wa Aliya. Suna shiga suka samu掳 Aliyar zaune tana goge jiki, ta fito wanka. Salma ta ce, "Sannu Anty Ya nuna mata gurin jinin, "Ki gyara nan Salma ta nufi gurin zuciyarta ta tashi, amma haka ta daure ta kwashe ta kulle uwar a ledar da Aliyar ta ce ta dauko a store, ta goge ko ina tsaf da Detol sannan ta fesa turaren daki; ta koma dakinta zuciyarta a tashe, ta shiga ta yi wanka, sannan ta yi sallah,"Da safe Shatima ya dauki maijego da danta ya kai su asibiti don likita ya duba lafiyarsu. A ranar dangin Aliya suka cika gidan daga Zaria, Amna sai da ta tashi fita zuwa shago sannan ta shiga don yi wa

'Aliya barka. Kusan tunda take a gidan wannan ne karo na farko da ta shiga gurin Aliya, gara ma gurin

Page 27

Salma ta shiga lokacin da aka z0 daukan gadonta da Shatima ya taba ajewa a daya daga cikin dakunan Salma.

Aliya ta ce ma matar yayanta su yim脿

Shatima magana su tafi da ita Zaria tunda shi ba ya nan, yana Abuja, babu kuma wanda zai taya ta aiki. Shatima bai musa ba domin shi ma hakan zai fi masa sauki, don Salma ba za ta iya yi mata aiki ba, saboda aikin jini da ta yi sai da ta yi ta amai, har sai da ya amso mata magani, Don haka zuwa yamma ya kai suda wasu yan uwanta. Washegari kuma ya koma inda ya kai su

Alhajinsa, nan kuwa aka yi wa yaron huduba da sunan wani Kanin su Alhaji da ya rasu, ubansu daya, Aminu.

Shatima ya bada duk abin da ya san zai bada duk da za su zo suna shi da Nafisa, ita ma Hajiya tayi kayan barka kamar yanda ta yi ma sauran.
Chapter 19 · 0% Book details