← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka nan in ka ganta tana tsalle-tsallenta sam ba za ka ce tana da aure ba. Salma da ma yarinya ce, sannan ga ta da son wasa, shi ya sa kawancensu ya dace da Salma Sadik. Suna cikin group din Kwallon tebur da kuma rawa irin ta makaranta. Wani lokacin ma wayarta ta

kan kunna a gida tana cashe rawarta.

Yau Shatima dakin Salma yake. Dafadukan taliya ta yi, ta zubo masa don ta lura yanzun yana cin abincinta, tunda aka yi wannan hayaniyar.

Ta aje a gefensa yana zaune kan kujera yana aiki da laptop. Ta

koma ciki tana atisayen rawar da za su yi gobe in sun je makaranta. Ya kwalla kiranta.

Ta fito ta durkusawa a gabanshi, ya ce,

"Wai ke duk lokacin da zan shigo sai in ji kina jin wannan sautin, ina ki ka samo shi?"

Ta ce, "Muna amfani da shine a club dinmu na rawa"

Ya kware da abincin da ke bakinshi, nan ya shiga tari.

Salma ta ce, "Ya salam!"

Ta tsiyaya ruwa a kofi ta mika masa. Ya amsa

ya shanye, ya ajiye kofin sannan ta dube ta murya a shake ya ce, "Rawa? A wane club kuma?"Ta ce,

"Yaya na makaranta ne, an ce mutum ya zaba ko rawa ko waka Ya ce,

"Kina manta cewa kina da aure ko?"

Ta ce,

"Ban manta ba". Ta sunkuyar da kai.

Ya ce,Gaban maza ku ke rawa ko?" Ta ce,

'A'a Ya ce,

"To kar dai ki sake in ji an ce kin shiga gasar rawa, balle a zo ana yinta a gaban mutane

Ta ce, "Ba zan yi ba, jibi ma za a yi mana hutu' Ya ce,Shi kenan.

. Yauwa Badi'atu ke ta damuna wai dinkin anko wane kala za a yi miki? Na ce in na dawo zan neme ta. Bari in kira miki ita"

Salma ta ce,

"Mun yi waya dazun Yaya, da ma wai ba ta same ni ba ne ta kira ka. Nida zaka barni inje Zaria din da na kai wadansu kayan

Ya ce,

"A'a sai biki za ki je gaskiya

Ta ce,Allah sarki Yaya, kayana sun sha ruwa wadanda aka dinka min"

Ya ce,Yau saura kwana goma sha daya bikin,zan je ranar asabar sai ki ba ni sako Ta ce,

*Badi'atu za a bai wa, zan amshi wasu style a hannun Salma Sadik"

Ya dago ya dube ta,

"To wa zai biya kudin dinkin?"

Ta yi murmushi,

"Ni zan biya kayana

Ya tattara hankalinsa a kanta,

"Ina ki ka samu kudi?"Ta ce,

"Wanda nike tarawa.Ya yi murmushi, "Kawo su mu gani, sun kai) dubu goma?"

Ta yi dariya tare da nufar daki. Ledar da ake

saka zanin gado ta dauko ta zo gabanshi, ta juye kudin a Kasa. Mamaki ya kama shi, ya ce, "Wannan duk sune?"Ta ce, "Sune mana"

Ya ce,Lallai kudi wawaye ne, sun, kai nawa Yanzu tace

, "Sai dai a kirga a gani".

Ya dauki yan dari biyar, bari in hada wadannan, ke kuma ki hada sauran

"Bari in hada

Ta soma hadawa tana cewa,

Kila su kai irin dubu talatin din nan

Sun gama lissafi abin da yaba su mamaki, sai ga kudi dubu dari da biyar har da naira sittin. Salma tace, "Kudina ne kadai kuwa?"

Ya ce, "Ana ba ki ajiya ne?"

Ta ce, "A'a, ni dai to ko aljanu suna saka by Mistake?

Ya yi dariya, "Kin dauki watanni kina tara su'

Ya dube ta, "Ni ma za ki ba ni aron dubu hamsin

Ta ce, "a,a dai a raba zan dai ba ka kyauta.

Toni ban ma san ya zan yi da su ba. Ka amsa duka

mana?"Ya ce, "A'a ba zan amsa ba, ai kudinki ne"Y脿 Kirgi hamsin, "Wannan ma na ara ne, zan baki insha Allah".

Tace Ni dai bar maka na yi gaskiya
Shi ma ya sake cewa,

"A'a zan ba ki su.

wadannan kuma in kin je gida sai ku yi shawara da su

Inna, ki yi yanda ki ke so"

Ran'- da za su tafi Zaria ita ce ranar farko da

dukkansu za su je gidansu, don haka duk suna cikin murma da doki sunje wajen shiga mota nan ne akadanyi wasan kwaikwayo nafisa da aliya duk sunata harin gaban mota salma tana ganin haka sai tayima kanta mazauni a baya

Aliya da yake ta fi Nafisar lafiya sai ta yi maza ta fada gaban. Nafisa ta kama kugu ciki

ya yo gaba, ta ce, "Ni ce zan zauna a gaban mota, don nice da girki"

Aliya ta kalle ta, da dan murmushi,

"Ai gaba mazaunin babba ne"

Shatima ya riske su cikin wannan musun, don ya je gurin Baba maigadi ya sallame shi da abin da zai rike kansa kafin su dawo. Ya kalli Nafisa da ke tsaye,ya ce,

"Kina nufin sai na zo za ki shiga?"Cikin dan wasa ya yi maganar.

Ta ce, "Ni gaba zan zauna .

Ya kalli gahan, Aliya ce a ciki, ya ce, "To ki shiga baya tunda ta riga ta zauna"

Nafisa ta ce,

"Oho, da ma kai ne ka ce gaban mota na uwargida ne?"

Aliyar ta yi *yar dariyar kissa,

"Da ke sai ki bar babba a baya?"

Shatima ya ja tsaki, wai har shiga motar ma sai an yi masa wata ka'ida? Aliya ta ce, "Shi ne na gani"

". Cikin 'yar dariya ta yi maganar.?

"Maimakon ki shiga baya ga ciki inda za ki sake abinki" Nafisa ta koma baya ta coge, tare da dafe ciki,

ta ce, "Sai dai ko a bude but din a fito min da kayana,don kuwa babu dole sai na je a cikin motarsa'

Kar in sake in ji kin bi motar haya. Inba za ki shigo ba, to ki koma ciki ki bude dakinki ki shiga

Ta tura baki, "Ai dai ka san wanna bikin dole in je shi. Domin yanda ka ke jin cewa 'yan uwanka ne za su yi aure, haka ni ma 'yan uwana ne"

Page 5

Ya ce,

"To za kiyi min rashin kunya ne ko zaKi fada min magana ne?"Ta yi shiru tana rike da Kugu.

Ya koma ya zauna, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya soma magana da Aliya, "Yi hakuri ki koma bayan"

Aliya ba ta so haka ba, amma sai ta wayance ta bude Kofar tana fadin, "Zo ki shiga ba don halinki ba,

kuma kar ki sake ki takura min yaro na fada miki"Nafisa ta shige tana zumbura baki. Salma duk tana jinsu, ita neman layin kawarta Salma Sadik takeyi. Aliya cikin son daba ma Nafisa magana tace, "Ke baki fadan shiga gaban motar? Da yake yanzun Salma ta Gama sanin wace ce Aliya sai ta tabe baki, tace,

"Anty ai ni gaban motar Yaya in da gundira ya kamata ya gundure ni. Kullum sai na hau zuwa makaranta"

Aliya ta tabe baki ba ta sake magana ba.

Suna hawa babban titi layin Salma ya shiga.Kuka suka soma shirmansu, "Hi kawata ya ki ke?"Ta ce,

"Ya ki ke Kawas? Gamu za mu je Zaria din Tace Haba ki ce yau sai City?"

Salma ta ce Ga mu a hanya, in na dawo zan Zo in kawo miki kayanki"

Salma ta ce,

"Ke din ce zaki zo? Lallai

Salma ta ce,

"Allah zan z0. Zan roki yayana ya

barni inz0 ko ya kawo ni in maido miki style dinki dana ara kin ga mun yi hutu, kuma za a shiga azumi Salma Sadik ta ce "Ki bari dai zan z0 miki da sallah

Salma tace "Za mu sake zuwa Zaria da sallah,

amma duk da haka zan jira ki".

Ta ce, "Shi kenan". Suka yi sallama.

Shatima yace, "Ina za ku je yawon sallah din?"

Salma ta ce, "Uhm

Ya ce"Na san kin ji ni",

'Ta ce, "Zaria mana da sallah fa"

Ya ce, "A'a ba za ku z0 ba, kun je daf da azumi sannan ku je da sallah:"

Ta yi shiru. Aliya da Nafisa har suna hada baki gurin cewa, "Haba dai, sallah guda!"?"

Ya ce, "Au kuma kuna son zuwa ne?"

Aliya ta ce, "Haba my love, sallah lokacin ziyara ne Ya ce,

"To ni dai ba dinkin sallah zan samu damar yi muku ba, don akwai abubuwa a gabana"

Aliya ta ce, "My love ta ya ya ma za mu ce maka sai ka yi mana kaya, ga' zannuwan nan na lefenmu za mu dinka".

Nafisa ta ce

-Ni kam zanyi da ace tun muna gida aka yi wannan zancen da na zo da kayana na bada dinki".

Shatima ya ce,

芦Wannan ai mai sauki ne, in zan sake shigowa Zaria zan z0 miki da shi"

Ya kai hannunshi daya ya shafi cikin Nafisa tare da fadin,

"Ke kuma wa yace miki kwalliya ba tayi miki kyau?"

Cikin shagwabar da ta san yana so, ta ce, " In jika mana

Ya maida kanshi titi, "Kin ma san me ye? Ai kin ma fi kyau a haka. Ina kallonki da dan yarona

'Ta ce, "Ni nace maka yarinya ce fa"

Ya ce, "Ai ni na yarda da batun likitan, duk da

shi ba Allah ba ne. Amma Allah ya ba shi ilimi a kan haka

Aliya bakin ciki ya hana ta magana; sai da

Shatima ya ce,

"My love wannan layinku ne, hoto ya
nuna namiji amma tana musu".

Ta yi dariyar yake, "Ai kin dai ji an ce namiji ne to hakan ne"

Nafisa ta ce, "Ni dai Allah ya ba ni mace ba zan daina wannan addu'ar ba

Aliya ta ce, "Ki dai roki alkhair kawai".

Yace, "Abin da ya fi kamata ma kenan

Sun isa Zaria cikin tukin da yake na nutsuwa da

kwanciyar hankali. Kai tsaye gidan su Hajiyarshi ya nufa da su.

Ta sa an gyara gurin bakin ta dauka har da

Amna za azo ta sa an yi girki na alfarma da kaji. Tafito da fara 'a tana fadin, "Sannunku.

鈥� sannunku"Ta dube su, "Ina Amna?"

Shi ma wanda ke kokarin fita ya ce,

"Sun je umra

Hajiya tace

"Masha Allah, Allah ya dawo mana da ita lafiya

Sannan ta kalli salma

"Kowa ya nemi gidan uwarsa in- yana da shi, tunda dai ku ba baki ba ne, dama na sa an gyara sasan ne saboda Amna, don nice uwarta ta Zaria

Shatima yaCe,
Chapter 3 · 0% Book details