Sashe 23
Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Aliya ta sabi danta wanda suke kira da Abulkhairi ta nufi akin Salma. Ta same ta zaune tana. cin tuwo, ta yi sallama, Salma ta dube ta a wulakance, sannan ta amsa. Aliya cikin mamaki ta kalli Salma, ta daure tace
'"Baban Abulkhairi yace ki daga waya yana ta kiranki, ko kin yar da wayar ne'?"
Salma ta dube ta cikin son jin Karin bayani,
"Waye kuma Baban Abulkhairi?"
Aliya tace, "Tofa! Yau kuma har mijin naki ba ki. sanshi ba?"
Salma ta saki *yar dariya irin ta rainin wayo,sannan ta ce,
"Baban Jafar, Baban Ashraf, Baban Abdul wa kikace ma?"
Aliya ta ce,Kai yau wata rashin kunya ki ke ji ne haka? To ko Baban wa aka ce an ce don ya haifa ne. kuma ke ma da kin haifa na san sai kin ce baban wane. Tunda kuwa ba a da da sai a bari masu ya' ya matansa mu yi"Salma taCe,
Tofa! Har dasu gorin haihuwa?"
Ta saki dariya, har da "yar shewa. Aliya ta ce,
"An yi miki, in fitsari banza ne kaza ta yi mana"
Salma cikin fusata tace, "Ni don Allah ki je kin sa tuwona ya huce ina surutu".
Aliya tace
"To da ma mijinki ya ja min wanna rashin kunyar da ki ka yi min, don shi ya turo ni" Salma tace
"Ki fada masa ba ni da lokacin daga wayarsa" Ta dago wayarta daidai lokacin da kiran ya Kara shigowa,
"Gashi nan ya sake kira banji dagawa ba
Ta maida wayar ta aje. Aliya ta zaro ido tana kallon Salma, ta mike ta dauki robar tuwon ta nufi kicin tana cewa, "Ki je ki fada masa sakona, don nasan ko ban ce ki fada ba kai tsegumi aikinki ne Aliya ta juya cikin tsananin mamaki, jiki har Bari yake, ta kira Shatima tana fada mishi wai Salma ta zage ta tas! Har da kuka, kuma ta ce ba ta da lokacin daga wayarsa.Shatima ya cika da mamaki, ba don Aliya ta fada mishi da, ba zai yarda ba. Duk da haka sai yana tantama, don haka sai ya tura mata sako kamar haka.Kin ce ba za ki daga sakona ba a kan me?Sai Salma ta tura masa amsa kamar haka.Haka na fada'. Ta tura mishi.
Mamaki da tsoro suka dirar ma Shatima, ji yake tamkar ya kulle ido ya bude ya ganshi a Kaduna. Ya soma lissafin ranaku, kwana uku ya yi masa nisa. da ya zo gida bai iya daurewa ba yana fada ma Nafisa wai Salma ce ta yi kaza da kaza.Dariya Nafisa ta saki tare da cewa,Ai dama
_karshen alewa Kasa, kuma dama tunda kace ta je jami'a ai dole idonta ya bude" yace ni kuma nafi tunanin ko aljanu ne suka shigeta nafisa tace aljanun iskanci ba Ranar juma'a Salma ba ta je makaranta ba ta bari ne sai in ta koma Zaria. Kayanta ta ke ta linki tana. loda su cikin akwati, ta kalli lodin kananan kayanta wadanda ta dinga siya tana sakawa lokula da dama in Shatima yana dakinta. Ashe ita aikin banza take yi? Ta girgiza kai tare da fadin, "Humm Allah
Ya dawo da mutumin nan lafiya ya sha mamakina Takwas da mintuna na safiyar juma' a Safwan yana kwance kan gadonsa kamar ba shi ne zaibi jirgin karfe tara zuwa Abuja ba. Din yanada sabgogi da yawa kuma yanason ya ga Shatima.
Ya kai hannu ya dauki wayarshi da nufin ya sanar da Shatiman cewa, yau fa zai shigo Abuja, kuma yanason in zai zo a kan son ganinshi da Shatima ya ce yana yi, sai dai kuma yana dauko wayar bai dire ko ina ba, sai kan rubutun Salma. Duk kwanakin nan matsawar ya dauki wannan wayar, tofa sai karanta rubutun Salma kafin ya yi abin da zai yi. kuma fa ba wai yana farin ciki da zantukan nata bane, domin ya gama nazarinsu kaf babu so a zantukan illa haushin mijinta da ta ji sakamakon abin da ya ce a kanta. Kuma hanyar da ta biyo don yin bore ga mijinta ba za ta bayar da masalahar da ake so ba, illa ma a samu matsala in ba a yi sa'a ba rikicin ya shafi dangi. In ya yi tunanin rubuta mata sakon dakatar da ita ta bari har sai lokacin da ta gama karatun kamar yanda y盲 ce, sai kuma ya fasa in ya tuna da gargadin da ta masa cewa ba zasu sake ji daga juna ba har saita zama ba matar Shatima ba.
Agogon dakin ya buga tara, da sauri Safwan ya danna kiran Shatima. Ya dauka sun gaisa, sannan Safwan ya fada masa cewa zai shigo Abuja, kuma zai zo don ya ji neman da yake yi masa. "Ya ce, to shi ma dai yau zai tafi Kaduna don wancan satin bai je ba. Safwan ya ce, to ya jira shi sai su dawo tare.
Karfe uku da rabi daidai Safwan suka isa gidan Shatima, inda Shatiman ya je ya dauko shi.Nan suka ci abinci har ya yi wa su Ashraf kyautar kudi. Suna cin abinci Shatima ke fada masa bukatarsa ta son gwada kasuwanci.
Safwan yace,
"Gaskiya kayi tunani.kasuwanci yana sama da duk wani aiki a gurina, ko don da shi na bude ido?"
Shatima ya ce,
"Haka ne, ba wai don ka bude ido da shi ba, haka batun yake. A rana sai ka ci ribar albashin wani na wata daya Safwan ya sa dariya, ya ce,
"'Na wata kadai. na shekaru ma Sun tattauna sosai. inda Safwan ya ba
'Shatima shawarar ya shiga harkar man fetur, ya ce,amma jarin naira miliyan goma sun yi kadan saidai ya zuba kar ya waiwaye su yanzu a yi kamar shekara. Shatima ya gamsu da duk shawarwarin da Safwan ya ba shi Sun nufo Kaduna tare shi da Shatima,
zuciyar Shatima tam da tambayoyi a kan Salma.Ita kuwa Salma zaman jiran zuwan Shatima take yi, don ta hada kayan sawarta gaba daya gadonta ta jingine, ta tattara kujerunta gefe guda ta
Zuba kayan kicin dinta a buhu ta daure, ta tara komai a falo, sannan ta ci uban kuka idanunta sun kumbura suntum! Muryarta ta dashe, sai dai ita baza ta ce ga dalilin kukan nata ba. * Shatima bai san dalili ba, yana shigowa gidan ya ji wata mummunar faduwar gaba.
Idanunsa suka dira kan dakin Salma, dakin a bude yake a wangame. Kai tsaye can ya nufa da kayan da yake dauke da su a hannuwanshi. Baki ya saki ganin babu labulan a kofar, ya karasa falon nan ya yi turus! Ya zube kayan da ke hannuwanshi ya shiga cikin falon tsibi-tsibin kayan yake bi da kallo.Ya yi karfin halin kwala mata kira,
"Salma! Salma!!"
Ba ta amsa ba, sai dai ta fito daga cikin
dakin tana rataye da jaka da kuma akwatin da za ta iya dauka tana janshi. Ya kalle ta tare da fadin,Lafiya?"
Harara ta watso mishi da jajayen idanunta,
"Lafiya ka ke tambaya? To ita ta kawo haka, ba don ina jiran takardar saki ba da babu abin da zai saka tarar dani a gidan nan yanzu kam ka bani takarda ta don bazan sake kwana a cikinshi ba Ta daga murya shatima ka sakeniiiii
Mu hadu a littafi na hudu kuma na karshe
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*