← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"'Maimakon a sako zanin sai a sako

kyalle?"Ta ce,Sun saka ne in mutum ba zai saya a hannunsu ba sai ya yi amfani da wannan kyallen'

Ya ce,Nawa suke saidawa?"Ta ce,

"Dubu uku ne yace

"Ina ne ake saidawa

' Ta ce,

"A sabon Kawo ne gidan su amaryar

Ya ce, "To su kawo miki amma a cikin bashi da kike bina zan sai miki"Ta tsura mishi ido, "Wane bashi?"

Ya ce, "Dubunki hamsin da na ara, ai ban manta ba Salma ta CE,

"Yaya tun a ranar na fada maka ba bashi ba ne, baka fa na yi"

Ya ce,

"Ni ma tun a ranar na fada miki cewa ba shine. ki kira su kawo miki zanin

Ta ce, "Ba ni da waya, ta lalace

Ya tura mata karamar wayarsa,

"In kina da lambarta kira

Salma tana ta mamakin yayan nata a yau. Ta juya bayan katin inda ta sa Habibar ta rubuta mata lambarta, ta ce,Yauwa, ga lambar

Ta sa lambobin ta kira, babu kati, ta dube shi,

"Babu kati a wanna layin Ya turo mata katuwar,Kira da wannan

Ta dauki wayar cikin tsoro tana juya ta, ba ta san ina za ta shafa ta kawo ba.

Ya kalle ta,Shafa tsakiyar"

Tana shafawa wayar ta kawo. Hoton Ashraf da

Junior da Shahid ne. Ta tsura ma yaran ido. Ba ta san a fili ta ce,

"Suna kama". Ba sai da ta ji ya ce, "Duk ni suka biyo Ta yin murmushi, sannan ta soma saka lambobin.

- Habiba ta daga, Salma ta ce, "Ni ce Salma Bash"Habiba ta ce, "Oho, ya ki ke?"

Suka gaisa, ta ce,

"Ina son anko guda daya, su Salma Dan kasa sun amshi nasu?"

Ta ce,

"Gobe da safe, za ta zo ta amsa".

Salma ta ce,

"Ki bata nawa ki ce ta bada a yi mana dinki iri daya da nata

Page 20

Ta ce, "Zan ba ta, ba za kisai na dinner ba?"Salma ta ce, "Dinner kuma?"

Ta kalli Shatima, "Kuma karfe nawa ce dinner Din Habiba ta ce, "Karfe tara dai za a tafi".

Salma ta ce, "Wai! Ba za a bar ni ba. Ki dai ba ta atamfar sai ki z0 ki amshi kudin".

Ya ce, "Ko ta turo account dinta" Salma ta ce, "To ki turo account dinki zan tura da kudin dinki don Allah ki ba Salma"

Ta ce, "Zan ba ta"." Suka yi sallama, Shatima ya kalle ta, "To me za ki je mata tunda Dinner ta yi dare?"

Ta ce,Kamu za ni"

Ya ce,Har da maza?"

"A'a ban da maza".

"Shi kenan"Har za ta mike, sai ta ce,

"Ina son ma nayi magana da Anty Badi'atu"

Ya kalle ta, "Kina son cinye kudin cikin wayata ko?"Ta girgiza kai, tare da yunkurin mikewa.

Ya ce, Kira ta dai minti biyu za ku yi".

Salma ta yi murmushi, sannan ta soma saka Lambar Badi atu. Sai sunanta ya fito ya saka mata sister. Ta daga tare da fadin,

Yaya Salma ta ce, "Na'am Badi"atu tayi dariya,Salma ya ki ke?"

Ta ce, Lafiya lau, da ma kwana biyu ba mu gaisa ba. Bikinki saura kwana sha tara ko?"Badi' atu ta ce,Au kina ma tambaya ne?" Nan

Salma ta sa dariya,

"Ina dai son in kara tabbatarwa ne"Badi' atu ta ce,

"To saura sati biki za ki z0?"

Salma ta ce, "Sosai ma tun saura sati daya zan zo Zaria tare za mu raba kati"

Hira ta yi wa Salma dadi har da zama dirshan kamar ma ta manta cewa a waya take magana, kuma ta manta da aron wayar ta yi, ta manta da mai wayar a kusa da ita, suna ta tsara yanda shagalin zai kayatar.

Shatima shiru ya yi yana kallon Salma komai in tana yi burge shi take yi. Bai taba ganin tana hira haka cikin sakin jiki ba, ya kasa katse ta sai kallonta kawai yake yi. Har sai da ta ji daga ciki an soma gargadin saura minti daya kudin su Kare. Da sauri ta dube shi tare da ciro wayar a kunnenta ta katse, sannan ta ce,

"Yi hakuri Yaya Sai ta ga ya yi murmushi,

"Kin manta kina waya ne ko? Kati fa na zuba ba wai bonanza ba ce" Da hannu biyu ta mika mishi wayar tare da sake maimaita,"

"Yi hakuri"

Ya dubi gefen katifarsa, ta gane nufinsa ta aje masa a gurin, don haka ta aje ta mike cikin sauri ta fita.

Ya bi ta da kallo.

Ranar kamu ta kama alhamis, karfe biyar aka rubuta a jikin katin. Salma ta so bari sai karfe shida saboda sanin wannan mummunar al'adar ta African time, amma kuma ta san in ta kai shidan nan Shatima
zai iya dawowa, kuma zai iya hanata tunda ya san ya bata kudin motarta dubu daya, kuma yana zaton tunda rana za ta tafi biyar da rabi ta gama kwalliyarta,ta yi kyau cikin anko, dauri mai hawa-hawa ta yi don yanzun ta kware sosai grin tsantsara kwalliya da kuma daurin dankwali. Takalmi mai tsini ta saka,mayafi da 'yar poss dinta mai igiyar chain. Sun dace da atamfar, _ tana kulle kofar dakinta, Shatima yana shigowa. Har zai wuce-sai kuma ya tsaya, ta nufo shi bayan ta gama rufe Kofar ta rusuna,

"Yaya sannu da dawowa 鈥� Ya daure fuska,

*"Kina nufin cewa yanzu za ki tafi?禄 Gabanta ya fad矛, ta ce,Ai Yaya da yamma ake

Yin kamu fa".Kina nufin titi za ki tafi yanzu a haka ki hau mota?"

Ta ce, "Ai dole mota sai a titi" sai Ya je ya yi baya da mota ya juya, daidai ita ya tsaya sannan ya ce, "Shigo in kai ki"

Ya kalli fuskarta bayan ya miki layin nasu don zuwa titin, yace Da haka za ki biyo ta nan da wannan shafe-shafen? Dubi maza cike a nan Ta yi shiru. Suna shiga sabon Kawo ya ce,

"To inane gidan?"Ta zaro ido,

"Lah na manta in z0 da katin saboda duba adress . Ya rage tafiya yace

"Au da ma haka za ki zo Kiyita garari a layi Ta ce, "Wallahi yaya na manta katin ne

Ya nuna wayarshi a caji,

"To dauki waya

Ta ciro wayar cikin murnar ta samu madita sai kuma ta yi turus da ta tuna ai a bayan katin na rubuta lambar Habiba. Shatima ya ja tsaki tare da fadin,

"Ki hakura da bikin bari mu juya gida .Cikin sauri ta CE, Bari in kira Salma Dankasa, har ta sare saboda Salmar ba ta daga ba,domin wannan ne kashi na biyar da ta kira Salma amma ba ta daga ba. Gab da tsinkewar kira na shida,sannan Salma ta daga, Salma cikin fushi ta ce ma Dankasa,

"Banza kawai mara aji, ina ki ka aje wayar?"Ta ce,

"Salma Bash, Allah ban san ke ba ce.

Wayar tana hannuna na zaci wani ne da yake ta damuna, naqi dagawa a zatona shine ya canza lamba"Salma ta ce,

'Kuna ina ne yanzu mun shigo Sabon Kawo, ga shi ba mu san adireshin ba"

Salma tace,

"Ga amarya ta yi muku

'kwatancen inda muke tare za mu tafi da ita'

Habiba ta yi musu kwatance, ashe ma suna kusa da gidan, ta ce, "To Salma Dankasa ta fito mu ganta a waje

Daidai gate din suka samu Salma, ita ma ta yi kyau cikin anko, ta sha kwalliya. Ta zo da sauri ta gaida yaya, Salma za ta fita ya ce,

"Kar ki kai magriba Ta ce,

"Yaya yanzun fa karfe shida, kuma Karfe bakwai saura ake yin magariba, ga shi kuma ko ramarya ba a dauka ba".

Ya ce, "To yanzu karfe nawa ki ke nufin za ki dawo?"Tace Sai dai mun je ko ba a tashi ba ni sai in dawo Wannan shi ne karo na farko da za kiJe biki. To ki sani ana wanke tukunya don gobe ne" Salma tace

"Insha, Allahu zan dawo da wuri".

Ihu suka saki lokacin da suka hadu da sauran

Kawayensu. Amarya kuwa ta ci gayu sosai ana kan shirya ta. Sai kusan magriba suka isa hall din, inda suka dafa wa amaryarsu zuwa gurin zamanta. Da yake har da kanwar Habiban ita ma da nata Kawayen.Ango sun shigo da abokansa, sannan aka yi kamu kawayen amarya da amarya sun shiga rawa ana ta ruwan kudi. Salma duk ta tsorata da wani saurayi cikin abokan ango da ya zo yana yi mata liki. ta canza guri ya bi ta, har dai ta fita a filin ta samu guri ta zauna. Sam ba ta ji zuwansa ba, sai magana ta jita bayanta, "Yammata kin gaji da rawar ne?"

A tsorace ta kalli gurin da yake, sannan ta kauda kai. Ya ja kujera ya zauna,

"Ki fada min sunanki da kwatancen gidanku"
Page 21

Salma ta firgita matuka gani take ma magana ma idan ta yi wa wannan mutumin alhaki ne, amma dole ta tanka ko don ta roke shi. Ta dube shi, sannan ta -waiwaya baya ta kalli gefe da gefe, sannan tace

"Ina da miji bawan Allah, ni matar aure ce

Ya yi dariya,. '

"Ta ya ya zan yarda da ke? Ba kiyi kama da matar aure ba. Ni sunana Yusuf Bashir, muna zaune a Malali, dalibi ne a jami'ar

Ahmadu Bello dake Zaria, kuma yanzu ina shekara ta karshe, ina karantar.

Salma ta daga mishi hannu, "Malam, don Allah ka tashi a nan! In kuma ba za ka tashi ba ni bari ka ga". Ta mike da sauri ta koma filin, ta rike hannun Salma Dankasa, tace Salma zan tafi gida, ku zo ku raka ni"

Salma Dankasa ta dube ta, "Haba don Allah,yanzu fa aka fara, kuma ko abinci ba ki ci ba".

Ta ce, "Kin san da ya yaya aka bar ni? Don Allah ni dai zan tafi, ga shi gurinmu da nisa, zan iya rasa abin hawa fa"

Salma ta ce, "Ki bari komai yayi dai dole akai ki har gida"

Salma ta hakura ta ci gaba da zama, amma a darare. Ko da aka soma ciye-ciye Salma kawai ta yi ta ajiye. Ta kalli agogonta, tara saura ta mike da sauri ta nufi gurin Salma inda suke ta daukan hotuna. Tace

"Salma ko ba za ku raka ni ba
Chapter 15 · 0% Book details