← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace Kar ki dau fushi da sauri Majiya,kin san manyan nan sai a hankali, da ma hulda dasu sai hakuri*

Hajiya tace "Uhum'! Tafiya ma zan yi"

Ta ciro wayarta a jaka, tana nemo lambar Shatima yana dagawa, tace

"To ya kamata mu tafi haka ko?"

Ya ce, "Da sauri haka Hajiya? Ki bari mana Sai yamma?"

Ta ce, "Ni yanzun zan wuce, in kuma ba za ka tafi ba to mu je mu hau ta haya

Ko ba a fada masa ba ya san Hajiya ranta ya baci, ya yi tsaki cikin tunanin me ya faru? Amna ta mike,

"Tunda ya gama bari a kai shi su Hajiyar su ganshi ko?'

Yace Yauwa, kai shi"

Sai yanzun ya gane abin da ya sa Hajiya jin zafi. Tana ta zumudin ganin yaron, amma har yanzun ba ta ganshi ba.

Amna ta shiga ta mika yaron ga Aliya tare da fadin, "Ga shi"

Hajiya cikin

*yar gajeriyar fara"a mai boye damuwa tace

"Da kun barshi ma Allah ya raya

Amna wadda ba ta cika damuwa da damuwar mutane ba bare ma ta gane wai haushi Hajiyan ta ji, tace, "Badi'atu ba ta z0 ba ne?"

Hajiya ba ta tanka ba, sai Aliya ta ce,

Sai ranar suna Amna ta fita ta koma gurin mijinta.

Page 15

Mun tsaya

Amna ta shiga ta mika yaron ga Aliya tare da fadin, "Ga shi"

Hajiya cikin

*yar gajeriyar fara"a mai boye damuwa tace

"Da kun barshi ma Allah ya raya

Amna wadda ba ta cika damuwa da damuwar mutane ba bare ma ta gane wai haushi Hajiyan ta ji, tace, "Badi'atu ba ta z0 ba ne?"

Hajiya ba ta tanka ba, sai Aliya ta ce,

Sai ranar suna Amna ta fita ta koma gurin mijinta.

Da Kyar Mama ta lallashi Hajiya ta dauke shi domin da ta ki, ta ce, ai ta ganshi a hannunsu. Duk wannan abu da su Hajiya ke yi sam Momy da 'yan
uwanta ba su san ma arziki tana bori ba.

Shatima tamkar ya tafi da dan gudan jininsa haka yake ji. Sun yi batun kayan suna, ya ce zai sa

Anty Momiyo ta turo mata lesissika da atamfa don ta zaba, ya kuma tambaye ta ko nawa zai ba da game da
abincin suna?

Amna ta ce,

"Ni ban sani ba, amma bari in tambayi Anty Amarya

Anty amarya ta ce,

"Tabdi! Gaskiya ban san ya zan ce maka ba sha'anin gidan nan ana kashe kudi sosai, ka dai kimanta ka bada kawai

Ya ce,

"In na ba da dubu hamsin ya yi?"

Duk suka yi shiru, duk da sun san karfinshi baikai nasu ba, amma dai dubu hamsin bai kai ko kudin kajin da za a dora a kan abinci ba. Ban da Sada ya zama.ka'ida dole a yanka, ga nau 'o' in abinci da na sha.
Jin sun yi shiru Shatima ya ce,

"Anty abin ne da
yawa, yanzu haka Nafisa a watanta ta ke

Anty ta ce,

"Duk da haka sun yi kadan sosai".

Ya ce, "To insha Allah zan kara".

Amna ta ce,

"Ni ka bada dari da hamsin ko dari biyu sai ka bar kayan da za ka sai min na fitar suma, tunda ina da kaya ko na lefena ban taba ba, sai nadauka a ciki"

Anty amarya ta ce,

"Momy ma ta dinka miki kayan suna tun zuwansu Dubai"

Ya kalli Amna,

"Shi kenan, in dari biyu ba ta samu ba zan yi kokarin ko dari da hamsin ne. na gode
da karamci, in ina da kud矛 kin cancanci in kashe duk abin da na mallaka a kanki da dana"

A mota Hajiya tana ta mitar abin da aka yi musu a gidan su Amna, fadi ta ke,

"Ban da isa sai a wani share mutane ana nuna irin wannan iko? Kai da
gudan jininka sai an wulakantaka sannan za a ba ka?

Mu ba rokonsu muka je ba, ba ruwanmu da abinsu"Mama tace

"Ke ma kina da gajen hakuri ne

Hajiya, shi fa shi'anin masu da shi din nan sai da kai zuciya nesa, don sai ka iya zama da su"

Shatima ya Ce,

"Wai me ya faru?"

Hajiya ta shiga rattafa mishi abin da take ganin an yi mata. Cikin sauri Shatima ya ce, "Laifina ne, nine na kasa ba da shi, ki yi hakuri"Daga nan ta dan saurara.

Ranar suna gidan tankam da dan Adam. Da masu masu zuri'a ne sosai, dangin Shatima da matansa sun z0, amma ban da Salma. Nafisa ma tazo ta gane wa idonta. An ci an sha kuwa komai sai da aka barshi, ga maijego da jariri suna ta shiga suna fita.Nafisa kuwa a ranta fadi ta ke, ai gara da na zo na gane ma idona don kar in haihu ba a yi min wani abin ba.

Kyauta kuwa ta kaya da kud矛 har da mota yaro ya samu, babban wansu Amna ya sai mishi. Aliya kuwa tamkar "yar aiki haka ta zamar da kanta, duk wanda yazo ita ce mai zuba abinci duk da cewa akwai wasu da aka tanada don raba abinci. Da ma neman suna take yi a gurin dangin Amna, kuma ta samu. Don in sunata yaba mata. Da za su tafi aka hada musu kaya rigijit Sai Karfe takwas da wani abu suka isa Zaria.

Nafisa ta ce, ita kam ba za ta tafi Kaduna adaren nan ba, gobe a kawo ta.Cikin wanna daren ciwon haihuwa ya taso ma

Nafisa, aka nufi asibiti da ita. Hamida ce ta kira

Shatima a waya ta sanar da shi. Ji ya yi tamkar ya yi tsuntsu ya nufi Zaria. Ta sha wahala sai asubahi ta haifi danta mai kyau. An yi mata dinki don sai da aka karata.

Da sassafe su Hajiya suka je asibitin da Alhaji,
sun yi murna sosai, Alhaji ya rungume yaron yana yi masa addu'a. Ba tare da neman shawarar Shatima ko

Nafisa ba ya yi wa jaririn huduba da Musa, sunan mahaifin Nafisar, Kaninsa. Ya mika wa Hajiya shi tare da fadin,

"Karbi Musa na yi masa huduba

Hajiya ta ce,

"Alhaji ka yi shawara da iyayen
dan ne, ka san fa su

*ya yan yanzun kafin a haihu an zabi suna

Nafisa ta yi dan murmushi tana daga kwance,

Tace A'a ba mu zabi suna ba

Alhaji ya ce,

"Ko ma dai kun zaba ta sunan dan
uwana Allah ya ci da shi".

Sallamar Shatima ce ta sa Hajiya canza abin da za ta fada zuwa amsa sallama.

Gurin Nafisa ya wuce kai tsaye ya kama hannunta yana yi mata sannu.

Mama ta fito daga
bandaki tana yi musu sannu da zuwa. Suka gaggaisa, ta dubi Shatima ta ce,

"'Har ka zo?"

Yace Eh mama

Sai lokacin ya gaida su duka.

Hajiya ta mika mishi jariri tare da fadin,

Babanka Musa"

Mama tace

"Wa ya yi masa huduba da sunan tsoffi? Don ita da ma sunan kakanta ne.

Alhaji ya ce,

"Su sai su ce ba sa son sunan

Baban nasu in ji

Shatima ya manna dan a Kirjinsa tare da fadin

"Wane mu? Allah ya sa ya biyo halin Baban namu Duk suka amsa, sannan suka koma kan

shawarar inda za a kai Nafisa gidanta ko nan Zaria.Shatima ya ce, shi dai ta koma dakinta. Hajiya ta ce,

"Wane ne zai kula da ita can?"

Mama ta ce,

"Tunda dai mijinta ya fi son ta zauna a can a barta ta koma can"Hajiya ta ce,

"A'a in ba za ki tafi da ita ba, ni in tafi da ita"

Shatima ya ce,

'"To duk yanda ku ka yi".Ya dubi Nafisa,

"Ina ki ka fi so?"

Ta ce,Ni gurin Mama zan tsaya"Ya ce,

"Shi kenan. Aliya ta ce in gaida ki kafin ta zo. Ni ma yanzun zan wuce gurin aiki ne"

Kaka ta ji dadin yanda a ka sa wa jaririn sunan kakansa don ita tana son ake yi wa juna kara.

Kwana biyu da haihuwar Nafisa kwatsam sai ga Hadiza da Innarsu murna a gurin Salma ba a magana.

Ta yi musu girki mai dadi ta kuma hada musu abin sha.

Sun yini sun sha hira amma ko da wasa Salma ba ta sanar da su Inna rashin jituwarsu da Shatima ba. Ta dai fada musu haihuwar Amna da kuma ta Nafisar da ta ji a bakin Aliya, don ko shi ma ba ta samu ta yi masa barka ba.Inna ta ce, in ta koma za su je da Hadiza su yi
wa Hajiya kaka barka.

Salma ta ce, har da can gidan

Shatima duk ku je. Sai a nuna muku gidansu Nafisar tunda tana can Zaria din. Inna ta ce,

"Insha Allah za taje"

Da za su tafi, Salma ta kawo dubu' biyar ta bai wa Inna ta ce, ta yi jari ko na kayan miya ne don Inna ta yi kuka da rashin sana"a. Ta raka su suka tafi.

A bakin Aliya Shatima ya ji cewa Innar su Salma tazO, ya same

"ta a dakinta tana rubutun islamiyya, ya ce,

"Ke wato su Inna sun zo shine ba zaki iya kirana ki ce min sunzi ba ko?".

Ta ce,

"To ai Yaya ba ka daga wayata shi ne dalili? Ya CE,

"T貌 me ya hana ki yi min message?"

Ta yi shiru ba ta son jayayya ne kawai, amma message nawa ta yi masa babu amsa. Ya ce,

"Kar ki sake yi min irin haka. To me ki ka ba su?"Ta dago

"ta dube shi a dan tsorace,

"Kudin hannuna ne kawai na ba ta duka".

Ya juya zai fita, ta ce,

"Ashe Anty Nafisa ma ta haihu?"

Sai da ya saka Kafa a waje sannan yace"Eh".

Gidan su Nafisa ta koma, Hajiya ta hada kayan barka ta kai. Alhajin su Shatima ya sai raguna. Ranar barka ko in ce ranar kauri, gidan cike da dangi da yake su ma akwai zuri'a.

Page 16

Mun tsaya

T貌 me ya hana ki yi min message?"

Ta yi shiru ba ta son jayayya ne kawai, amma message nawa ta yi masa babu amsa. Ya ce,

"Kar ki sake yi min irin haka. To me ki ka ba su?"Ta dago

"ta dube shi a dan tsorace,

"Kudin hannuna ne kawai na ba ta duka".

Ya juya zai fita, ta ce,
Chapter 11 · 0% Book details