Sashe 2
Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kai watan. Su kafin haka nasu ya fare, ita ko Salma
dubu daya a wata, dubu talatin, sannan bana sai mata kaza. In na siyo gasasshiya har da su nike saye. Haka kuma akwai kudin kati da nike saka musu duk sati, ita ko ko wayar ma ba ta mallaka ba bare kudin kati ya je mata
Shatima ya dubi Hajiya,
"Zancen makaranta kuwa,alkawari na dauka tsakanina da mahaliccina cewa, zan taimake ta tu帽 kafin in yanke shawarar zan aure ta
Ya numfasa sannan ya kalli Mama,
"Akwai abin da ba ku sani ba. Babu son Salma ko digo a cikin zuciyata, so na soyayya dai sam babu wannan. Na auri
Salma ne don in taimaki rayuwarta ta yi karatu. Ta so in aura mata wani ne, in mata kayan daki don ta cika
burin Babanta. Ni kuma na aure ta don ta cika duk
burikan guda biyu ne. Zan iya zama da Salma har karshen
rayuwarmu, in kuma da zuri'a a tsakaninmu har mu
samu rabo, ba zanyi Ki ba. Amma ba don so ba. In kuma tana bukatar rabuwa da ni yayin da burinta ya cika, zan iya sahale mata ta je ta auri wanda ta ke so, yake sonta.
Ban fadi haka don cin fuska ga Salma ba, sai don hakan shine gaskiya, kuma Hajiya ta gane cewa,Salma ba su yi min asiri ba
Salma kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ke
zuba a idanunta masu radadi. Tun da aka soma rigimar
bata tsinci kanta cikin bakin cikin da ya kai na yanzun
nan ba. Kalaman Shatima sun yi tsauri, kuma sun yi
ma zuciyarta daci, sannan sun yi ma kwakwalwarta nauyi. Har ma ta ji da ma ya bi umarnin mahaifiyarsa
ya sake ta din zai fiye mata jin wadannan munanan
kalaman da suka fito daga bakinsa. Ta soma rainon
zuciyarta, har ta soma koyon sonshi, da tantance son
Page 3
Don ta samar da sotsan tsamara gauraye. Ashe ita tana aikin banza ne, gara ma da ta sani tun da wuri.
Ta dago jajayen idanunta ta kalle shi, yana da Kimar da ba za ta iya maida mishi magana ba, don haka ta sake sunkuyar da kanta.
Alhaji yace
"Duk abin bai kai a yi wannan tone-tone ba, kada in Kara jin an yi zancen saki, ko
asiri
Ya dubi Hajiya Amina, yace
"In kin ci gaba da dagewa a kan wannan maganar zan ta sa ki har gaban Hajiya Azumin, sannan mu je gurin malam su bani hujja'
Ya nuna ta da yatsa,
"Kin san zan iya Alhaji Musa ya ce,
"Wannan shine gaskiyar magana
Mama ta ce, 芦Ni wallahi duk wannan abu ba a son raina suka faru ba. Ban so aka tono wadannan zantukan ba, tunda ban san komai a kai ba. Mun dai z0 duba mara lafiya
Alhaji yaja tsaki, "Ga shi mun rasa jam'in
magariba a kan zantukan nan marasa tushe, bare makama
Ya kalli Hajiya,
'"Ke ce babbar mai laifi a cikin wannan al'amarin"
Ya kalli Salma 芦Tashi yarinya kin ji daga wanna durkuson
Salma ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta yunkura da niyyar tashi. Kafafunta sun yi tsami, ba za su iya daukarta ba, don haka ta koma ragwat! Ta zauna.
Alhaji Musa ya ce,
'"Sannu, Kafafun naki duk sun yi tsami ko?"
Ya sa hannu a cikin aljihunsa ya ciro kudi ya kirga naira dubu goma sha biyar ya mika wa Shatima, ya ce,
"Ga shi ka sai mata waya ko karama ce, don ita ma ake saka mata katin ko da iyayenta sa gaisa
Ta dubi Alhaji Musa ta ce,
"Baba na gode".Muryarta tana rawa.
Yace
"Babu komai "yata"
Yaci gaba,'da Kowacce ta koma gurinta ta zauna lafiya da mijinta da
"yar uwarta, zuciya daya
Amna ta kalli Hajiya,
"Babu maganar asiri-asiri ko?"
鈥� Alhaji ya amshe,
"Babu wata magana da ta
shafi asiri, duk sharri ne'
Ta ce,To, ku gaida gida".
Ta nufi sashenta cikin jinjina abin da ya faru.
Aliya ta mike tana fadin, "Ga shi ko abincin ma ba ku ci ba. To ku gaida gida"
Salma ta bi Aliya da kallo, ba ta shakka ita ce ta hada komai. Ta soma tuno wasu abubuwa da ta yi mata masu kama da ingiza mai kantu ruwa.
Salma ta yunkura ta mike da kyar ta dubi su
AlhajiBaba ku gaida gida"
Ta kalli su Hajiya,
- "Sai anjimanku, Allah ya tsare hanya Su Alhaji suka ce,
"To sai anjima, ki yi hakuri kin ji ko?"Hajiya ta tabe baki tare da raka Salmar da harara.
Nan Alhaji ya yi ma su Hajiya fada sosai,sannan suka ce,
"Ku shirya bari mu yo sallah mu zomu wuce"
Salma ranar da zazza6i ta kwana, haka kuma ba
ta jin cewa za ta je a yau. Lokacin da Shatima ya shiga
gurinta da safe tana nade a zanin gado a can tsakiyar gadonta. Ya kira sunanta,
"Salma".
Da kyar ta daga idanunta jajir ta ce, "Na'am."
Ya ce, "Ya ya dai, ba ki da lafiya ne?"
Ta maida idanu ta rufe, zuwa yanzu ba ta son taji ko ta ga Shatima. Ta ce,
*"Dan zazzabi ne'
Ya hau gadon ya saka bayan hannunshi a sassan wuyanta. "Kai! Haka jikin naki ya yi zafi? Tashi in kai ki asibiti
Ta yunkura tare da fadin, "Ka barshi kawai, zai bari anjima kadan
Ya ce, "To in turo Aliya ta duba ki?"
Ta ce,
"Ka barta anjima kadan zan warware"
Ya ce,
"Yaushe ki ka soma gardama da ni?"Salma ta yi shiru,
Ya kama hannunta,
"'Sakko in kai ki asibiti"
Jallabiya ta saka suka tafi.A bakin
makarantarsu suka tsaya, ya rubuta *yar takarda ya bawa mai gadi ya ce ya kai ofishin shugaban makaranta.
An ba ta allura da magunguna, ya dawo da ita
gida. Ya shiga gurin Aliya. Da ma ta ga fitarsu, ya ce,
don Allah ta lura da ita ba ta da lafiya.
Aliya tace, "To"Yana fita ta zauna cikin fargaba, kar dai ita ma
wannan cikin gare ta? Na ba ni ni Aliya, nice kenan zan zama karshe?"
Ta mike da sauri tare da fadin, "Bari na je dakin Salmar na gani"
Ta same ta kwance kan kujera. Salma tana gaminta a ranta ta ce, "Allah ka yi min tsari da duk sharrin da matar nan ta zo min da shi
Aliya ta je gabanta ta tsaya tare da rike kugu,
"Ashe ba kya jin dadi?"
Salma ta ce,
"Uhum".
Aliya ta ce,
"*Ko ke ma cikin ne?"
Salma ta ce, "Oho! Ni ma ban sani ba"
Ta sake matsawa kusa da ita,
"Wane irin gwaje-
gwaje aka yi miki?"
Salma ta yi mata banza. Tsaki ta ja ta fita tana mitar, yana fadin ba ya sonta amma ga shi nan da cikinsa a jikinta.
Salma ta shiga kunci da bakin ciki sakamakon kalaman Shatima. Duk da wautarta da Kuruciya ta san
Shatima ya ba da ita badawa ta karshe, ya kunyatata gami da tozartata. Ta yanke ma kanta dakatar da son
Shatima, sannan za ta ja baya da shi. Za ta ci gaba da kallonshi a matsayin Yaya kurum
***
Kwanci tashi asarar mai rai inji masu iya
magana. Amna da Nafisa ciki na ta girma. Domin
Amna tana da shidda, Nafisa tana da wata biyar.
Shatima ya samu Amna da batun zuwa awon
ciki, ta ce masa ita sai sun dawo daga umara. Ya dube ta cikin al'ajabi,
"Za ku je ummara yaushe?"
Tace
"Jibi insha Allahu za mu tafi da su Momy
Yace, "Ikon Allah, shine ban isa ki fada min ba bare ki nemi izinina?
Ta ce,
"Jiya Mom ke fada min ni ma'
Shatima ya yi shiru cikin bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya, abu daya zai sa ba zan hana ki ba, amma gaskiya a guji shigar min hakki"
Ta dube shi.
"Ban gane ba? Kana nufin da saika hana?"Yace
"Kwarai kuwa Ta yi *yar dariya irin ta rainin wayo, ta ce,
"Kai kana da son rigima"
Ya kauda zancen don ba ya son su fara sa'insa,
don haka sai ya ce, "Ke nan ba ki nan za a yi bikin su Hannatu, yaran Yayan Alhaji marigayi na Kaduna?"
Ta dan yatsina baki,
"Ko ina nan ka san bai zama lallai inje ba don bana son hayaniyar mutane
Shiru ya yi yana kallonta, don tuni ya lura ba ta son duk wani al'amari da ya shafi danginsa, domin ko
kwanan baya da Hajiya Kaka ta yi rashin lafiya babu yanda bai yi ba a kan su je a duba ta ba, amma ta ki, kuma sauran duk sun je. Amma bari ya yi mata uzuri ta haihu.
Bikin "ya'ya biyu za a yi, babban dan Kaka wanda ya rasu, bikin a Zaria za a yi shi. Haka kuma
bikin zai kama ana saura sati daya azumi. Da Amna ta
Page 4
shirya za ta tafi Kano don yin tatiyarsu, Shatima ya yita maza ya ce,
"Allah ya tsare hanya". Ya kuma kawo dubu goma ya ba ta.
Kanwar su Alhaji Hajiya Sauda ita ce ta fito da
anko, ta kira Shatima tana sanar da shi cewa, ga na" matanshi kala bibbiyu, kudinsa naira dubu arba" in.
Ya ce, "Anty na mutum uku za a cire, Amna bata nan anty tace To zan barsu gurin Kaka"
Ya ce, "*Shi kenan, ki turo account in tura miki
kudin Da ya sanar da su batun anko, Nafisa ta ce za tasa Hamida ta je ta amshi nata a gurin Kaka din. Aliya ma cewa ta yi za a zo daga gidansu a karba mata.
' Salma kuwa cewa ta yi, nata a bai wa Anty Badi 'atu ta bai wa mai mata dinki.
Ya ce, "To telan ya sanki ne?"
Ta ce, "Ta yi masa kwatance na kawai
Salma Bash shine sunan da *yan makarantar su Salma ke kiranta da shi. Kawarta Salma Sadik Dankasa
ita ce ta rada mata shi. Zuwa wannan lokacin Salma ta waye, ta goge, ga turanci tana gane karatu sosai.