← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki Yaya, bai ma fada min ya biya kudin ba. Allah ka ba ni ikon gama karatun nan, ka albarkace ni da samun aiki, zan taimaka masa da dukkan abin da zan iya sannan in taimaki iyayena"Suka yi bankwana a kan sai gobe.Hajiya ta dubi Momiyo.Ni fa Allah tunda

Aliya matar Shatima tazo lokacin da ta yi arba' in din nan take ba ni labarin irin kudin da Shatima ke kashewa kan konanniyar yarinyar nan du tsanarta ta karu a raina, ga iyayenta shine cinsu da shansu, shi ne kudin haya

Momiyo ta ce,Karatun jami'a kam da kashe kudi, amma tunda shi ya ga zai iya ke ki daina damun kanki mana Hajiya taCe,Allah dole in damu. Shekaran jiya Aliyar ta sake kirana tana fada min,wai ga shi har ya kai matakin kasawa da su. Duk da albashinsa mai tsoka da yake dauka, har bashi yaci na abincin gida Momiyo taCe Bashi kuma?

Wane iri? Shatima gaskiya gara a san abin yi Hajiya ta ce, Ba ina fada miki ba ya z0 da son shiga kasuwanci ba, har kina murna? To na fasa bashi kudina, karshe ni zan kwana ciki a bashi ya kashe musu anty Momiyo ta ce,

"Kar ki hana shi, amma ki masa kashedi, kuma ki nuna masa kin. san me gidan nasa yake ciki" Tace Ai in na nuna masa na san abin da gidan nasa yake ciki sai ya yi mata magana, kuma daga nan zan daina jin komai. Zan dai san yanda zanyi in ga na raba su, don bala'I ita ba haihuwa ba ba komai ba sai tsatsibar kudi kawai suke yi" Momiyo tace

"Kaka dai tana yinta sosai" Hajiya ta ce,

"Ta yi ta yinta din, ni dai dole ya rabu da ita ba zan iya ba. Na soma yi wa Alhaji mitar yayu tsalle ya ce kar ya kuma jin haka Momiyo tace, "Allah dai ya kyauta, amma dai Hajiya ki bi a hankali"

Shatima yana tafe cikin motarsa gida ya nufa,don shi ba shi da dabi'ar yawo babu dalili.

Kyakkyawar yarinyar da yake yawan gani a kusa da gidansa ce ta sa mishi hannu alamun ya tsaya. Kamar ya wuce, sai kuma ya tsaya. Ta iso da dan saurinta gefe da ba kowa ta kalle shi, "Don Allah Baban Ashraf gida za ka?"

Ya dauke kai daga dubanta, don wani salo da ya ga tana yi da idanunta, sannan ya ce, "Eh"

Ta ce,In shigo ka taimaka min, na rasa abin hawa Ya ce,Bismillah"

Ta bude ta shiga tare da fadin, "Na gode"

Bai tanka ba ya figi mota.

Ta dube shi, hankalinsa yana kan tukinsa, tace, "Ba ka yi mamaki da na kira sunanka ba?" Ya dube ta, fara ce tas ga kyau, ya maida kai Kan titi Ban yi wani mamaki ba gaskiya, don an fada min haka Ta ce,

Ka san ni to, da ba ka ji mamaki ba?"

Ya ce,Ban sanki ba gaskiya, amma na taba ganinki a layin da nike"Ta saki wata yar dariya,

芦Tunda nike ban taba ganin mutumin ddaya ganni sau daya ya kuma ganina bai gane ni ba. In na tambayi dalili sai ace kyauna ne sila'Shatima ya sake kallonta cikin mamakin maganarta. Ya maida kai titi, "Hakika kina da kyau. Ta ce, "Kai ma ka yaba kenan?"Ya ce,A'a, na dai fad矛 abin da yake zahiri"

Ta dan yi shiru kamar mai nazari, sai ta sake dubanshi.Kusan kowa ai yana yabawa da mai kyau, musamman ku maza Ya ce,

"Haka ne, amma kowa da ra'ayinsa ba a komai kyau ke burge ni ba, musamman ga mace.Don bana son abin yayi da kuma wanda kowa ke so. Ina ki ke ganin yanda Kuda sukan taru a kan alkakin da ya ji suga Maganar ta shige ta, don haka ta ce,

"Ai kuma irina ba kowa nike ba fuska ba?".

Daidai lokacin ya tsaya a kusa da gidansa,

"Kina iya sauka zan shiga gida"

Ta bude, "Har mun iso?"

Page 31

Bai tanka ba, ta dube shi bayan ta fita, " Na gode Nan ma bai tanka ba. Ya karasa gidansa. Nafisa da yara suka fito suka tari Shatima, sai yanzu ta gane cewa zamanta a Abuja jin dadi ne, don tana manta cewa tana da wasu kishiyoyi. Ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta zauna suka shiga cin abinci, Saura sati daya bikin

Auwal, Salma tana wanki sako ya shigo wayarta, har kashi biyu a jere. Hakan ya tabbatar mata ba

"yan gidan waya ba ne. ta dauraye hannu sannan ta goge ta dauki wayar. Daga ganin rubutun ta san wanda ya iya' ne ya yi shi. Da turanci ya turo sakon kamar haka;

Salma, barka da war haka, na san cewa yau hutu ne na karshen mako kina gida. Ina fatan kina cikin Koshin lafiya. Safwan ne, babu mamaki ba ki da lambata, don na ce ki kira in samu lambarki amma kin ki. Ban ga laifinki ba, domin kina kare aurenki ne. salma na so in hakura da tsananin sonki da ya kama ni a ranar da muka yi karo da ke, amma inna tuna wasu kalamai da mijinki ya yi a lokacin da muka je siyan wayarki, sai in samu kwarin gwiwa tare da yarda cewa zan iya cimma burina. Ya sanar dani ke da shi ba auran soyayya ku ka yi ba, kuma ya ce shine dalilin da ya sa bai kuma tunkararki da huldar auratayya ba tun sau daya da ya gwada ki kaKi yarda. Kuma ya tabbalar min da rashin son da ki ke masa ne ya sa ki Kinsa, amma ba rashin wayon da ki ka nuna masa a lokacin ba tunda yara ma wadanda ba su kai ki shekaru ba sun san rayuwar aure, kuma in na tuna yanda ya nuna ba zai takura miki ba in kin fidda wani mijin zai barki, sai ince tattala min ke yayi. Kuma ban da Allah ya hukunta cewa ba shi da rabo ya za a yi ya zuba wa mace kamarki ido? Salma cike da karfin gwiwa nike fadin ina sonki, so na hakika, kuma na shirya daukan duk wani kalubale da zai taso a dangi in ma da shi. Sannan zan nuna miki soyayya irin wadda ba a taba nuna ma wata ba a duniya ba cika baki ba. Fatan za ki yi nazarin zancena sosai, kuma kar ki damu kanki da cewa sai kin ba ni amsa, na fi son ki yi nazari. Na barki lafiya abar kaunata

Salma ta jike sharkaf da rufa, ta maimaita karanta dogon sakon ya kai sau goma sha biyu, sannan tuni ta manta da batun wanki ta hau gado don son yin nazari. Duk da ta yi bakin ciki da sakon Safwan, amma ba ta ji haushinsa kamar yanda take jin na Shatima ba. A fili take fadin,

"Lallai Yaya Shatima ya kai makura a rashin sona. Na zaci tuni ya bar Wannan zancen?"

Ta tashi ta je gaban madubi.

"Mene ne laifina? Duk da ban kasance kyakkyawa ba, amma ban zama mai munin da za a guje ni ba Gaskiyar Safwan ne Shatima ba ya ra'ayina, da ko bai sona zai bukace ni. Na yi ta yin tunani a lokuta da dama ina neman dalilin da tun tayin farko Yaya bai sake kula ni ba, ashe Kaunata ce ba ya yi"

Ta ja numfashi, sannan ta saki kuka. Ta yi kuka sosai domin tana tuna lokacin da ya fada a gaban kishiyoyinta da iyayenshi. Lallai ya kaita babbar hujja, kuma daga yau ta ja layi da Shatima, ta shirya yaki da tallarta da yake yi. Ta sake fadawa kan gado, ta ce,

"Ban san adadin mutanen da ya fadamawa ba ya sona ba. Gara ma ya sauwake min in huta, matanshi ma duk a banza suke kallona'Yar karamar hauka dai Salma ta yi ta a ranar, kuma ta lashi takobin nuna wa Shatima cewa ta gaji da zama da shi, wanna satin in ya zo sai ya sake ta.

Ranar dai wanki bai gamu ba, sai washegari.

Ta kwana cikin fushi da ko abincin dare ba ta ci ba.Ta zuba idon ganinshi a washegari lahadi, amma bai zo ba, kila wanna satin ba zai zo ba, don ya kan yi haka yanzu.

Ranar litinin ta dawo makaranta da dare tana kwance, duk ta gaji har ranar ba ta da walwala. Ta dauki wayarta tana kara karanta sakon Safwan. Ta samu kanta da rubuta mishi amsa duk da yace ba ya bukata.

*Yaya Safwan ban ji haushinka ba, da na zaci ko kana son yin hulda da nine a munafunce lokacin da ka sa min katinka cikin laptop din da ka sai min. In ka shirya za ka aure ni zan yi yaki in bar wanda ba ya sona, in koma ga wanda yake sona. Da ma ni ban damu da so ba bare in ji haushi, ina nufin ban san so ba. Sai dai na yi imani in na zauna da mai sona Zan koyi so, tunda ance zama da madaukin kanwa. Na gode sai dai ba za mu sake magana ba har sai na zama bazawara ko in ce sakin wawa Ta tura a layin Safwan.

Salma me take shirin yi? Domin yau talata kwanaki uku-kenan ba ta daga kiran Shatima, sakon dubu biyar din da ta gani a account dinta ba ta gansuba ta gani ba. Ranar talatar ba ta je makaranta ba,don ba za su yi komai ba tunda sun gama jarabawa.Tana yin tuwonta tana kallon kiran Shatima yana shigowa yana tsinkewa har kashi uku.A gefen Shatima, ya shiga damuwa da rashin samun Salma. A iya saninshi ko missed calls dinsa in Salma ta gani za ta mishi filashin ko sako. Ya fi tunanin ba ta da lafiya ne, amma Aliya ta ce masa lafiyarta lau kuma tana zuwa makaranta. To me yake faruwa? Ya kuma kiran Aliya, ya ce,Salma tana gida?" Ta ce,

"Eh, don yau ba ta je makaranta ba

Shatima ya ce,

"Ki je ki gani lafiya? Sannan ki ce nace ta daga wayata yanzun nan
Chapter 22 · 0% Book details