← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma ta zuba idanu tana kallonshi, ya yi kyau
cikin yadi mara nauyi mai ruwan madara. Hular kansa ta yi matukar dacewa da kayan. Ya kalle ta, ta lumshe ido, tare da fadin, "Barka da zuwa".

Ya ce,

"Yauwa. Na ga ko shiryawa ba ki yi ba?"

Ta ce, "Wai har tafiyar ta tashi? Na zaci sai dare"

Ya yi mata hararar wasa, tare da fadin, "Amma na ce miki ki shirya ba?"

Ta mike, "Bari in yi wanka"

Ya ce, "Wane wanka kuma? Tashi kawai mu tafi ki yi shi a gida in mun koma".

Inna ta ce, "Gaskiya kam, domin ba zama zai yi yana jiranki ba".

Salma ta tura baki don yin shagwaba ga Inna, tace, "Kuma hijabi kadai zan zira?"

Inna ta ce, "Oho! In ma a haka za ki babu hijabin je ki"

Shatima cikin murmushi ya ce,

"Inna fada mata dai".

Inna ta dubi Shatima tana 'yar dariya, tare da yin godiya da dawainiyar da ya kawo musu,

Ya ce Haba Inna, a yi hakuri da shi, garin ne sai a hankali"

Salma ta hada kaya tana tura baki, ga su da dan yawa saboda dinkunanta da ta amsa. Shatima ne ya
kinkimar mata kayan. Ita kuma ta rataya hijabi a katada.Shatima ya ce, 鈥濨a ki fa san gatse ba fa ke? Ki saka hijabin mana .Salma ta yi mamakin ganin Aliya a cikin mota,

ashe ya dauko ta. Salma ta yi ta maza ta dube ta, but ya zuba kayan Salma sannan ya shiga. Ita ma ta shiga baya suka nufi gidan su Nafisa.

Suna isa Abin da ya bai wa Salma mamaki sal taga

Aliya ta fita ta nufi cikin gidan su Nafisa tare da Shatima,

ita ma saita Fito ta bIsu. A zuciyarta kuma tana tambayar me ya sa ba ta shiga nasu gidan ta gaida Innarta ba?

Sun samu duk yan gidan a falo, Da alamu Nafisa tuni ta shirya don jiran zuwan Shatima. Aliya cikin
kissa da irin salonta ta nufi Nafisa.

Yar uwa ya ya dai?" Natisa ta yatsina, fuska, "Lafiya, ya ki ke?". *"

Aliya ta ce, "Lafiya Ta rusuna tana gaida Mama,wadda Suke magana da Shatima. Salma ma ta rusuna tana gaida

Maman. Hamida cikin fara'a ta dubi Salma,

"Za ku tafi?" Salma tace Eh. Yauwa Hamida ina

hotunanmu na wayarki?"Ta ce, "Bari in dauko in tura miki Aliya ta kalli Shatima, "Taso mu je Nafisa karmu yi tafiyar dare Tuni Salma ta fahimci Aliya tana fadin haka ne

don taji Hamida za ta tura mata abu a cikin waya. Saita zauna tare da fadin, Dauko ki tura min, ni ban yi hotuna sosai da wayata ba, kin san ba ta da kyan hoto Ko da Aliya ta azalzala su tafi hakan bai saka

Salma ta tashi ba, sai da Hamida ta gama tura mata

sannan suka fito a tare zuwa gurin motar. Aliya ta kalli

Salma wadda ke rike da jakar Nafisa ta taya Hamida dauka. Ta ce,

*Ai na zaci ke ba yau ba

Salma ta yi tamkar ba ta ji ta ba, suka yi

sallama suka hau mota. Salma ta yi dan murmushi ganin Aliya an dawo bayan mota, Nafisa ta hakimce a gaba. Nan suka nufi Kaduna.

Sun dawo da 'yan kwanaki aka soma azumi.

Ranar farko dai Salma daure ta yi domin makara ta yi,

washegari ta yi Kudirin tashi nan ma daure ta yi har da zuwa rana ta uku, a rana ta hudu Shatima a dakinta
yake, ya zaci za ta tada shi kamar yanda sauran suke yi,amma sai shine ya tada ta. Ya ce,

"'In don saboda ke ne makara za mu yi

Ta ce,Ai ni ban taba yin sahur ba'

Ya ce,Saboda me?"Ta ce, "Makara nake yi"

Ya ce,

"Shirme kenan, bacci ki ke kwanciya ki ta sharawa a wannan watan mai albarka?"

Ta yi shiru, ya ce,

"To daga yau 'na kashe baccin nan. A tashi a kai kuka gurin Ubangiji"

Salma ta ce, "To zan tashi, amma sai ka taimaka gurin tashina Ya ce Shi kenan, zan dinga kiran wayarki, sai ki dinga barinta a bude

Ran da ya koma gurin Aliya, sai da ta nuna

rashin jin dadinta da tashin Salmar duk da bai tahimci ta damu din ba. Cewa ya yi ta miko mishi wayarsa a caji, sai tace wa zai kira? Ko mutan Saudi zai kira?

Sai da ya soma kiran layin Salma din sannan ya ce,Salma zan tada daga barci

Ta yi 'yar dariya, "Salmar yanzu don lalaci sai an tashe ta! Ya kalle ta da dukkan gaskiyarsa, " Salmar! Baki ganin yarinya ce, wai ashe duk azumin nan dore take yi, wai makara take Ta tabe baki daidai lokacin da yake sake kiranta, bayan kiran farko ya katse. Cikin barci ta ji

" Karan wayar ta farka da sauri cikin mayen bacci tadaga wayar tana fadin, "Yaya na tassshhhi!'

Ya ce, "Kin tashi ko dai na tashe ki?"

Ta yi murmushi mai sauti, cikin amsar gyaranta ta ce, "Yaya to ka tashe ni'

Ya ce, "To a yi maza kar a makara.

Ya dubi Aliya wadda takaici ya cika ta, yana yar dariya ya ce, "Kin ji ta wai na tashe ta amma tana fadin ta tashi"

Aliya tace

"To wai ita bata sallar dare kenan?"

Yace ai dole in matsa mata takeyi.

Aliya tace

"To kai ma kaci abincin kar kai
kuma ka makara.

Ta mika mishi kofin shayin da ta gama hadawa.

Haka kuma a dakin Nafisa randa ya je sai da tayi Korafi da zai tashi Salma, wai ita bai taba tashinta ba in ba ya dakinta.

Ya ce, "Kar wannan ya dame ki, ita ai yarinya ce ke,ki ke tashina wani lokacin ma fa

Ta ce, "Ba wani, don dai ta san za ka tashe ta din ne shi ya sa take shantakewa

Azumi ya soma tafiya, har lokacin Amna ba su dawo ba, a zatonshi sati biyu za su yi, "amma shiru!

Yana dai jira ya ga ikon Allah. Hankulan mutane ya karkata kan sallah, Aliya ta matsu da son ta samu kudi domin ta lura neman suna sai da kudi, ga shi ba ta nemi komai ta rasa ba, amma ba ta da kudi a hannunta. Wata

dabara ta fado mata, bari Shatima ya zo ta kallallame

shi ko zai ba ta kwangilar siyan kayan jarirai don ta so a ce ita ce da ciki domin da tayi tatsa sosal.

Suna kwance bayan idar da sallar asham wadda

yake jansu a falon Aliya. Salma da Nafisa sun tafi

lokacin, ta ce, "Wai masoyina sai yaushe za a sayi

kayan jarrai? Ka san fa ana yin sallah za su haihu.

Yanzun ya kamata kawai ka siya a wuce gurn in sallah tazo sai aji da hidimar sallah*.

Ya kai hannu ya janyo ta zuwa jikinshi tare da fadin,

"'Shawara mai kyau, amma kin san dole sai

Amna ta dawo sannan mu je a siya. Ban ma san ko me da me za a siya ba .

Ta tashi zaune, "Haba dai, kar ka fara da haka,

ka zama namijin da kowane lokaci a gidansa shine mai
tsarawa, kuma shine mai zartarwa. Ni na san duk abin

Page 8

MUN TSAYA

Wai masoyina sai yaushe za a sayi kayan jarrai? Ka san fa ana yin sallah za su haihu.

Yanzun ya kamata kawai ka siya a wuce gurn in sallah tazo sai aji da hidimar sallah*.

Ya kai hannu ya janyo ta zuwa jikinshi tare da fadin,

"'Shawara mai kyau, amma kin san dole sai Amna ta dawo sannan mu je a siya. Ban ma san ko me da me za a siya ba .

Ta tashi zaune, "Haba dai, kar ka fara da haka,

ka zama namijin da kowane lokaci a gidansa shine mai tsarawa, kuma shine mai zartarwa. Ni na san duk abin

ZAMU TASHI

da ya kamata a saya game da jarrai da kuma maijego, don haka ka bar komai a hannuna

Ya dago ya kalle ta Fuskarsa dauke da murmushi, ya ce,

"Haka ne, amma bana son korafin

Natisa. Bari in yi magana da ita, sai in kai ku ku zabo har da na Amna tunda an tabbatar mana cewa duk maza ne"

Aliya ta zaro ido, "Da ma ita ma Amna namiji ne?"Ya ce,Eh"

Ta hadiye wani wahalallen yawu sannan ta kirkiro murmushi,

*Ka ce gidan namu duk sojoji ne ashe?"Ya kai hannu ya shafi cikinta,

"Ke kuma sai ki kawo mana 'yar budurwa ko?"

Ta saki dariyar yake, *Eh mana"

A cikin ranta kuwa fadi ta ke,

"Allah ba zai biya bakinka ba, ni ma

namijin zan santalo, Kila yan biyu ma".

Cikin wasa ya lakaci kumatunta tare da fadin,

"Ga shi ma kinki ki yi cikin"

Maganar ta sosa mata rai har ta kasa dannewa sai da ya gani a kan fuskarta. Ya ce Ki yi hakuri banyi da nufi ba. Ina yi miki wasa ne

Ta dai cije suka canza hira.

Washegari Shatima ya tunkari Nafisa da batun siyan kayan jarirai. Ya ce,

"Ina son ki shirya mu je

kasuwa ke da Aliya ku za6o kayan jarirai naki da na

Amna, in kuma babu damuwa sai mu je ni da ita"Natisa ta fusata,

"Nima fa na san hanyar nan ba sai an je min ba ko an raka ni"Ya ce,

"To amma ai ke daya ga ciki, kuma ina

ki ka sani a Kaduna ba sai ku je tare ba?"

Nafisa ta ce,

"Ni dai a ba ni kudin kawai

Ya ce, "To na ji, yanzu nawa zan ba ki?"

Ta Ce,

"Abin da za ka bai wa Amna, ko don ita

daban ce tunda su masu kudi ne?"

Ya ce, "Au abin da ki ka tsiro da shi kenan? To bari in ta dawo na baku tare don bana son zargi Ta ce,

"Na yarda

Ana jibi sallah Shatima ya shigo da shanu gidan

don bai san ko kaji nawa zai siya ba. Ana gobe sallah

ya sa aka gyara shanu aka raba hudu, ya bai wa kowa nata, aka zuba na Amna a freezer. Nafisa ta yi waya
aka zo mata da Hamida har ta zo mata da dinkunanta,
Chapter 5 · 0% Book details