← Book details Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Rana Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yarinyar nan bana jin dadin yanda ka ke mata. Ka ga ko zanin nan da ka sai min ita ba ka sai mata ba, banso ba na yi shiru ne kawai

Ya ce,Ki bar wannan zancen".

Ta ce,Na bari, yanzu dai ina son don Allah ka barta goben sai mu tafi tare"

'Zai yi magana ta ce, "Don Allah ni za ka yi ma wannan

Yace Shi ke nan ta ci albarkacinki"

Tace,Na gode".

Ta jima sannan ta fito ta samu Salma zaune a

'falo, a hankali ta ce, "Ki shirya za ki je"

Salma ta ce,Na gode Anty.

Washegari suka nufi suna, Salma ba ta ji komai ba da ta ga Aliya ta saka sabon leshi irin na maijegon,sun yi armashi duk da bai kai na Amna ba, amma taro ya yi kyau tunda an tashi lafiya. Kwanansu daya suka dawo.

Kwanci tashi masu jego suka yi arba"in. sai da

Nafisa ta gama zaga dangi sannan ta dawo. Jaji gurin Antynta sai da ta kwana biyu, Anty Maimuna ta sa aka hada mata *yan gara masu kyau. Da ma da suna cewa tayi ba za ta ba ta komai na gudunmawa ba,ta ce za su hadu in ta yi arba"in. tun a lokacin ma ta hada mata wani tsumi wanda ta ke sha a cikin jego.

Don haka Nafisa a shiryenta ta dawo, Amna kuwa saida tayi wata biyu da kwanaki sannan ta dawo. Lokacin ne aka gama zuba zama. Aliya ta soma shige ma Nafisa kafin dawowar Amna, ta dauko Ashraf shi ne sunan da suke kiran yaron Nafisa. A goya shi, ta yi ta wannan fi'ili bare ma in ta ga Shatima yana nan, ko in ya shigo da shi, a amshe shi a goye a baya ram!

Da Amna ta dawo sai kuma aka koma gurinta,sam Amna ta hana danta in ta zo sai tace yana bacci, ko za a yi masa wanka da dai sauran uzuri, har dai ta gane ba a son ba ta shine ta hakura.

Sai ma wani sabon haushi da ta tsinci kanta,wanda kuma ba ta da damar magana. In Shatima yana dakin Nafisa ko Amna ba ya fitowa da wuri, ta san yana can yana wasa da yaranshi. Haka dai ya kan zo da

Ashraf don Amna ba ta bada yaronta. Ya kan ba da duk

hankalinshi a kan yaron, yana yi masa wasa. Wani

'lokacin ma ko tana magana ba ya ji, sai in ta yi dabara ta amshi yaron ta goya, sannan za su yi hira. Hakan yana matukar kona mata rai.

鈥� Salma kuwa karatunta ta sa a gaba. Sannu-sannu su Salma sun zana jarrabawar fita daga J.S sun shige SS 1, har lokacin Salma ba ta kara Kiba ba sai

' tsawo. Amma cudanya da yaran masu kud矛 irin su Salma Dankasa da sauransu ya sa ta waye sosai. Babu

yanda za a yi ka ga Salma ba ka yi tunanin cewa "yar masu kudi ba ce Zuwa yanzu ta manta yanda Shatima

yake fara"a, ta fi sabawa da yanayinsa na yanzun. Tana

Kallonshi matsayin wanta mai kula da ita, kuma wanda

take shakkarsa. Sai dai ta kasa manta kalaman nan masu muni da ya yi mata, hakan ya taimaka kwarai gurin Kara nesanta zuciyarta da son Shatima.

Har zuwa yau za ta yarda cewa, ba ta san so ba,kuma ba ta damu da ta sanshi ba. Haka lokuta da dama ta kalli kanta a madubi ta san cewa, ita ba mai kyau ba ce, amma kuma ba ta da munin da Shatima zai ki ko da sake nuna sha鈥檃warsa a gare ta matsayinta na

matarsa. Ta yarda rashin so ne kawai dalili. Domin don

ya neme ta sau daya ba ta yarda ba bai isa ya zama dalilin da zai sake kasa gwada sa'arsa ba. Zuwa yanzu ta fi daukar kanta a ba matar aure ba. Hakan ya fi saka ta kwanciyar hankali. Haka kuma ba ta tambayarshi

komai sai in fita unguwa za ta yi. Game da kudi ko wani abu ba ta ce masa tana son kaza, sai abin da ya

kawo ya ba ta. In ko kudin makaranta ne, sai dai ta

kawo masa takardar banki na islamiyya kuma da ma na

shekara yake biya mata. Daga cikin kudin motanta *yar dari biyar din nan take makalewa shine take siyan dan kayan bukata irin na mata.

Aliya dai tun tana boye damuwarta na rashin samun ciki, har ta dawo tana nunawa. Sai dai ta kan ji sauqi kadan in ta tuna cewa ba fa ita kadai ba ce ba tayi cikin ba, ga Salma nan. Shatima kullum yana lallashinta a kan haka, sai yake ganin kamar tana zargin shi ya kasa. Don haka da ta zo masa da batun son neman aiki a asibiti baiqi ba, don yana son ta rage kewa. Ganin in har tana fita aiki za ta dan samu kwanciyar hankali. Ta hanyar abokin aikinsa ya sama mata aiki a asibitin Kawo, Amna kuwa wata plaza yayanta ya siya a kan titin Ahmadu Bello da ke Kaduna, don haka

Momi ta ce a ba ta shago daya don ta zuba kaya. Shago
biyu aka ba ta tunda suna tausaya mata, suna ganin tana auren mara karfi. Daya aka sa mata kayan kicin,

daya aka saka mata na yara. Aka nemi masu saida mata aka zuba, kullum take zuwa don da office dinta a ciki.

Shatima bai so- ba, amma dole ya yi shiru don ya san ma ba za ta yarda ba ko ya hana ta. Lokacin

Jafar wanda suke kira da Junior Mamansa kuma tana ce masa Honey. An yaye shi don shekararsu daya,

Nafisa dai ba ta yi niyyar yaye Ashraf ba, sai ya shekara da rabi cif? Sai dai ita ma ta tada balli a kan cewa za ta shiga makaranta, don ko ba za ta yarda ba

18

Mun tsaya

Jafar wanda suke kira da Junior Mamansa kuma tana ce masa Honey. An yaye shi don shekararsu daya,

Nafisa dai ba ta yi niyyar yaye Ashraf ba, sai ya shekara da rabi cif? Sai dai ita ma ta tada balli a kan cewa za ta shiga makaranta, don ko ba za ta yarda bace kullum tana gida kowa ya fice ba. Cikin haka kwatsam sai ga Nafisa ta soma jinya.

Suna zuwa asibiti aka ce ciki, Nafisa ta daka tsalle ta ce,Saidai a zubar, Shatima kuma ya ce,

wallahi in ta sake ta zubar masa da ciki zai mata hauka, za ta sha mamaki. Rikicin da sai da ya kai su gaban

Mamanta, inda Mama ta yi mata tas, ta kuma cc kar ta sake jin makamanciyar irin wannan maganar. Dole

Nafisa ta zo ta dangana, amma sai da Shatima ya nemo mata mai aiki
saboda kulada Ashrat, tunda ita
laulayinta ba ya mata da wasa.

Wani abu da ya sa Shatima cikin wani mugun Bacin rai,

Amna ta saka Jafar a makaranta mai

matsanancin tada. Ajin wasan yara, kuma sai da ta kaishi ta yi komai ba tare da ta sanar da shi ba. Sun yi rigima sosai ba tare da kowa ya sani ba. Kinyarda da

ka^idojin da ya saka. mata ne na cewa, lallai ta ciro yaron daga makarantar domin dan ikonsa ne ba nata ba. Abin da ya sake bata masa rai da ya kira mahaifinta ya sanar da shi, sai ya nuna cewa, ai shi ta taimaka kasancewar ba ta ce ya bada kudinshi ba. Haka kuma ita ma tana da ikon yi wa dan komai tunda ita ta haife shi. Rikicin bai Kare ba, sai da ta kai kara gurin Hajiyarsa.

Hajiyarsa ta hada su ta yi musu nasiha inda ta nuna ma Amna cewa ba wai laifi ba ne don ta saka dansu a makaranta, amma komai ya zama cewa za su

ke yin shawara. Shi kuwa Hajiya ta ce ya yi hakuri

komai ya wuce. Da ma Aliya ita ce ta yi ta kara

tunzura shi. tana
nuna masa cewa kan ya yan zai

bambanta in har ba makaranta daya suke zuwa ba

Sannan yaran Amna za su raina shi a nan gaba matsawar suka gano cewar uwarsu ce ta ke yin dawainiya da su, shi za su ga kasawarshi. Irin wannan

zantukan na Aliya suke saka shi jin tsanar Amna da jin

zafinta. Bugu da Kari, Amna ta je ta saka maganin hana
daukar ciki don tace masa baza ta iya haihuwa duk bayan shekara biyu ba. Nan ma sun sha rigima da jin zafin juna.

Ranar wata litinin Salma sun je makaranta, sai aka ba su hutu domin mataimakin shugabar makarantar ya rasu, Salma Dankasa ta ce bari ta je gidan su Salma Bash sai ta yi waya a z0 a dauke su tunda direbansu ya wuce. Su Amina Hamza da su Jamila A Ramalan sukace suma za su je. Salma kuwa ta ja su suka je, ta yi musu girki suka ci, suka sha hirarsu har suna tambayarta wai nan sashenta ne ita daya sai ka ce wata matar aure?

Salma ta ce, ai yayanta yana ji da ita,

"Ni yayan nata ne ma wallahi ya yi min, akwai aji

Salma dai ta bi su a haka, kowa ta nufi gidansu,

Salma kuwa direbar,u ya zo ya dibe su da kannanta.

Aliya aikin rana gare ta, tana gida lokacin, nan ko ta kira Shatima a waya ta ce, ga Salma nan ta debo zugar " yan makarantarsu sunzo suna ta yi wa mutane hauka. Nan ko Shatima ya cika dam, don in har Aliya ta fada mishi magana tamkar wahayi ba ya bincike. Ya kira lambar Salma a kashe, bai san ta yi wata ba ta da waya ba. Domin wayarta da Baban Nafisa ya sai mata ce kuma ta samu matsala.

Yana dawowa dakin Salma ya nuta, tana zaune tana yanke farce. Ya fado tare da sallama. Cikin tsoro

Salma ta dube shi, tareda amsa sallamar.

Yace, "Wane zugar yaran ki ka debo min zuwa gida yau?"

Ta zaro ido, cikin rawar baki tace

"Salma ce fa da Kannenta.

Ya katse ta,
Chapter 13 · 0% Book details