← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka ta fara min,ni kuwa naje na zaunar da ita a kan gado ina kallonta,domin ni sha'awa take bani yadda take kukan dan ji nake dama nice na samu damar zubar da hawaye.

Ganin batada alamar tsayawa da kukan yasa na fara rarrashinta.
Daqar tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya.

Sis ina kk shiga inata nemanki,kuma kinsan a halin danake ciku ina buqatarki a kusa dani?"nace ina qarasa goge mata hawayen fuskarta.

Kiyi hqr sis,bama nan ne sai dazu muka dawo,kuma danaje gidan ammi tace kuna asibiti"

Eh muna nan tun ranar alhamis,amma ina kukaje?"

Muna asibiti ne ya sadiq bashida lpy,wai ciwon zcy ne ya kamashi,yanata aman jini,shine uncle dinmu yace kawai a fitar dashi abroad,to jiya da dare suka tashi mukuma yau da safe muka taho"

Ciwon zcy?nusaiba ciwon zcy fa?meyasa ni bai kamani ba sai ya sadiq?Nusaiba dan allah ki kaini wajenshi naganshi"nace ina girgizata.

A yanxu sis ya sadiq ya mana nisa,yana buqatar nisanta da duk wani abu dazai daga masa hankali,kuma a matsayinki na matar wani a yanxu inaso mubar mgnr wani daban"

Matar wani?waye ya fada miki ni matar wani ce a yanxu?"

Naje gida mana ammi tace jiya da safe an daura aurenki,ko kina nufin baki sani ba??

Shiru nayi dan bani da abin cewa.
Yanxu ina gadon asibitinma baza'a hqr da wannan qaddararran auren ba?wai me nayiwa abbi da zafi haka harya tsane ni?

Amminma cewa tayi Abbin yace anjima za'a kaiki wai kya qarasa jinyar acan,shiyasa ma na taho dan muyi sallama"

Anjima za'a kaini?Lallai abin na abbi ya girmama.

Sannan ya sadiq yace na fada miki dan allah ki maida hankali akan krtnki danki cika masa burinsa,a lkcn baya iya mgn sai a paper ya samu ya rubuta min"nusaiba ta kuma cewa.

Wayyo nusaiba ina akeso na saka kaina?krtnma an hanani birinsu na mutu kawai.ni dama nasan na rasa komai tunda na rasa ya sadiq"

Kibar fadar haka khadija,dama allah yayi bazaki cika masa burin ba"

Amma nusaiba rashin adalcin....

Ya isa dan allah khadija,ba kowani mgn ake fada a irin wannan al'amarin ba,bamusan abinda allah ya boye ba"

Haka nusaiba taita tausata da dadadan kalamai har lkcn da ya aisha ta dawo,bata wani jima ba ta tafi wanda sai lkcn na samu hawaye suka zubomin.
💙💙RABON KWADO....💙💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

🅿51-🅿55

Nayi nisa a tunani naji alamun tafiya.ban dago ba dan bana buqatar ganin ko waye.

Sannunki da zuwa 'yata,ya kuma kk zauna a qasa kamar wata baquwa?"

Saurin dagowa nayi dan jin muryar mace.
Kallo daya zakayi mata ka gano tsantsar kamar da sukeyi da mijin ya fatima🙁.
Kana ganinta kaga cikakkiyar mace mai kamala,wadda ta jiqu da naira.
Katse tunanin nayi na fara gaisheta ganin tana ta sakarmin murmushi.

Lpy lou,ya jikin naki?"

Da sauqi"nace ina tunanin ina tasan banida lpy.

Ai inata son xuwa dubaki to allah bai nufa ba,ya hqrinmu na rashin fatima?"

Alhmdllh"nace idona na kayo ruwa.
Da gudu shahida tazo ta hau kaina.

Aunty wai grandy tace tare zamuje gidanmu dake,kina dafa mana abinci,ki shirya mu mu tafi scul kamar yadda momy take mana?"
Daga mata kai kawai nayi.

Amma ke bazaki tafi ba kamar yadda momy ta tafi koh?"nan ma daga mata kai nayi.
Zata kuma watson wata tmbyr matar tace da ita.

Ya isa haka,kibarta ta huta bakiga bata da lpy ba?"

Tashi tayi ta koma can gefe ita a dole taji haushi.
Sai lkcn daddyn nasu ya fito yana riqe da hannun iman sai shahid a bayansa.neman guri sukayi suka zauna inda iman tazo ta hau kaina ta zauna.

Kai bakaga auntynku ba bazaka gaida ita ba"tace tana kallon shahid dake game abinsa.

Baiyi mgn ba saima tashi da yayi ya koma inda ya fito.

Tasamu a gaba tayi taita nasiha,nidai inaji ne kawai amma hankali yanaga yadda zan fara rayuwa a gidan ya fatima a matsayin matar mijinta,da kuma yadda zan rayu da mutumin da natsana ya tsaneni.Ammi zanyi qoqari wajen ganin nayi duk abinda nasan baza'a samu matsala a wajena na.

To ummi xamu wuce dare yanayi"ya fada yana miqewa tare da duba agogon dake tsintsiyar hannunsa.

Ka daiji abinda na fada maka koh babanah?banason wani abu ya fara daga gareka dan nasanka sarai"

Insha allah ummi bari muje"yace yanayin gaba.

To 'yata Allah ya tsare hanya ya qara sauqi.Ki kula sosai kinji?su kuma yaran za'a barsu anan zuwa wani satin kafin nan kin qara warwarewa"

Wayyo allah!!yanxu mu kadai zamu tafi salonma ya kasheni a hanya?yanxu taya zan fara rayuwa daga ni sai shi a cikin gida?
Miqon ledar datayi yasa na dago tare da qaqalo murmushi.

Nagode ummi saida safe"

Har harabar gidan ta rakoni inda shi tuni ya shige mota.

Ganin a backseat nazo hakan yasa yanxuma na bude nayi zama na a ciki.

Munfi mintuna biyar a wajen bamu tafi ba,nidai bansan dalili ba.

Wlh idan baki dawo gaba ba zaki fitar min a mota sai dai ki taho da kanki"najiyo muryarsa.

Ikon allah!shi matar tasa ta mutu ma bazai saduda ba?
Budewa nayi na shiga gaban batare dana kalleshi ba,dan ko kallonsa banason yi.

Kin zata kin kai matsayin da zan zama driver dinki ne?to kisani ko a mafarki hakan bazata kasance ba,idiot kawai"

Kalmar idiot din ce kawai ta bani haushi amma sauran maganganun ko a jikina,dama ni bana kai kaina inda allah bai kaini ba.

Haka na cigaba da tunani har na fara bacci.har mukaje ban sani ba,dan mugunta maimakon ya tasheni shine ya bugamin kai da jikin motar.

A firgice na tashi dan naji zafi sosai,shi kuwa ficewarsa yayi ya barni.
Haka na fito ina sosa gurin ina binsa a baya.
Bangarensa ya shige ya barni a nan,ganin tsayuwa bazata yimin ba yasa na nufi bangaren ya fatima.

Falon yananan kamar yadda nasanshi sai dai wasu canje canje da ba'a rasa ba kamarsu labulaye da sauransu.

Kai tsaye bedroom din na shige dan sosai nake a gajiye.
Danayi shirin baccin kuma sai na kasa na shiga tunanin rayuwa.

Allah sarki ya sadiq ko yanxu a wani hali yake?Tuni idanuna suka ciko da kwalla.

Ya allah ka bawa bawan nan naka lpy,ka bashi sauki da kuma hqrn rashina.
Saukowa nayi daga bed din na nufi akwatin da naga ni dan ina tunanin itace wadda ya aisha take fada.
Wayata na shiga dubawa dan inason jin muryar ammina.
Amma abin mamaki ba waya ba dalilinta.harna hqr xan koma na kwanta sai kuma na bude aljihun akwatin.

Wata qaramar wayace wadda ake mata laqabi da keypad sabuwa dal.
Kunna wayar nayi amma ba contact ko daya,dana qara dubawa ma sai naga ba sim card dina bane wani sabone.

Allah sarki ni!!haka akeso na cigaba da rayuwa ba tareda farin ciki ba.

Number din ammi nasa da yake na hadda ce amma bata shiga ba,dole na hqr na fara dannawa ya sadiq kira duk da an sanar dani baya ma qasar.
Ba yadda banyi na tuno number din nusaiba ba amma na kasa dole na sawa zcytah hqr na koma nayi lamo kamar wata marainiya.
Ganin kwanciya bazata min ba yasa na tashi naje na dauro alwala dan kai kukana wajen ubangiji.
Sai uku saura na tashi daga sallaya dan jin barci ya fara doko sallama.

Tun daga ranar ban kuma ganin ko quda a tare dani ba,koda yaushe ni kadai kamar mayya.
Hakan yasa na qagu sati yazo dansu shahida su dawo koba komai sa runga debemin kewa kafin su tafi scul.

Tun inajin tsoron girman gidan ni kadai har na hqr na fara sabawa da zaman shiru da tunani.
💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

So much luv u my fans💞💞Allah ya bar qauna💋💋

🅿56-🅿60

A daddafe nayi sati daya a gidan nan,jina nake kamar a prison,to ko a can ai ba kai kadai kk zama ba.
Yau sati na daya a gidan amma jina nake kamar nayi shekaru,to ai koba komai mutum ma rahma ne,bareni da bansaba zaman shirun ba.

Tunda safe na tashi da dokin yau su iman zasu dawo dan haka nayi wanka na shafa mai wanda rabona dashi tun kafin rasuwar ya fatima.
wata atampa na saka sabuwa,Don naga sababbin kaya a cikin wadrob nasan aikin ammina ne ko yanuwana.

Kitchen na shiga na fara dora ruwan shinkafa wanda tunda nazo tea kawai nakesha idan naji yunwa zata halaka ni,rana daya ce nasan na dafa indomie.

Shinkafa da miya nayi lafiyayyiya wadda miyar taji kaji dan ba laifi komai na amfanin gida akwai a kitchen din kai harta kayan lambu(vegetables)friege dinsu daban,kaji ma haka.

Coslow nayi sannan na hada pineapple juice.Dinning nakai na jefe sannan na zauna zaman jiran tsammani wanda yafi kama dana gawon shanu,domin har la'asar basu ba dalilinsu.

Bedroom din na koma na dauko wannan akwalar wayar wadda tafi kama da calculator,dan ganinta ma bata min rai yake tunda batada wani amfani.Ba contact bare memory shiyasa tun a ranar na kashe na jefa akwatin.sai yau dana dauko na kunna gidan radion da ya sadiq yake ko xanji wani abu game dashi.

Dakinsu shahida na shiga na gyara kafin na dibo wasu kayan nasu na kayo cikin wadrob din bedroom din ya fatima,dan idan suka dawo bazan bari suna kwana su kadai ba,koba komai nima na riqa jin motsin mutum a kusa dani.

Tsaf na gyara dakin tare da saka room freshner sannan na rufo.
Dakin oga shahid na shida dan duka dakunan a jere suke sai qaton falo a tsakiya tare da dinning area.irin dai wanda ake cewa mu hadu a falo.

Dakin kaca kaca yake da takardu ga kayansa da suke bar baje a qasa.haka nabi na tattara na gyara sannan na fito nayi alwala dan magriba tayi.

Har akayi issha babu su hakan yasa na cire raina a yau zasu dawo.
Har na fara gyangyadi akan sallaya naji an fado kaina.

Momy au aunty mun dawo"

Ai nayi fishi tun dazu inata jiranku bakuxo ba"nace ina juya baya.

To ba daddy ne yaqi zuwa da wuri ba muma mukaita jiransa"Shahida tace.

To naji ya ummin take?"

Lpy lou,tace wai mu gaida ke kuma duk abinda kk ce muyi mu ringa yi kema momynmu ce.wai haka aunty?"

Eh mn kuda baku sani ba?ba kuga da momynku tana nan ba idan kukace ayi muku abu tana cewa ga babarku can kuje gurinta?"
Chapter 9 · 0% Book details