← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan baki idan kinxo gida"nace ina fita daga dakin.
Har bakin get ta rakoni,ai kuwa muka ci karo da ya sadiq dina🙊🙈.
Da gudu nusaeba ta koma ni kuwa nayi kasaqe.

Khadija!!"naji yace a hankali

Daqar na samu kalmar Na'am ta fito a bakina.

🥰Khayratie Er mutan Ungogo😘
💙💙 RABON KWADO...💙💙

NA ER MUTAN UNGOGO🥰

🅿16-🅿20

"Meyasa bakyajin mgn?
Dagowa nayi na kalleshi dan bansan rashin jin da nayi ba.

Banaso nasa mutum abu ya qiyi kinji?daga yau idan nace kiyi abu ki ringa yi,ko kinaso muyi fada?
Girgixa kai kawai nayi ina tuna me yasa ni banyi ba.

"Jiya banji dadin abinda kikai min ba,nace ki shigo kk qi"

"Kayi hqr"nace ina satar kallonsa.

"Ni dama banyi fishi ba,kinsan meyasa?"
Qara girgixa kai nayi.

"Sbd bazan iya fishi dake ba"
Shuru nayi dan gaba daya na kasa gano ma'anar mgnr.

"Idan kin gama school me kk son xama?"ua katsen tunani.

"Inason zama zama doctor"

"Aa khadija ba doctor xaki zama ba,kinsan me nakeson ki xama?"
Girgixa kai nayi.
"Inaso ki zama lawyer,nayi miki alqawarin baki gudummawa da goyon vaya da aljihuna da lokacina indai kikai min alqawari zaki maida hankali kiyi krt"
Juya maganganunsa kawai nake dan naji yana mgn kamar wani abbinah.

"Koda yake gana abbi aure yake muku koh"naji ya fada

"Indai nace inason krt zai barni"
"To ki maida hankali indai kinaso mu shiryaa"

"Tom"

"Kije gida kar ammi taga kin dade"
Mamaki nake yadda sunan ammi da abbi yake radau a bakinsa.

"Ko akwai wani abu"yace dan ganin na tsaya.

"Eh,dan allah kabar nusaeba ta runga zuwa gidanmu"

"Murmushi yayi"kema zaki ringa zuwa nan gidan?"

Eh"

To zan barta ta ringa zuwa"

"Ngd"nace ina wucewa.

Ranar asabar aka daura auren ya fatima da wannan mutumin,lahadi aka kaita gidanta dake rijiyar zaki.
Sosai gidan ya daina yimin dadi sbd daga ni sai ammi dan ya zee ma ta fara zuwa wata computer school.
Hakanne yasa kusan kullum muna tare da nusaeba,idan batazo ba ni zanje.A hankali muka fara shaquwa nida ya sadiq,har takai indai a rana banganshi ba sai inji duk na damu🙁.
Hakan yasa na bashi no.din ammi duk dare muna waya ba tare data sani ba.
Ana gobe xan koma school kuwa kuka ne kawai banyi masa ba amma shagwaba ba'a mgn.
Daqar ya lallasheni mukai sallama dan saida ya nunamin indai ban maida hankali nayi krt yadda anan gaba zaiyi alfahari dani ba zai daina kulani.
Haka washegaru na tashi sukuku har abbi saida ya tmby ni koh lpy?nace masa kaina yana min ciwo.

AFTER 3YEARS

Abubawa da yawa sun faru a cikin shekaru uku,ciki kuwa harda kammala krtna na secondry,inda na dawo gida cikin dokin ganin iyayena,yanuwa,aminiyata da kuma masoyana a haqiqa wato ya sadiq.
Zuwa wannan lkc soyayya mai qarfi ta qullu a tsakanina da ya sadiq amma a gidanmu ya zainab ce kawai tasan tsakaninmu.
Ya aisha yanxu yaranta 4 biyu maza biyu mata,ya ruqayya itama yaranta 4 duk maza,sai ya fatima da take da yara 3 namiji sai mata guda biyu,ya zainab yarta daya amma allah yayi mata rasuwa,sai yanxu da take dauke da wani cikin.
Sosai nakeson yaran yanuwana kamar yadda iyayensu suke sona,amma wani abinda zai bawa mai krt mamaki har yanxu bama ga maciji da mijin yaya fatima,shiyasa da wuya idan nazo hutu naje gidanta,tun tana fishi dani harta bari ganin abin nawa bana qarewa bane.Ammi har abbi ta fadawa shima yayi min nasiha akan riqo nidai na bishi da to amma banajin wata ma'amala xata shiga tsakaninmu dashi.
Gama mkrnt ta yasa ya aisha ta siyamin waya mai kyau da tsada,ya ruqayya ta bada kudi a saka ni a mkrntr koyan girki da kuma kwalliya,ya fatima baiwar allah dinkuna tayimin wajen kala bakwai,Inda ya zainab ta siyamin kayan kwalliya dana shafa.
Gsky ni yar gata ce shiyasa a kowani lkc nake alfahari da yanuwana duk da kasancewarsu mata amma suna qoqarin yimin abinda koda yanuwa maza gare ni ba lallai suyi min haka ba.

Zuwa yanxu tsantsar kyauna ya qara fitowa,duk da kasancewata baqa amma inada wani kyau na ban mamaki,inada gashina dai dai na zaman falo,sannan ni bamai qiba bace,doguwace ni mai dogon hanci sannan inada beauty point a kumatuna,kai na taqaice muku dai ni mai kyau ce kawai😉.
Wayar da nayi yasa muka bude sabon babin soyayya nida ya sadiq,abinda yake qara min qaunar ya sadiq shine yadda yake bani kwarin gwiwa akan karatu,ya damu da krt na sosai dan lkcn da zamu fara SSCE kamar shi zaiyi exam din duk ya damu,kullum cikin nasiha da qarfafa gwiwa,dan yace sai yaga na fara krt a university sannan zai kai mgnr mu gaban abbi.
Cikin ikon allah na mayar da hankali na akan koyan kwalliya da girki dan naga yanxu sune mace duk wadda bata iyasu ba ita ce baya.
Yauma kwance nake a kan katifar dakinmu ina waya da ya sadiq ammi ta dago labule.

"Sannu daddawar daka,ni bansan yaushe kk koyi zaman daki ba mutum ma ya rasa abinda kikeyi a daki"
Janye wayar nayi a kunne na kafin nace.

"kaii ammi ni maixan qulla baki sani va"

Kya dai ji dashi idan tayi wari ai xamuji,ki tashi ki damawa abbinku fura nasan yanxu yana hanya"
Da to na bita,saeda ta fita mukai sallama dashi na tafi yin aikin.

Kwana biyu abbi yayi tpy qauyensu ziyara,kadaici ya isheni na shirya na tafi gidan ya Aisha.
Sosai muke hira inda yaranta suka baibaye ni kamar su maidani ciki.
Babbar itace muhibba yanxu shekararsa 6,sai Ammar,hanif sai kuma Hudallahi.

"Wai bazaku qyaleta ta huta bane ba muhibba?kuyita damun mutane kamar xaku shige cikinsa"ya aisha tace ganin yadda suka tarusuna sukuwa a kaina.

"Qyalesu yaya ai nama fasa kwana tunda basa jin mgn"
Da sauri suka sauka kowa ya nutsu dan anaso na kwana.
Kwana biyu nayi niyyar yi amma washegari nace ni gida zan tafi na baro ammina ita kadai.

"Ai dayake wani abune xai cinyeta ko kuma ke inkinje wani abu xatayi miki"ya aisha tace

"Yaya baxaki gane ba,ita uwa dadine da ita,jina nake kamar na shekara bama tare duk da dazu munyi waya,kuma nusaiba tace tanason gani na da lbr"

"Oho kudai kuka sani,dan ba tun yau ba nasan akwai abinda kuke qullawa dake da nusaiban"

"Wlh ba abinda muke qullawa sai alkhairi"nace ina ninke kayan dana cire xan shiga wanka.

"Oho dae idan tayi wani maji"tace tana fita a dakin.
Sai yamma na baro unguwar,kamar kullum saida muka sha dabi da yaran sannan na taho,wai kowa sai ya bini,wayyo ni uwar yara😜.
Tun dana sauka a titi wani yake bina a baya,ina sane dashi,qara sauri kawai nayi dan banaso ya biyoni cikin layinmu dan yau juma'a nasan yanxu ya sadiq yana gida kar ya jamin fishin sahibil qalb😝.

Assalamu alaikum"najiyo sallamarsa a baya na.
Saida na runtse idona kafin na amsa sallamar,dan banso ya min mgn ba dan mun kusa da gidansu ya sadiq.

"Baiwar allah idan baxaki damuba ba ki bani mintina biyu muyi mgn"
Banyi mgn ba dan sallamarma nasan muhummancinta shiyasa ba amsa,gashi hankalina yana kan qofar gidansu ya sadiq dan ban manta marin da nasha shekaru biyu da suka wuce ba agunsa,akan wasusun biyomu nida nusaiba munje gidan wata qawarmu.
A lkcn harna koma mkrnt ban qara ganin dariyar ya sadiq ba,a lkcn muka fara ganowa sona yake dan alamu duk sun bayyana.
Ganin har lkcn mutumin nan bina yake yasa na tsaya dan neman maslaha.

"Dan allah bawan allah kayi hqr,wlh an kusa bikina kuma babanmu idan ya ganni dakai dukana zaiyi"

"To shikenan yanmata na gode,yaushe ne bikin sai nazo idan an gayyace ni"

Murmushi kawai nayi wanda yayi dai dai ta qarasowar ya sadiq inda muke tsaye,kallon da yayimin kawai yasa nasha jinin jikina.Wucewa yayi dama akan lifan dinsa yake da dukkan alamu daga wajen aiki yake dan a gidan radio yake aiki kasancewarshi dan jarida.
Ban kuma bita kan wannan mutumin ba nayi gaba dan duk shiya jamin nasan halin ya sadiq da kishi amma saiya wayence wai karatu karatu,wai na daena kula kowa inba haka ba zan samu rauni a krt na kuma daga baya yaxo ya kasheni da kalaman soyayya😄.

Daga lkcn xuwa dare nayi masa missed calls sunyi goma,hakan ya bani tabbacin na taro march.
Da wuri nayi bacci dan yau ba abokin hirar.nusaiba na kira itama swich off dan haka baccin takaici ne ya daukeni.
💙💙 RABON KWADO..💙💙

Na Er mutan ungogo💋💋

Luv u oll Readers❤❤❤

💙💙RABON KWADO...💙💙💙

💋💋Er mutan ungogo💋💋💋

🅿21-🅿25

Washegari ma haka naita kiran ya sadiq wayar a kashe,duk sai naji ba dadi duk da allah ya sani ba laifina bane.
Wayar nusaiba na kira dan samun mafita kasancewarta abar shawaratah.

Hello sis"najiyo muryarta daga can bangaren.

Naam sis kin tashi lpy?"

Lpy lau,yadae najiki haka?"

Sis ya sadiq ne ke wahalar da zuciyata"

Hhhh,me kuma ya faru?"

Labarin abinda ya faru na shiga bata.

Tab!ashe kece kk jamin yau akaqi amsa gaisuwata"

Dan allah da gsk?wayyo ni ya zanyi?"

Kawai ki shareshi malama idan ya gama fishin nasa ya sauko,mutum yaita wani abu sai kace mijinki?"

Aa sis kar miyi haka dake,kishi pa halak ne,nasan nice mai laifi dan haka dole sai na bashi hqr"

Kedai kk sani"

Au haka ma xakice koh?"

Allah kuwa sis wani lokacin kamar a dakeki,ki qyaleshi dan allah kepa mace ce allurar cikin ruwa mai rabo ka dauka"

Kinga ni shawara na kiraki ki bani ba wani qarin bayani ba,in kuma baxan samu ba nayi gaba"

Maida wuqar to,yanxu ya kk so ayi"

Inaso ki tayani bawa ya sadiq hqr har mu shawo kansa"

Tom xan gwada na gani"

Haka mukai sallama na ajiye wayar na shiga aikin gida,amma xuciyata duk a jagule.

Har dare ba wani canji dan ya kunna wayar amma yaqi amsa kiran.
Dan dole na hqr,amma xuwa yanxu na fara fusata akan lamarin,Taya zanta kiransa yaqi dagawa,dole nabi shawarar nusaiba na qyaleshi har lkcn da xai sakko.
Haka na cigaba da harkokina dukda xuciyata ta kasa jure rashin ya sadiq amma haka naita dauriya,qarshe dai na yanke shawarar barin unguwar gaba daya.

Inason xuwa gidan ya fatima amma wannan mijinnata mai baqar zcy shine banson gani.dan hk gidan ya ruqayya nace zanje.
Chapter 3 · 0% Book details