← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga yau banaso na qara zuwa nace ki tashi mu tafi,idan kunne yaji...."yace tare da sakin hannuna yayi gaba.

To meye hakan?yana nufin a part dinsa zan ringa kwana?Wayyo ni hadiza naga ta kaina🙆

Masu bibiyar littafin RABON KWADO..💙💙
Muna gdy,da fata za'ayi mana afuwa na rashin yin typing na kwanaki,hakan ya faru sakamakon rashin lkc da bana samu,amma insha allah zan ringa qoqari inayi ko da babu yawa.ngd

Sannan akwai mistake na page number da nayi zansa 101-105 nasa 111-115 ina fatan za'amin afuwa.

Er mutan ungogon ce dai💋💋💋💋💋
[07-23, 20:48] Sistoh: 💙💙RABON KWADO...💙💙

11:02] 🍭Rukiey🍭: 💙💙RABON KWADO💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿111-🅿115

Ganin tsayuwar bazata amfaneni ba yasa naja qafafuwa na nabi bayanshi,duk da shi tuni ya shige abinsa.

Hannuwana na rawa na dorasu akan handle din qofar.

Kamar barauniya nake sanda a makeken falon,wanda haduwarsa ma baki bazai iya fada ba.

Duk wani abu dake cikin falon white and pink ne.kasancewar yaune ranar dana fara shigowa bangaren sai na rasa inda zan dosa.

Qofofine guda biyu suna fuskantar juna,nidai gudun kar nayi laifi yasa na nemi daya daga cikin kujerun falon na kwanta.

Ban dauki lkc ba bacci yayi gaba dani.

Jin sanyi na shigata ta ko ina yasa na bude idona.

Duhu ne sosai har bana iya ganin komai,hkn yasa na shiga lalube ko zan samu abinda zan lullube jikina dan jin sauqin sanyin.

Jin abu mai laushi wanda nafi tunanin bargo ne hakan yasa banyi tunanin komai ba na shiga ciki tare da komawa bacci dan sosai naji sanyin ya ragu.

A firgice na tashi jin an ja minin gashi kamar za'a cire shi.

Duk da zafin da nakeji hakan bai hanani tsorata ba dan ganina kwance jikin daddyn shahid.

Qara jan gashin yayi wanda na saki qara tare da hawayen azaba dan da mugunta yake jan gashin.gashi ya hanani sauka daga kanshi.

Kuka nake sosai dan azaba jinake kamar kaina zai cire dan jan gashin yake kamar yanajan igiya.

Tun ina kuka mai sauti har wahala tasa bana iya qara sai dai hawayen dake zuba kamar fanfo.

Inaso kisan bakin rijiya ba wajen wasan yara bane,sbd nace kixo dakina ki kwana har hakan zaisa qaramar kwakwalwarki tayi miki wani gurbatatten tunani?To ki canja tunani kuma ki saka a ranki nafi qarfinki har abada,useless kawai"ya fada tareda ture ni ya tashi.

Ruf da ciki nayi inajin zafi da zugin da kaina yakeyi.

Ba bata lkc zazzabi ya rufeni wanda ko hannuna bana iya dagawa.

Cikin ikon Allah zazzabin ya sauka sai dai kan ne da har lkcn yake sarawa.

Agogon dake bedside drower na kalla wanda ya nuna 12:04

Lallabawa nayi na kashi dan ko sallar asuba ban samu nayi ba.

To nida na kwanta a kujera waye ya kawoni gado?tunanin da nakeyi kenan ina fitowa daga bedroom din.

Yana zaune a qasan rugs yana danna computer tare da kurbar wani abu a kofi.

Kallo daya nayi masa na dauke kaina dan babu riga a jikinsa,daga shi sai sai gajeren wando.

Wani haushi da tsanarsa ce ta qara huruwa a raina,dan ba makawa tsanar da yakemin ta ninka wanda nake masa.

Zo nan"

Yi nayi kamar banjishi ba nayi ficewata.

Mubina har lkcn bacci take,dan haka wanka nayo da brush,kafin na gabatar da sallah.

Akan sallayar na kwanta cikin qanqanin lkc bacci ya daukeni.

Sai 2 na harka inda nayi alwala na gabatar da sallar azahar don lkcn mubina bata dakin.

Gadon na hau ina shirin kwanciya ta shigo.

Sannu matar broh ashe kin tashi"tace tana qarasowa inda nake.

Ya jikin?"tace tana dafa goshina.

Waya fada mk banda lpy?"nace ina kallonta.

Hararar wasa tayi min.

Tun dazu ai mijinki yazo ya tasheni,wai na hada breakfast baki da lpy,to tun dazu na gama yace karna tasheki na bari ki tashi da kanki wai baki samu kinyi bacci da dare ba"

Munafikin Allah ta'ala!

Na fada ina qara jaddada kwarewarsa wajen iya Tsara zance.

Ki tashi muje kiyi breakfast don amanarki ya bani yace inda hali ko quda karna bari ya tabaki,baki gani ba duk ya damu daqar ya fita ma"

Takaici bai barni nayi mgn ba.jin ya fita yasa natashi muka fita nayi b/fast din.

Magani ta kwaso wai yace idan na tashi ta bani nasha.haka na karba nasha dan nasan ni kaina ina buqatar mgnin.

Falon muka fita inda ta dauki wayata wai tana buden watsap.

Nida ba contact ba ai bazanji dadin watsap din ba"nace ina dora kaina a kan cinyarta.

Yanxu kuwa zakiyi contact yammata,dan har grp zan sakaki na matan aure,kinsan muma mun kusa shiga daga ciki sai kana leqa irin wadannan grps din kana koyon abubuwa,harna hausa novels ma"

To ni inaga lkcn karatun novels mubina?"

Duk da haka dai zan sakaki,idan kin sallami mijinki da yaranki ai saiki ringa karantawa"

Nidai shiru nayi mata.

Wai naga number din aunty anisa ce kawai a ciki kota ya abdul babu"tace tana kallona.

Sabon sim ne,wancen daddynsu shahid ya kwace tun farkon xuwa na"nayi mata qarya don bansan mezance mata ba,dan ko number iyayena da yayyena ai a gani a wayar.

Wlh ya burgeni,shiyasa nake qarason broh sbd ya iya tattalin mace,muma allah yasa mazajenmu irinshi ne"

Murmushi nayi kawai.

Wai har yanxu daddyn shahid kk fada masa?gsky ya kamata ki canja masa suna kinsan yayan namu dan soyayya ne,bakiga har wani jan sunanki yake ba wai nernahh"

Dariya kawai nayi.

Allah da gsk khadija kidan samo masa irin sunan soyayyar nan,bakiji aunty fatima hayaty take ce masa ba?koni da bamuyi aure da fahad ba Baby nake ce masa"

Sosai ta bani dariya.

Wai yaushe ne wannan bikin ne?"nace ina dariya.

Saura 2 months"

Kice zamusha biki"

Sosai ma"

Duka muka dago muna amsa sallamarsa.

A hankali na koma na kwanta inda mubina tace.

Broh mantuwa kayi ne?"

Aa mubina,kawai dai na kasa nutsuwa ne kinsan nabar nernah ba lpy shiyasa na haqura da meeting din kawai"yace yana tsugunnawa tare da dafa goshi na.

Nernahna ya jikin naki?"yace yana langwabar da kai kamar qaramin yaro.

Mai karatu idan ke ce wace irin amsa zaki bashi❓❓

A kafta!

Yawan comment yawan posting😉

: 💙💙RABON KWADO💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿116-🅿120

Shiru kawai nayi batare dana ce komai ba.

Mubina taci abincin kuwa?"yace yana kallon mubina har lkcn hannunsa na goshina.

Taci amma kadan,har magani na bata"

That's gud"yace yana dawo da kallonsa kaina.

Kimin mgn mana soulmate kona samu na koma office,aiki ne dani sosai na baroshi na dawo duk sbd ke,amma ko swt voice din ma baza'a barni naji ba?"yace kamar abin tausayi.

Hada ido mukayi da mubina inda tayi min mgn da ido,duk da ban gane mai tace ba nasan tanaso nayi mgn ne.

Nifa naji sauqi kawai dai banajin qarfin jikina ne"nace ina qasa da idona dan ya zubamin idonunsa masu kama dana mage.

To ko asibiti zamuje?nifa wannan zazzabin daren ya fara damuna nernah,gashi sai wata rama kikeyi wani sai yayi zaton bana baki kulawa ne"yace yana satar kallon mubina.

Wlh munafiki ma wutarshi daban take"na ayyana a raina.

Gsky yaya kawai kuje asibitin,ka sani ma ko za'a yiwa su iman qani ne?"tace tana dariya.

A tare muka kalli juna inda nayi saurin dauke idona.
Wai ita wannan bakinta baya tantance mgnr da zai ringa fada ne?ko duk cikin shirin aunty anisa ne dan tace zasuyi waya da mubina?

Wai haka nernah?"yace yana shafan kumatu.

Yaqe kawai nayi.

Hhhh ai yaya ita ta sani akwai kawai dai bazata fada bane,barima na kira ummi dan na riga kowa samun gift wlh"tace tanayin dakina da gudu.

Nashi uku🙆🏻🙆🏻mubina nada hankali kuwa?

Hancina daya ja yasa nayi saurin dagowa.

Fuskarsa a hade ya zubamin ido.

idan ma keci kk sanar da ita wannan shirmen ki gaggauta fada mata ba haka bane,idan kuwa kika bari ummi taji zaki gane kuskuran da kk aikata"

Nifa ba abinda na fada mata"nace kaina a qasa.

Kedai kk.....

Eh wlh ummi gata ma"muka jiyo muryar mubina tana qarasowa.

A kunne ta kara min wayar inda najiyo amon muryar ummi.

Cikin ladabi na gaida ita,ta amsa cikin sakin fuska.

Yanxu nakejin abin farin ciki wajen mubina,to allah ya raba lpy kuma ki kula sosai kinji?,da zuwa gobe nace za'a dawo da yaran amma za'a barsu zuwa wani lkc kafin ki qara warwarewa"

Tom ummi ngd"na fada kaina a daure ga wani kallo da daddynsu shahid yake jipana dashi.

Ina baban nawa mubina tace kuna tare?"ummi tace.

Eh ummi gashi nace ina miqa masa wayar.

Tashi yayi ya nufi bangarenshi,suna mgn da ummin.

Maida kallona nayi kan mubina.

Yanxu dan allah ke waya fada miki ciki ne dani da zaki fara yadawa mutane?to ko cikin ne dani sai ki fara buga waya kina fada?"nace ina hade rai.

Hhhh lallai ma ke dinnan,to ki rantse ba cikine dake ba.ni kinga burina ya cika ummi tace naje company na zabi mota dama abinda nakeso kenan dan na qagu na fara driving da kaina dama mijinki ne ya hana mu"tace tana tsallen murna ita ko a jikinta.

Takaici yasa ya tashi nayi daki dan wani qululu nakeji a zcytah,gashi shi wancan mutumin ya dauka ko sanshi nake dazanje na fadawa wani ciki ne dani.allah ma ya rabani da daukan cikinsa😔.

Shiga ta daki yayi dai dai da qarar wayata dake ajiye akan mirrow.

"Sis mufyderh" naga yana yawo akan screen din,wanda ba makawa na gano mufida ce dan nafi zaton mubina ce tasa min number din.

Hello momyn twins"najiyo muryarta.

Wayyo allah wlh mubina ta gama cuta ta.

Ko cikinne ya fara hanaki mgn?"na qara jiyota,keda kinji kinsan cikin nishadi take mgn.

Wai waya fada miki ciki ne dani"

Hhh radio mai jinin gidanki mana,ni kinga ma hada kaya nake dan nima tahowa zanyi ayi rainon cikin nan dani kafin hutun semester ya qare"

To allah ya kawo ki"nace ina ajiye wayar dan da alama qaramin ciwon kan xasuyi idan suka hadu.

"Aunty anisa"

Shine sunan daya qara shigowa cikin wayar.

Jikina a salube na daga tare da sallama.

Aunty khadija manyan qasa"tace bayan ta amsa sallamar.

Aunty kinga mubina sai yadani take wai ciki gareni"nace kamar zanyi kuka.

Dariya ta saka.

Ai ni wlh ta burgeni,wannan ma wata hanya ce mai kyau"

Kenan aunty da hadin bakinki?"nace da mamaki.

Ko kadan khadija,kindai sai halin mubina ni bama muyi wannan xancen da ita ba"
Chapter 18 · 0% Book details