← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toilet din na shige na barshi a wajen.dana fito baya dakin dan haka na qara kwanciya dan naji dadi daya fita.

Aunty!Aunty ki tashi mun dawo"kamar a mafarki naji ana fada ina bude ido naga iman.

Oyoyo"nace ina bude mata hannu inda ta fado jikina tana dariya.

Aunty tun dazu muka zo daddy yace kina bacci,shine grandy tace wai zaki haifa mana baby mai kyau koh?"

Murmushi nayi.

Ita grandy dince tace hk?"

Eh kuma dama frndz dina a scul duk suna da baby a gidansu"

To ai kece babynmu anan gidan"

shigowarsa yasa ta tashi da gudu tayi hugging dinsa.

Daddy wai aunty tace zata haifa mana baby mai kyau,nima nacewa frndx dina muna da baby a gidanmu"

Riqe hannunta yayi kafin su qaraso.

Kice mun kusa yin baby koh amminah?"yace yana zama a gefen gado.
[07-26, 19:42] Cwt-besty: 💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutanen ungogo💋💋💋💋

🅿131-🅿135

Eh daddy kuma zan ringa goyata kullum koh?"

To idan Amminah bata goyata ba waye zai goyata?"yace yana jan habarta.

Murna take sosai inda ya dawo da kallonsa kaina.

Kiyi qoqarin kawo baby nan sbd kowa ya huta,domin ga kakarsa can ma ta doko sammako dan taga lpyr jikanta"

Lallai ma mutumin nan.na fada a raina.

Hade rai nayi na ciri mayafin kan iman na daura a kaina kafin na tashi na bar musu dakin.

inaji suka biyoni a baya nidai na fito inda na samu ummi dasu mufida duka a falon.

Shahida ce ta taso da gudu inda shahid ya tsaya yana murmushi.

Aunty ina babyn da zaki haifa mana?"

Duka suka saka dariya,nidai janyeta nayi daga jikina na qarasa na kwashi gaisuwa a wajen ummi.

Sai kika gammu da sassafe,wlh fitinar yaran nan yawa ne da ita ko b/fast ba'ayi ba aka dameni baby baby nidai nace a zo muje a ga wannan baby a huta"

Murmushi kawai nayi.

Ganin anata hira yasa na tashi naje nayi wanka na shirya kafin na fito mu fara shirin abun karyawa duk da lkc 11 ta wuce.

A saman dinning aka hadu kowa da kowa ana cin abinci,inda gogan naku ya kafa ya tsare sai wani nan nan yake dani kamar gsk,nidai kunyar ummi da yaransa duk ta cikani,dan danayi sakema abinci a baki zai bani.

Duk na takura sai wani shigemin yake yana kashe min murya.

Saida ummi ta kammala ta tashi kafin nadan fara sakewa.

To surukar taki ta tashi sai ki bude baki kice abinci"yace yana kawon kofin tea wajen bakina.

Nifa na qoshi"nace kamar na fasa ihu.

Broh kawai ka barta kasan su masu ciki ba komai sukeson ci ba,kawai ka tmbyta avinda take son ci"mubina uwar tsari tace.

Shikenan me kk so kici?"yace yana riqoni

Ni babu komai"nace ina tashi daga wajen.

Parlou din na koma na zauna muna dan taba hira da ummi.

Shiya fara dawowa falon inda ba kunya yaje ya kwanta a jikin ummi.

Tashi fa zakayi babanah dan mu tfy zamuyi,kana girma wannan dabi'ar ta son jiki taqi tabarka"

Ummi idan banyi miki ba wai wazanje nayiwa?kuma kinsan kedin kawai nake iya yiwa"yace yana qara kwanciya.

Naji tattaromin yaran nan mu wuce rana tana qatayi."

Mudai bazamu biki ba gsky"shahid yace yana kwabe baki wanda qarasowarshi kenan.

Ai kuwa saikun bini dan bazaku takuramin yarinya ba"

Ummi kawai ki barsu ai naji sauqi"nace kaina a qasa.

Kuma ummi gasu mufida zasu ringa kulawa dasu"ya fada.

To ai shikenan tunda yaranku kukeso nima sauqina ne naji shiru kwana biyu"tace tana tureshi tare da miqewa.

Duka mukayi mata rakayi har bakin mota,saida driver ya fitar dasu kafin mu dawo ciki.

Mgn ce dai guda daya akan cikin da babushi sukai tayi shi kuwa sai biye musu yakeyi,idan yasan ya fadi abinda ba haka bane saiya kalloni tare da kashen ido.

Sosai a jiya zuwa yau lamuransa suke bani mamaki dan idan yayi wani abun kamar ba shi ba.Gashi duk wannan budirin da ake yana maqale dani kamar za'a kwace masa ni.💙💙RABON KWADO....💙💙

Er mutan ungogo💋💋😊💋💋

🅿136-🅿140

Ta qarfin tsiya su mufida suka hana su shahid kirana da aunty sai dai mommy.

Tun inajin kunya da nauyin amsawa har nazo ina amsawa,shi kanshi gogan naku ya goyi bayan haka.

Wata irin kulawa nake samu ta musamman daga gareshi wadda na kasa tantance ta gsky ce ko kuwa shirin film ne.

Yanxu ko mu kadai ne a guri wannan kulawar tananan,yaita wani nan nan dani,ni kuwa na samu waje sai shagwaba,muyita narkewa juna dan shi kanshi zakusha mamakin yadda yake sakin jiki yaita shagwaba,ni wani lkcn ma dariya yake bani wlh.

Tun inajin nauyi idan yanayi a gaban yaransa har na fahimci su basa daukar haka a wani abu maybe sun saba ganinshi yanayi ne.

Ta bangaren aunty anisa ma sosai take bani gudummawa sai dai abubawa da dama bana iya aikatawa dan banason na wuce gona da iri ko yaga gajen hqr na.

Yau tun yamma ciwon mara yake damuna dan hk walwalata qalilance,kawai dai ina daurewa ne domin idan ya tayar min baya min da sauqi.

shahida sai dira suke a kaina,tun ina juriya har take na turo su dama akan 3seater nake a kwance da tsautsayi iman da bige baki da jikin kujera bakinta ya fara jini.

Sosai na shiga damuwa muka hadu dasu mubina muna aikin rarrashi tunda shi tun safe ya fita wai yayi baqi a company din motar su.

Ganin taqi shiru yasa na goyata duk da azabar ciwon dake damuna har na samu tayi bacci.

Kafin ta tashi kuwa baki ya kumbura,shi kuma yana dawowa shahida ta sanar masa na fasawa iman baki.

Haka ya rufe ido ya dawo asalin daddyn shahid dinsa.

Tun su mubina suna bashi hqr har suka gaji sukai shiru domin kadan ne ya rage bai mari mufida ba da tana mayar masa da abinda ya faru.

Nidai banda kuka ba abinda nakeyi,dan haka yace so nake na kashe masa yara tunda na qona shahid yanxu kuma na fasawa iman baki.

Saida yayi mai isarsa kafin yaja yaransa zukayi part dinsa.

Rarrashina su mubina suka shigayi nidai kukana na cigaba.saida na gaji dan kaina nayi shiru.

Tsit gidan yayi kamar ba wasu halittu a ciki,dan har lkc suna part dinshi su kuma su mufida sun tasani a gaba sunyi jugum jugum.

Sister ki tashi mu fara shirya kayanmu dan gobe zamu tafi,dan yaga munxo gidanshi shine zai ringa yi mana fada"mubina tace tana nufar inda kayansu yake.

A hankali na miqe ina roqonsu da karsu tafi amma mubina tahauni da fada.

"Ai duk laifinki ne da kk bari yana miki duk abinda yaga dama,ni wlh miji bai isa duk shirginsa ya kwaso ya doramin ba,bacin kema yaran nan nakine,ki gama wahala dasu sai dan rana daya an samu matsala za'a nuna miki iyakarki"

Haka taita bambami kamar ta ari baki mudai kallonta kawai muke.

Har washegari mita takeyi,daqar ta yadda muka hada b/fast dan tana idar da sallah tayi wanka tayi shirin tpy.

Muna zaune akan dinning ya fito da yaransa biye dashi.

Mufida ce kawai ta gaidashi ita daya kusa marin ma,amma mubina kicin kicin tayi ko kallonsu batai ba.

Nima kallo daya nayi musu naci gaba da jujjuya abincina dan tun dazu na gagara ci.

Tun safe nake jina wata inconculusive jina nake kamar ina missing wani abu amma na rasa ko menene shi.

Ciki ciki ya amsa gaisuwar yace taje ta canja musu kaya dan inaga da kanshi yayi musu wanka.ni dama haka yakeyi daya ragemin wata wahalar.

Falo ya koma tare da kwalawa mubina kira.

Qasa qasa yake mgn dan hk banajin abinda yake cewa kuma nima ban damu da naji din ba tunda ba abinda ya shafeni bane.

Tattare kwanikan na farayi dan na kasa cin abinci tea din dai na dan kurba.

Tare suka fito da mufida inda ta tarkato kansu sukazo suka tsaya a kusa dani.

Mommy kiyi hqr"suka fada a tare.

Murmushi kawai nayi.

Ai bakuyimin laifi ba yaya shahid,zo nan baby naga bakin"nace ina miqawa iman hannu.

Mommy yanxuma ya daina min zafi,daddy ya sakamin mgn"tace tana riqeni.

Nima bari nayi miki addu'a sai ya kuma warkewa ko?"

Daga kai tayi,sannan nayi mata addu'a.

Hada musu abincin nayi ina basu a baki muna hirarmu kamar ba abinda ya faru.

Sis ki kaiwa yaya abincin mana"mufida ta fada.

Wlh baza'a kai masa ba,yayi mata laifi sannan itace zata bishi,kar kiyi masa mgn indai baiyi miki ba"mubina tace tana zama.

Nidai cigaba da abinda nakeyi nayi,duk da inaso na kaimasa abincin dan nasan yanxu yanajin yunwa🙁

Idan baki tashi tsaye ba wlh abinda zaiyi miki nan gaba saiya fi haka,dan yaja miki raini ma a gaban yara zai ringa yi miki fada"mubina ta cigaba.

Ganin yaran suna kallonta yasa nayi mata alama da ido tayi shiru.
Sannan ta juya akalar zancen.

Wai sister kinji roqona yake karmu tafi yau sbd ummi zata dauka wani abun ne tunda tasan ba yanxu zamu koma ba"tace tana kallon mufida.

Dama ba kece ba wai dole sai mun tafi ni dama ban shirya komawa da wuri haka ba,dan horo nake bawa Abbas"

ai mazan ne saida horo"tace tana tabe baki.

Mubina kenan mutuniyata,wai kece babba ne"nace ina dariya.

Wlh nice babba amma idan tanamin wani abu saiki dauka haifata tayi"mufida tace.

Ai kin fita sauqin kai da hqr"na kuma fada.

Mantawa kikayi ni fetir ce"

Hk muka cigaba da hira munashan dry amma rabin hankalina duk yana kan duk wani motsinsa,duk da ba gano fuskarsa nakeyi sosai ba.

Da wannan leqen ai da wajenshi kk je"mubina data gama ganoni ta rada min a kunne.

Murmushi nayi dan da gsk inason zuwa wajenshi amma bansan mezan fada masa ba🙁

Mufida ya kuma kwalawa kira.

Allah sarki wlh yunwa yakeji wai dan allah na samar masa tea"mufida tace bayan ta dawo.

Tausayinsa naji a raina,to wai dacan a ina yake cin abinci?

Wlh karki biyewa mubina taita zugaki kiqi yiwa mijinki biyayya,ki tashi kije ki kula dashi"mufida tace.

Nidai tea din na hada na barsu sunata yi kamar zasu cinye juna.

A hankali na samu gefensa na zauna tare da sallama a baki na.

Ciki ciki ya amsa dan dabadan bakinsa danake kallo ba bazansan ya amsa ba.

Ya abdul ga tea din"na tsinci kaina da fada.

Ture laptop din gabanshi yayi kafin ya kalleni.
Chapter 20 · 0% Book details