← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da rigima da komai na samu na kallama shiryasu cikin uniform dinsu,inda na nufi dakin oga shahid dan taimaka masa ya shirya dan lkc ya tafi gashi ko breakfast basuyi ba.

Haka muka fafata dashi,ko dan yaga ina cewa yai sauri ya ringa abubuwa kamar mara laka,nidai danaga ya fito a wanka na fito na qyaleshi.

Dinning mukaje na fara hadawa su shahida b/fast din dan 7:30 din harta dan gota.

Kamar kullum da tpyrsa ta taqama da isa ya shigo falon inda sai a lkcn ma nasan akwai kofa da zaka iya shiga bangarensa ta nan falon.

Tashi sukayi sukaje suka rungumeshi,kafin ya sakarwa kowa kiss a kumatu.

Good mrng my angels"naji yace yana shafa fuskokinsu.

Shahid ne ya fito nidai na hada masa nasa abincin,inda nake saqe saqe na gaisheshi ko kuwa?

Kar naje na gaidashi ya yarfa ni,kuma sai nake ganin kamar idan ban gaida shi ba ban kyauta ba.

ina kwana"nace ba tare dana kalleshi ba.

Bai amsa ba hakan yasa nayi dana sanin biyewa dayar xcyta data saka na aikata haka,gashi ya shareni kamar baisan inayi ba.

Shahid sauri fa zakayi kaga driver yana jiranku kar kuyi late"yace yana zama akan kujerar falon.
Saida shahid din ya gama suka dauko lunch-box dinsu dan tafiya,a inda shahid din ya bude dan ganin mene a ciki.

Kai kai kai!Daddy kaga abinda tayi mana,wlh ni baxanje da wannan abin ba yan class dinmu suyi min dariya"yace yana ajiye basket din nasa a gaban daddyn nasu.

Sai lkcn ya kalleni,nidai ina tsaye da plat din da suka gama cin abinci mamaki ya cika ni.
Dan yaje da faten doya shine za'ayi masa dariya?faten da na baje basirata akanshi shine akeyi masa haka?

Kuje wajen motar ganinan,duk ku ajiye baskets din"yacewa yaran.
Aikuwa ba musu suka dire suka fice.

Wato bakiji gargadin danayi miki akan kulamin da yara ba koh?to ki sani kamar yadda na fada indai kk yi laifi zan hukuntaki kamar yadda ake hukunta masu laifi to zan aiwatar da hakan,ki jira purnishment dinki kafin dare,hakan xaisa ki ringa kiyaye duk wani abu daya dangance ni da kuma yara na"

Yana gama fada yayi ficewarsa abinsa.

Guri na samu na zauna inda wasu hawayen takaici suka zubo min.Wato duk qoqarin da nayi na hana kaina bacci nayi abinda yace badan komai ba sai dan banason matsala ta fara daga bangare na amma hakan bai samu ba.Bai yaba abinda nayi musu ba duk da dama ba dan ya yaba nayi ba,amma shine zaice wani zai hukuntani.
Banga laifi na ko kadan ba,sbd bai fada min kalar abinda zanyi ba,bansan wani irin abu suke tafiya dashi ba amma da yake ya tsaneni shine zai dora laifin akaina.

Daki na koma na kwanta ina kuka,dan bacci da gajiya ke damuna amma nasan bazan iya baccin ba.

Haka na wuni sur ni daya a daki saida naji yunwa na neman kasheni na rarrafo na dauki faten da suka bari na fara ci.

Wai wannan abincin ne za'ace baza'aje scul da shi ba?to ko shugaban qasa ya samu wannan abincin ci zaiyi bare su daba yayan kowa ba.

Bayan la'asar zaman dakin ya isheni,ina fitowa falo na ganshi a kishingide.
Wlh na tsorata sosai dan banyi tunanin da mutun a gidan bama duka.

Zo nan"najiyo muryarsa cike da isa.

Can gefe na zauna ba tare dana kalleshi ba.

Kamar yadda na fada miki dazu zan hukuntaki akan lefin da kk yi,yanxu ina so kiyi abinci kala hudu da juice kala biyu,ko wanne ya kasance dai dai cin mutum goma ne,na baki nan da awa biyu idan kk wuce haka ki tabbatar gobe xakiyi wanda ya ninka hakan."

Komai na amfani akwai a kitchen,idan kuma kina buqatar wani abu zaki iya fada in babu sai a siyo."

Tofa!wata daban,da gsk aikin nazoyi kenan?
Ta inama zan fara wannan aikin har kala 4 a cikin awa biyu?kuma ma wai dai dai cin mutum goma.

Ko a gida bantaba yin girkin da mutum goma suka ci ba,amma gashi an kawo ni inda zanyi,allah sarki ni.

Kina batawa kanki lkc ne"na jiyo muryarsa.

Daki nayi ina zuwa na fada kan gado na rushe da kuka.

Abbi why?Abbi meyasa zaka kawoni inda ba'a qaunata?Abbi meyasa zaka daina sona ka hadani aure da mugu mara tausayi?
Ya sadiq kazo gareni dan allah,ina buqatarka a kusa dani,nasan da kana kusa bazaka bari a cutar dani ba....haka na ringa kuka ina surutai,saida nayi mai isata kafin na bawa zcyta hqr na yanke shawarar zuwa nayi girkin.

Tashi nayi na nufi kitchen tare da tunanin abubuwan da zan dafa masu sauqi wadanda baza su ja lokaci ba,dan yanxu ma na kusa cinye awa daya.

Haka na raba hankali na,inda na dora coconut rice akan electric,fried rice a kan cooker,sai kuma blander din kayan miya dana jona a socket,ga blander din fruit itama tana markada min abinda zanyi juice dashi.

Juice din na fara gamawa,inda nayi lemon mangwaro,sai kuma pineapple and coconut juice.

Saida na gama coconut rice din sannan na dora macaroni armlet a electric din.
Da taimakon allah na samu na gama girkin amma kala uku nayi dan bazan iyayin na hudun ba tunda ba fadar allah bace,wannan dimma da nayi nayi qoqari dan sosai na gaji danma abincimasu sauqi nayi sannan na samu kayan aiki masu sauri.

A coolers na zuba abinci,yayin da na zuba juice din a jugs naje na jera a dinning,ni har mamaki nake yadda zaiyi da wadannan abinci masu yawa haka.

A falo na wucesu nayi ciki abina dan tun dazu ina jiyo dawowarsu dan yanxu har an idar da sallar magriba,inacan ina aikin daba godi bare na gode.

Shahida ce ta biyoni.

Aunty wai meyasa bakya zama tare damu da daddy muna hira kamar yadda momy takeyi kafin ta tafi?"

Kamo hannunta nayi muka zauna a gefen gado.

"kinga shahida banason surutu kinji koh?idan kuma kinaso mu bata shikenan"

To na daina"

Yawwa babyna,kije kuyi hira dasu ya shahid kinga na gaji wanka nakeso nayi gashi banyi sallah ba"

Dana shiga toilet haka naita gasa jikina da ruwan dumi sbd rashin sabo,dan yau na aikatu ba kadan ba.

💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

🤝Still ana tare🤝

🅿66-🅿70

Ina fitowa a wanka sallah nayi na kwanta a wajen dan wani irin ciwo da jikina yake min kamar ana sassarawa.

Wai kixo inji daddy"shahid yace yana juyawa.

Zo nan"nace dan naga rainin ya fara yawa.

Can bakin qofar ya tsaya yana turo maki.

Nan nace kazo"na fada ina miqewa.

Qarasowa yayi ya tsaya a kaina.

Hannunshi na kamo na zaunar dashi inda ya shiga kokawar qwace hannun.

Naga alamar raini ya shiga tsakaninmu koh?to wlh ina qyaleka ne sbd inajin tausayinka,amma duk ranar daka kaini bango zaka gane baka da wayo,mara kunya kawai"
Sakinsa nayi na tashi na fice dan zuwa naji me kuma zanyi masa dayake kira na?

Suna baje a falon kowa da robar ice cream irin manyan nan,sai ledoji wadanda nafi tunanin nama suka gama ci a ciki.

Dinning na kalla naga wayam ba coolers din.
To ina ya kaisu?

Nace kiyi abinci cikin 2hours shine bakiga dama ba sai sanda kikayi ra'ayi koh?to gobe zakiyi dai dai cin mutane 15 sannan banasan ki kumayin kalar wanda kikayi yau,kuma zaki qarasa ragowar nayau guda daya da bakiyi ba kinga kala biyar kenan.
Ina baki shawara kiyi abinda nace idan ba haka ba kullum zaki ringa yi kuma yawansu zai rinqa qaruwa.

Kuma bawai dan kkina wannan aikin zaki qyalemin yara ba,suma nasu dawainiyar tana nan,idan kika kuma wani kuskuren shima wani hukuncin ne zai hau kanki"

Jin yayi shiru yasa na gane ya gama,dan haka naja qafata na koma inda na fito.

Yanxu shikenan ni haka rayuwata xata cigaba?koda yake banga laifinsa ba,iyayen da suka haifeni suma banxatar dani sukai bare shi.

Ko Ammi bata nemeni ba sbd wani dalili su ya aisha fa?ko sadakata aka bayar ai yaci ace ko ba'axo inda nake ba a kira aji lpytah.Amma ba komai rayuwa ce.

Aunty wai gashi inji daddy"iman ta dawo dani daga tunani.

Inason yarinyar da yawa,dan duk itace mai kama da yan gidanmu,amma sauran duk can sukayi,dadin dadawa kuma sunan amminah aka saka mata wato maryam.

Karbar ledar nayi na duba.

Wannan ice cream dince da nama a qunshe a irin takardar nan mai kyalli.
Dacan ba'ayi niyyar bani ba sai da akaga na gani sannan,to bazanci ba.

Ungo kice masa na qoshi"nace ina danqa mata ledar a hannu.

Har ta juya sai kuma wani tunani ya fadomin,ai raba arne da makami ibadah ne.

Kawo nan iman,kixo nayi miki wanka kinga gobe da scul koh?"

Batai musu ba da dawo,Ajiye ledar nayi,kafin nayi mata wanka inda mukayi sallar issha tare sannan,na dauko naci naman na dora da ice cream.
Kadan nasha dan a qoshe nake kawai dai rabar arne nayi da makami.
Kayan bacci na saka kamar yadda na sakawa iman dan da wuri nakeso muyi bicci dan nasan gobe ma da wuri zan tashi.

Harna kwanta na tuno da shahida dake can falo.
hijabi na dora akan kayan baccin jikina tare da daukan ragowar naman da ice cream sannan na fita.

Surutu take ta zuba masa inda ya tasa laptop a gaba yana latsawa.

A friege din falon na saka ledar kafin na qarasa can kusa dasu.

Baby taso muje kiyi bacci,gobe da scul"nace ina kallon game din da shahid yake bugawa a tv.

Kaima shahid tashi kaje ka kwanta game din ya isa haka"daddynsu yace yana cigaba da latse latsensa.

Nidai kama shahida nayi muka tafi dan burina kawai na kwanta na huta.

Ina dubo mata sleeping dress bayan nayi mata wanka naci karo da ledar da Ummi ta bani da mukaje gidan.
Ni gaba daya ma mantawa nayi da ita,dan ina zuwa na bude wardrob na saka ta.

Turaruka ne masu qamshi da tsada,na fesawa da kuma na wuta.
Gsky naji dadin kyautar nan,dan ni mutumce mai son qamshi shiyasa nake qara qaunar ya sadiq dan shima akwai shi da fesa turaruka masu sanyi da qamshi.

Allah sarki,ko yanxu a wani hali yake?Allah shi kadai ya sani.

Aunty wai yaushe zamuje gidan Ammi ne?ke tunda kk zo bakya kira mana Abbi muna gaisawa"shahida tace.

Uhmm shahida magana,ke wai bakya gajiya da surutu ne?"
Chapter 11 · 0% Book details