← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ilahi!!banasan damuwa.Daukan kwalli nayi na saka tare da daukan hijabin dana cire.

Ki bude jakar can akwai hijabi,bakya ganin wannan yayi datti?"

Jakar na nufa kawai dan naga abin bana qarewa bane.jin an fara kiran magriba yasa na fasa kwanciyar na tada sallah dan nayi alwala danaje wanka.

Dana idar ma zama nayi ina azkar din yammaci.sai danayi issha kafin na tashi akan sallayar.kamar jira take ta wani biqon plat din abinci.

Karba kawai nayi na fara dannawa badan inajin dadin abincin ba.

Kiyi hqr kinji auta?insha allah zakiyi alfahari da wannan auren,kinsan dai abbi yana sonki bazaiyi abinda yasan zai cutar dake ba.maganar sadiq kuma ki ajiye gefe ki rungumi mijinki da 'yay'an yaruwarki"

Surutanta taita yi dan maganarta bata min rai take.wai zanyi alfahari da wannan qaddararran auren?na rungumi mijinah?uban waye yace mijina ne?wlh na kusa fara dura ashariya tunda baza'a barni na huta ba.

Turo qofar akayi tare da sallama.Abbi ne da mijin ya fatima yana binsa a baya kamar tsohon munafiki.
Da gudu shahida da iman suka zo suka dafe ni,su kansu yaran yanxu haushinsu nakeji.
Turesu nayi a jikuna ina tsugunnawa ina gaida abbi.

Sama sama ya amsa min kafin ya fara yiwa ya aisha mgn.

Kin karbo takardar sallamar ne?"

Eh abbi na karbo"

To ita ta gama shiryawa dai koh?"

Eh ta gama"

To khadija ga mijinki nan zaku tafi,kya qarasa jinyar acan dakinki,Allah ya qara sauqi ya bada zaman lpy"yace yana kallo na.

Tirqashi!!wato ni ko irin gatan da masu gata suke dashi na sallama da mahaifiya da karbar nasiha a wajenta ni bazan samu ba?bani da gatan da za'aje gida a dauko ni sai a asibiti?wannan ua alama ce ta an gaji dani,taya ma mijin zaiga daraja ta bare kuma miji irin wannan?"

Tunani nane ya tsaya danjin ya aisha ta kama hannuna ta nufi hanyar waje dani.

A wata muta ta sakani kafin tace.

Auta kiyi hqr,nasan akwai abubawa da dama daba haka ya dace ayi ba,amma inaso ki cire komai a raki kuma ki ringa tuna waye abbi da kuma matsayinsa a wajenki.Akwai wata akwati zaku gani duk kayanki ne na buqata,sauran suna cikin wardrob,Ammi tace tana miki fatan alkhairi"

Kifa kaina nayi a cikin cinyoyi na dan ganin abbi yazo bakin motar,inaji sukai sallama dashi suka shigo cikin motar.
Dukansu a gaba suka zauna saini a baya,inajin tashin motar na sawa raina nayi bankwana ta walwala,kuma nayi dammarar karbar ko wani matsayi ne a gidan tunda hakan aka zabar min.
Shiru motar tayi sai surutun su iman da suke tayi ba qaqqautawa,shidai da eh ko a'a yake binsu dashi.

Jin motar ta tsaya yasa na tabbata ta faru ta qare.inaji duk suka fita a motar amma ban dago ba.

Malama ki fito kona janyo ki wlhnajiyo muryarsa a gefe na.

A hankali na dago kaina dan nasan zai iya aikatamin abinda yafi haka.
Saurin kare fuskata nayi dan ganin hasken daya dalle min fuska.a hankali na zuro qafata wadda na tabbatar ba gidan ya fatima muka zoba,to inane nan?Allah yasa gidan yankan kai ya kawo ni su yankani na huta.

Ganin yayi gaba ya fara tpy yasa nabi bayansa.Ganin girman gidan da qofofin da muke wucewa yasa na gasgata zargina.

Ki jirani anan"yace ba tare da ya juyo ba ya cigaba da tafiya.
Guri na samu na zauna ina tunanin inda kuma su iman sukayi dan dana fito banfansu ba.
Ganin ya dade bai dawo ba yasa nace qila ciniki ne bai fada ba.
💙💙RABON KWADO...💙💙

Written by:Er mutan ungogo💋💋💋

🅿41-🅿45

Dana koma daki ma wani sabon kukan na dasa.
Da gsk na rasa ya sadiq?da gsk ya sadiq ba RABONA bane ba?lallai duk wadda ta samu ya sadiq tafi kowa sa'a a duniya,ni kuma dana rasa shi pa?ni kuma nafi kowa rashin sa'a.

Da dai daya yayyena suka fara zuwa,inda kowacce tazo tausata take da bani hqr,abin takaicin ba wadda ta bani goyon baya a cikinsu,nidai a ganina zuwan nasu bashida wani amfani.
Haka suka tattara suka tafi ba wani cigaba,dan har lkcn naqi cin abinci kuma ban bar yin kuka ba.
A jiya zuwa yanxu harna rame,fuskata kuwa kamar an hura baloom sbd kumbura,muyarta kanta zuwa yanxu ta dashe,hawayena ne dai basu kai da qafewa ba.
Ina a kwance sallah ce kawai take tayar dani,ga wani azababben ciwon kai dake damuna.
Wayata ce ta fara neman agaji amma banyi niyyar dauka ba,dan tun rana ake ta faman kirana nasan bazata wuce yan scul dinmu ba ace banxo test ba.
Jin qarar wayar ta fara damuna yasa dole na miqe na dauko dan da alama mai kira bashida niyyar dainawa.

"Heartbeat"shine sunan da yaketa reto a saman wayar,banda niyyar daukar wayar saima tasata a gaba da nayi ina rusa kuka.
Mai zai kira ya fada min bayan yasan na rasa shi?kodai ya yarda da qudirina na guduwa ne?
Da sauri na daga wayar.Daga can naji yace"khadija!!

Naam"nace da dasasshiyar muryata.

Har yanxu bazaki bar yin kuka ba koh"

Bafa kuka nake ba"

To naji,inason qara baki hqr ne,khadija bawai dan mun rasa juna shikenan mun daina rayuwar farin ciki ba,dan allah ki saki ranki,ki bada hadinkai ayi abinnan lpy kinji?dan allah kada kiyi wani abu dazai badawa abbi rai,kindai san fishin iyaye akan yayansu"
Kuka nake kawai,dan yanxu na tabbatar na rasa shi,wlh da gsk na rasashi😭.

Kinci abinci kuwa?"
Naji yace.

Eh"

Bakici ba nasani,kuma idan kinason mu shirya ki tashi ki dauko abinci kici,idan ba haka ba kafin gobe zakiji lbrn nabar garinnan"

Dan allah karka tafi,wlh xanci"na fada ina qara sautin kuka.
Baiyi mgn ba sai tari da yake tayi tun inayi masa sannu har nayi shiru ina kuka.

Ya sadiq ka gani koh?kaga zamu cutar da kanmu sbd farin cikin wasu koh?"na fada danjin tarin ya lafa.

Dif!!ya kashe bawar ba tare da yayi mgn ba,haka naita bin number din amma bata shiga.

**-**-**-**-**-*-*

Yau ta kama Alhamis,wanda a lissafinsu abbi saura kwana biyu daurin aurenah,zuwa lkcn duk wanda ya gani saiya tausaya min,sbd na lalace kamar ba khadija yar gayu ma'abociyar san ado da kwalliya ba.
Ina zaune a tsakiyar yayyena da suketa yimin magiyar naci abinci,amma ni duk hankalina ba'a kansu yake ba,tunanin nusaiba da ya sadiq nake,dan tun ranar da mukai wayar nan banqara samunshi a waya ba,nusaiba ita kanta na kasa samunta,gashi har lkcn ban qara ganin qeyarta a gidan ba.

Khadija!khadija!!ko khadijan bata nan ne"najiyo muryar abbi na kwalan kira.
Saida gabanah ya fadi danni yanxu tsoron kiran abbi nake.
Ya ruqayya ce ta miqon hijabi tare da cewa "maza kisaka kije kiranki yake"
saka hijab din nayi na fito tsakar gidan wanda na kusa kwana 4 ban tako shi ba.
Abbi yana tsaye a qofar dakinsa naje na zube ina gaisheshi da kodaddiyar muryata.

Ki shiga ciki Abdurrahman yananan"yace yana nunan dakinsa.

Abdurrahman?waye kuma haka?
Ganin ya tsaya yana kallonah yasa na miqe na danna kaina dakin ba tare da nasan mai kiran ba.
Rass!Gabana ya fadi dan ganin mijin ya fatima a zaune kan sallaya ya tankwashe kafa yana latse latse a wayarsa.

Ba shiri na tsugunna dan jin wani jiri danayi yana qoqarin kayar dani.
Mun dauki tsahon lkc a haka inata saqa da warwara na jiyo takunshi yana qarasowa inda nake.
Zama yayi daf dani wanda yasa bugun xcy tah qaruwa da sauri.
Sai daya gama qaremin kallo danni koya aka kalleni inaji a jikina.

Dubeki dan Allah,ke a dole xaki aure mijin yayarki saboda cin amana koh?to inason ki sani,zaki aure ni kamar yadda kike buqata,amma ki sani na karbi wannan qaddararran auren nakine sbd yarana suna buqatar 'yar aiki..."

Inaso kisa a ranki ba gidan aure zakije ba gidan aiki xakije,dan nasan kinsan nafi qarfinki tun ba yau ba"

Sannan naji kamar ance wai kina zuwa jami'a koh?to inaso daga yanzu ki saka hakan a tarihin rayuwarki,domin zakina zama a gida ne kinamin gadin gida na.wannan shine saqon idan kin kiyaye kanki"

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!
Wai meyake faruwa da nine?me yasa rayuwa zata juya min baya irin haka?bayan hanashi aurena da akayi burin nashi ma baza'a bari na cika masa ba?

Bansan lkcn da ya fita a dakin ba,sai muryar abbi dana jiyo yana cewa.

"me kuma kk jira har yanxu baki shiga ciki ba"

A hankali na furta"Abbi ku taimaka min na cigaba da karatu na koda zaku aura minshi dan allah"
Guri ya samu ya zauna kafin yace"khadija inaso kisan cewa abdurrahman a yanxu kamar mijinki yake,zan iya cewa yafini iko dake,kamar yadda ya buqata baya son kici gaba da xuwa mkrnt dole ki hqr da hakan.ki duba dukka yanuwanki akwai wadda take gidan miji take karatu?fasa rayuwa sukayi a haka?to ki cire wannan a ranki ki tashi ki bani waje"

A hankali na miqe na fara barin dakin,wanda a lokacin juya ta dibeni ta zubar a wajen.

Ina farkawa na ganni kwance akan gadon asibiti.
Meyasa ma aka kawoni?aida an barni a gida na mutu kawai na hutu da wannan baqin cikin.
A hankali na miqe zaune dan inajin qarfin jikina.zare allurar qarin ruwan nayi na wurgar domin bana buqatar hakan.
Tashi nayi na shiga toilet nayi fitsari tare da dauro alwala dan nasan ana bina sallah tunda yanxun naga kamar safiya ce.

Ina fitowa naga ya aisha a zaune.Riqoni tayi tanamin sannu,nidai daka na amsa na dauki hijabin dana gani na saka.

Yaya yau wace rana?"nace ina kallonta.

Yau friday"

Au ai nazata wannan karon sati nayi a asibiti ba numfashi,amma duk da haka langwabewa zantayi har abbi ya gaji ace an fasa auren,tunda ina asibiti dai ba'a dauran aure ba.

Saida na idar da sallah nayi wanka naci abinci na kwanta muna dan taba hira da ya aisha dan da alama taji dadin ganin nadan saki raina.

Da dare inajin muryarsu abbi na rufe ido haka suka gama maganganunsu suka tafi.

Washe gari nida ya aisha muka yini a asibitin dan bayan ita ba wanda ya leqo,da dare ma haka.
Ranar lahadi ina zaune na jingina da bango ina sana'ar tunani,ya aisha kuma taje gida,naji an turo qofar dakin tare da sallama.
Nusaiba ce,dan haka da gudu na tashi naje na rungumeta.
Chapter 8 · 0% Book details