← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

So nawa ne abu ya sameki kikayi kuka ya warkar miki da matsala ko damuwa?kuka ba shine mafita ba,banaso duk abinda broz zai miki ki yarda ya gano fishinki ko gazawarki"

Aunty anisa ki gane,daddyn shahid nice bayaso,da yake yanason ya fatima kin taba ganin wani abu ya hadasu?"

Naji baya sonki,shine yanxu nakeson yasoki fiye da yadda yaso duk wata mace daya taba so.idan kin yarda dani kinsan bazan cutar dake ba khadija kawai ki yarda kuma ki amince da duk abinda na fada miki.Ya abdul ba dutse bane bare kiyi tunanin bazai lanqwasu ba.inaso ki share hawayenki yanxu kiji wani matakine wanda zamu shirya na gaba"

Dan dole na share hawayena ina sauraron duk abinda take fada ba tareda na ayyana zan iya aiwatar da hakan a raina ba.

Sosai take tausata da qarfafamin gwiwa har saida taga na yarda na dauki duk wasu shawarwarinta.

Da yamma ma wanka nayi na kumayin kwalliyar,badan wai koxai yaba ba saidan kawai nabi shawarar aunty anisa,kuma koba komai gyara yana da dadi nima naji dadi a raina.

Tuwon semo nayi da miyar kubewa kamar yadda aunty anisa ta sakani,bayan na cinye qosan danayi da safe dan dama kadan nayi.

Haka shima na jere a dinning kafin na zauna a falo inayin game dita mai aji😄
[07-23, 20:48] Sistoh: 💙💙RABON KWADO.....💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿106-🅿110

sai wajen 9pm ya shigo kamar kullum fuskarnan a hade kamar hadari.

Sannu da dawowa"na fada cikin fargabar abinda zai biyo baya.

Ko inda nake bai kalla ba bare nasa ran zai amsa.

Bin bayansa nayi da kallo kafin na koma mazaunina Ina jinjina hali irin nasa.Amma a yadda aunty anisa take fada wai yana da sauqin kai,ko ina sauqin kan yake anan oho.

Kiran aunty anisan ne ya katsemin tunani.

Ita dai baiwar Allan nan ta damu da lamarina.

Khadija broz ya dawo koh?"ta fada.

Ni lamarinta har mamaki yake bani,tana abuja amma tasan duk wani motsi nasa da duk lokutan dayake gabatar da abubuwa?

Kiyi qoqari kiyi abubuwan dana fada miki kinji?"

Aunty anisa yanxu ma fa ko sannu da zuwana bai amsa ba"

Nasan bazai amsa ba dama khadija,yanxu ki bari zai fito kallon News falon saiki gabatar masa da abincin,insha allah indai yaga abincin zaici dan yana matuqar son cimar"

Da To naita binta har mukayi sallama.

Inanan zaune kuwa sai gashi ya fito,nan ma ko inda nake bai kalla ba ya fara kunna tv.

Ganin ya kishingida ya fara kallon labaransa yasa na tashi na shiryo masa abincin a babban faranti na kawo na ajiye a center table.

Flat na dauka na zuba abinci,kafin na zuba masa tataccen inibi a cup.

Ga abinci"nace ina kallonsa.

Wani mugun kallo ya watsa min nida abinci kafin yayi mgn.

Is better for u ki bar wahalar da kanki,ki daina bata lkcnki kina yaudarar zcyrki.Bakida abinda zaki burgeni dashi,zaifi miki ki cigaba da zama a matsayin yar aiki kamar yadda na shawarce ki tun farko"ya juya ya cigaba da kallonsa kamar bashine yayi mgnr ba.

Gwiwa a sace na fara tattare kayan abincin zcytah na zafi.

Kitchen nakai kafin na koma daki.kashe wayar nayi na sakata a drower,dan nasan dole aunty anisa ta kira.

Bazan qara kunna wayar bama bare ta kuma fadan wani abu dazan jawa kaina raini.

Tsahon kwana uku ban kuma yarda mun hadu dashi ba,dan yunwa ce kawai take fito dani daga daki.wayar ma tun a ranar ban kuma waiwayarta ba,dan zamana haka ya fiye min alkhairi da nakai kaina a wulaqanta ni.

Dauke nake da cup na fito daga kitchen ina shirin komawa daki naji ance.

Zo nan"

Saura qiris cup din ya fadi dan na tsorata sosai,banyi zaton da mutum a falon ba sai yanxu.

Falon na qarasa na nemi guri can nesa na zauna na fara shan custard din dake cikin kofin.

Tashi naga yayi,ga mamakina naga yazo kusa dani ya zauna.

Daxu munyi waya da ummi ta fadan Mubina gobe zatazo holyday,kuma nasan ummi zata turota ne C.I.D,dan haka zakiga abubuwa na faruwa karki dauka wani abun ne.sannan Me anisa zata fada miki ta dameni da kira?"

Nidai banyi mgn ba,hasalima ni ba wani fuskantar abinda yake cewa nake ba.

Kunnena ya kama yaja da qarfi wanda yasa dole na saki qara.

Banaso ina yiwa mutum mgn yayi min shiru"

Nidai Allah ya isa nake ja a zcyta dan ba qaramin ja yayiwa kunnen ba.

Sum sum na tashi na bar gurin ina qara jajjada allah ya isa.

Sosai naji dadin xuwan mubina,inda muka baje munata shan hira kasancewarta gwanar surutu,dama kadaici ya isheni.

Tare mukayi girki muka jere a dinning kafin mukayi wanka.

Das!na fito a cikin wata maroon din shaddata datasha aiki.duk da banyi wata kwalliya ba nayi kyau ba qarya.

Wannan duk kwalliyar yayan namu ce?kice haka ake kasheshi da wanka"ta fada da sigar wasa.

Murmushi kawai nayi ina feshe jikina da turare.

Nipa qamshin abincin nan duk ya hargitsani,nidai ci zanyi nasan ke saikin jira mijinki"tace.

Falo na dawo na kwanta ina kallon pictures a wayarta inda ta dawo falon tanacin abinci tana min bayanin hotunan daki daki.

Da sallama ya shiga hannunsa dauke da qaramar leda.

Fuskarsa dauke da murmushi ya qaraso yana amsa sannu da zuwan da mukayi masa a tare.
Nidai kallon mamaki kawai nake masa.ban gama mamaki ba sai danaga yaxo Daf dani ya zauna tare da dora kansa akan kafadata yana kallon wayar.

Nernah yau na gaji sosai wlh"yace da wata murya da bansanshi da ita ba.

Tuni na daskare a wajen,dan numfashima daqar nakeja.
Sosai abin ya bani mamaki dan gani nake kamar a film.

Mubina me kk yiwa matata taqi yimin mgn?"yace yana kallon mubina.

Ai kunfi kusa yaya,gatanan ka tmbytah,maybe dan baka dawo da wuri bane tanata jiranka ku ci abinci"tace tana cigaba da cin abincinta hankali kwance.

Wayyo allah!🙆🙆

Gyara kwanciya ya qarayi a jikina yana wani lumshe ido.

I'm sorry nernah,Dauko mana plat ga abin dadi na kawo miki"yace yana janyo ledar daya ajiye.

Nernah"na maimaita a zcyta.ya sadiq kadai ke kirana da wannan sunan,sai shi yanxu dan munafinci zai rada min?A iya tunanina duk tsahon zamanmu ko sunana bai taba ambata ba.

Wata dabara ce ya fado min,bashi ya iya bariki ba?hmmm

Ba fushi nake ba,kasan kaima bazan iya fishi dakai ba"nace ina sakar masa wani killer smyl.

Kallona yake da alama na mamaki ne,sai kuma yayi saurin dauke idonsa daga kaina.

To maza dauko plat din"yace.

Gafa abinci can yana jiranka,kuma kasan sbd kai nayi"na fada a shagwabe.

To duk zanci a kawomin"ya fada still yana kallona.

Ina barin falon na jingina da bango ina maida numfashi dan ba qaramin qoqari nayi ba.

A trey na jero abincin na kawo inda muka zauna qasan carpet din ya wani bude qaramin bakinsa shi a dole saina bashi abinci.

Yadda yake langwabewa yana zuba min shagwaba kamar wani qaramin yaro shi zaifi baku mamaki,ita kuwa mubina in banda dariya ba abinda takeyi.

Idan ka ganshi yanxu bazata taba tunanin daddynsu shahid bane wanda ka sani,dan yadda yake shagwaba ko iman batayin irinta.
Nima duk shagwabata saida na sara masa dan wannan har PHD yayi akan shagwaba😄

Shagwabar ma tafi cin abincin yawa,nidai biye masa nakeyi dan na qagu a gama cin wannan abincin.

Dan dole na bude nawa bakin yana zubamin loma.haka dai muka gama shirin film din na tattare kwanuka nakai kitchen.

Daga nan ban dawo falon ba nayi daki.

Wanka na sake nayi shirin bacci dan nace bazan koma falon ba,dan bazan iya wannan shutting din ba.

Wayatah na dauko na kunna na dannawa aunty anisa kira,dan nasan ban kyauta mata ba,kuma inaso ta bani shawara akan wannan rikitaccen al'amarin.

Sannu khadija kin kyauta"tace bayan ta amsa sallamar.

Amin afuwa auntynah"nace ina murmushi.

Ba wani aunynkikin samu miji shine kk manta dani"tace tana dariya

Aunty ba haka bane wlh"

To yanxu ya ake ciki?"

Lbr na bata duka kafin tayi shiru kamar bazatai mgn ba.

Kinsan me khadija?wannan ma wata hanyace mai sauqi Allah ya kawo mana,dan haka zagewa zakiyi kiyi duk wani abu daya kamata,akwai abubuwa masu tarin yawa anan gaba,dan haka sai mun qara shiri sosai"

Amma aunty.....

Khadija banason kina karaya haka,zaki iya kiyi kawai"

To Aunty nagode"

Yanxu ina mubinan?"

Na barsu a falo"

To maza ki koma ayi hirar dake,kuma duk abinda yayi ki biye masa,zamuyi mgn da mubinan itama"

Tom aunty saida safe"

Na dade zaune a gefen gado ina tunanin wannan baqon al'amari kafin daga bisani na zira hijabi akan kayan baccin duk da kasancewarsu masu kauri na fita.

Mubina ce kawai a falon tana waya naje kusa da ita na zauna.

Wai yau baza muyi bacci bane?"nace ina kallon agogo ganin 11 harta wuce.

Saida ta kashe wayar kafin itama ta kalli agogon.

Kinsan in mutum yana tare da masoyi baya sanin lkc yayi"tace tana dariya.

Qarasowarshi yasa na fasa mgn,inda yake sanye da farar riga mai qaramin hannu sai wando baqi ina gwiwa.

Laptop din hannunsa ya bude bayan ya zauna can wata kujera.

Yaya ana shirin bacci kana shirin aiki?"mubina tace.

Idan banyi yanxu ba mubina gobe bani da lkc"ya fada yana kallon abinda yakeyi.

Tom nidai saida safe"tace tana miqewa.

Bayanta nabi dan ni kaina baccin nakeji.

Wanka ta shiga inda ni kuma na nemi maqwanci.

Wai mene haka kin wani bar mijinki a can kinzo nan"tace bayan ta fito daga wankan.

Shiru nayi mata kamar banji ta ba.

Hawa gadon tayi tana jan blanket din dana rufa.

Wlh ki tashi ki tafi gurin mijinki babu ruwa na"

Dan allah mubina ki kyaleni,ni anan nake kwana'"nace inajan blanket din daga hannunta.

Kafa min idanu tayi kamar zata cinye ni.

Amma wlh khadija bakida wayo,to mijin naki wa kk barwa?"

Ke na barwa kije ki tayashi hira"nace ina dariya.

Ke wlh baki isa ba sai kin tashi kin tafi"tace tana jana.

Kaji mata da qarfin hali,dan allah ki barn..."

Sallamarshi ce tasa nayi shiru ina qara jan blanket tare da rufe jikina.

Tashi mu tafi"yace yana wani tsare gida kamar ba shagwababben nan ba😜.

Ganin ba alamar wasa a fuskarshi yasa na miqe ina turo baki.

Hannu ya miqomin ba musu na kama ya riqoni muka fita🤝

Muna fita ya juyo.
Chapter 17 · 0% Book details