← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ki fadawa ummi wlh qarya take kinsan dai ba'a shan ciki a ruwa"

Hhhhh naqi din,ni yanxu ma jinake kamar nayi tsuntsuwa nazo,dan ummi bata dauki zancen cikin nan da wasa ba,yadda kikasan bata taba jika ba,dan ko cikin shahid bancen tayi irin wannan murnar ba dan nima itace ta kirani ta fada min yanxu"

Wayyo ni,to yanxu aunty ya za'ayi?"

Ki bari zuwa next week insha allah zanzo dama akwai wasu shirye shirye da nakeyi miki"

Tom aunty Allah ya kawoki"
[07-26, 11:04] Cwt-besty: 💙💙RABON KWADO....💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿121-🅿125

Duk yadda mubina tayi dani qin fita falon nayi duk da ta tabbatar min ya koma office.

Tasani tayi a gaba da tsokana kala kala,nidai gyaleta nayi dan naga abin nata ba mai qarewa bane.

Sai yamma mufidat tazo,inda suka hadu suka maida ni kamar wata kakarsu.

Dan allah ku qyaleni,wlh qaramun ciwon kai kuke yi"nace cikin qosawa.

Kinga sis qyaleta kar wannan mijin nata ya dawo ta hadamu dashi"mubina ta fada.

To na bari dan yadda yake dokin cikin nan zai iya yin komai a kanshi"

Wai ciki.su sai zuzuta abinda babu shi sukeyi,kuma babu ranar samunshi.

Mai ciki me kk so mu dafa miki kar broh ya dawo yace mun barki da yunwa"mubina tace.

Ni ki barni idan zanci zanje da kaina na dafa"

Ai tunda kika samu ciki ko tsinke bazaki kuma daukewa ba bare shiga kitchen.yanxu ki kwanta ki huta kafin muyi miki farfesun kifi kici ko?"tace tana jan kumatuna.

Ni banajin bacci"nace ina turo baki.

Hhh kema mijin naki ya koya miki shagwabar kenan?ke mufida bakiga soyayya a gidan nan ba,ai daukar course kawai nake,dan bakiga yadda yaya yake wani narke mata ba yadda kikasan qaramin yaro,ashe duk shagwabar da yakeyiwa ummi nafila ce"mubina tace.

Wayyo kice kallo ya barni"

Ai kuwa dai"

Ganin bazasu barni ba yasa na kwanta na rufe ido kamar bacci nakeyi har suka gaji kowa ya kama gabansa.

Yau maigidan bai dawo da wuri ba dan har 10 bai shigo ba.

Dan hk abinci muka ci dukanmu a flat daya kafin muka dawo falo ko wacce ta dauki waya tana chat.nidai a kwance nake kawai,dan har lkc kaina yana dan min ciwo.

Kawai mafita nake nema dan banaso na kuma kwana a part dinshi,amma bansan wace hanya zan bi na kaucewa hakan ba.gashi yau harda mufida nasan banida hanyar dazan kare kaina.

Vibrating din da wayata takeyi yasa na janyota,ganin aunty anisa yasa nayi picking mukasha hira.

Aunty anisa akwai mgn fa,kuma ga yan biyun ummi sun tasani a gaba"nace ina dry dan ganin duk sun kalloni.

Sai ki tafi daki ai,badai mgnr matan aure ce ba?muma dai mun kusa shigowa daga ciki ehe"mubina tace

Ina dariya na tashi nayi daki dan duk abinda tace anty anisa na jiyota dan itama dariyar takeyi.

Inajinki khadija ya akai?"

Aunty mgnr cikin nan ce dai,ni wlh banaso anayinta kuma kinga har ummi ta dauka da gsk ne"nace ina kwanciya a kan gadon.

Kinga kibar mgnr nan plzz,shi broh din ma dazu na kirashi domin nayi masa congrts dan banaso ya fahimci nasan wani abu game daku.
To shine yake fada min ummi ta baki mota shi kuma yace mata ta barta tunda ba wani guri kk zuwa ba,kuma idan zaku fita akwai driver,idan ma kina buqatar motar zai baki qarama,amma ummi taqi wai wannan kyautarta ce"

Haka ne gsky a yanxu bana buqatar mota aunty"nace ina qara lafewa a kan gadon.

Duk da haka nace a karbo miki tunda kyautar surukarki ce sbd samar mata jika da akayi"tace tana dry.

Kema tsokanar tawa zaki yi?"nace a shagwabe.

Dariya ta cigaba.

Yawwa aunty,kinga Jiya da mubina tazo a part dinshi na kwana,kuma ni yau banaso na kwana a can"

Sbd me?"

Aunty Allah bayaso na kuma...."

Ya isa khadija,wannan tsakaninki da mijinki ne ba komai zakina fada min ba kinji?hk zaki daure ki ringa zuwa kina kwana,hakan zai qara muku kusanci da kuma sabawa da juna.ki tashi kiyi shirin bacci,akwai wata farar sleeping dress a cikin kayan nan ki sakata kije wajen mijinki,bayasonki ba hujja bace ba"

Aunty allah bazan iya ba"na fada kamar nayi kuka,dan da gsk bazan iya din ba,domin da rigarnan gwara babu.kuma shi zai fassarani da wani abu tunda jiya yace min bakin rijiya ba wajen wasan yara bane,ko yana tunanin wani abu naje nema oho,bare ya ganni da wannan shigar saiyafi wulaqanta ni.

To shikenan khadija,kita fadar bazaki iya ba kinji?"tace tare da kashe wayar.

Fishi tayi kenan?wai meyasa kowa ya gaza fahimta tane?ita danake samun dan sassauci a gareta yau dinma ta gaza fuskanta ta.

Allah kasan halin danake ciki ka sassauta min.

Tunane tunane na shigayi,wanda tsahon lkc ban samu wata mafita ba.

Mufida ce tazo ta tabani.

Matar broh wai bacci kikeyi?"

Dagowa nayi"Aa nadai kwanta ne.

Kije wajen broh dan yana cikin damuwa sosai"tace itama da damuwa kwance a fuskarta.

Damuwa kuma?ya dawo dama?"na jera mata tmbyoyi.

Tun dazu ya shigo,kukama naga kamar yanayi,kuma nasan bazai rasa nasaba da company din motors dinmu ba,nasan shi kadai yake iya karya zcyr ya abdul,dan family din Abbanmu sun sakawa company din nan ido khadija,kuma wlh dashi kawai muka tsira"nace tare da fashewa da kuka.

Rasa wani tunani xanyi don haka na shiga rarrashinta tare da bata baki,don a kalamanta na fara gano wasu abubuwa.

Daqar tayi shiru inda muka fito falon jikina duk yayi sanyi.

Kwance yake a qasan rug inda yayi matashi da cinyar mubina.

Nidai gefe nayi na zauna ina nazarinsu daya bayan daya danshi idanunsa a lumshe suke.

To yanxu broh ka sanarwa da ummi?"mubina tace.

Banason ummi taji wannan mgnr kwata kwata,kunsan ummi da saka abu a ranta nasan zatafi kowa shiga damuwa"

Amma yaya haka zamu zuba musu ido suna ja mana asara a company?"mufida tace.

Ganin da nayi mgnr kamar tasuce suda family dinsu hakan yasa na miqe domin basu waje.

Ina zakije?"na tsinkayo muryarsa.

Cak na tsaya dan bansan amsar dazan bashi ba.

Mufida kuje ku kwanta dare yayi,tea din nernarh ta dafa min"ya fada yana tashi zaune.

Saida safe sukai masa kafin suka wuce amma kana kallonsu kasan da akwai damuwa a ransu.

Lkc daya naji tausayinsu ya kamani duk da bansan gundarin damuwarsu ba amma na fuskanta daga bangaren mahaifinsu ne.

To wai duk dangin mahaifine haka?tunda gashi muma bama ga maciji da namu dangin mahaifin.to su ina nasu mahaifinma?

A yimin afuwa na rashin jina kwana biyu.Ngd
[07-26, 15:28] Cwt-besty: 💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿126-🅿130

Ina tsaye kamar an dasa ni naji an kama hannuna.

Juyowa nayi ina binshi da kallo.

Baiyi mgn ba illa jan hannuna da yayi zuwa part dinshi.

Binshi kawai nake kamar jela tare da faduwar gaba dan bansan abinda kuma zaiyi min ba.

Zama nayi kamar yadda naga ya zauna a daya daga cikin kujerun falon kaina a qasa.

Inda na zubawa hannuwanmu da har lkcn suna hade ido inda farar fatar hannunshi da baqin gashi yayi mata qawanya ta hadu da tawa baqar fatar.

Zan iya samun koda tea ne dan tun safe banci komai ba"yace yana shafa cikinsa da daya hannun.

Saida na kalleshi dan tabbatar da cewa shine yayi mgn,domin ban zaci hakan ba dan da wata tattausar murya yayi min mgn.

Ganin ya zuban ido yasa nayi qoqarin tashi amma still yana riqe da hannuna.

Da naga bashi da niyyar sakina yasa na fara qoqarin kwace hannun sannan ya sakeni.

Kitchen din naje na hado masa tea dan iyayi na harda soya masa kwai dan naji yace tun safe baici komai ba kuma nasan tea kawai bazai daukeshi ba.

Yana zaune inda na barshi,sai dai yanxu ya cire rigar jikinsa inda ya jingina da bayan kujera tare da lumshe ido.

Tausayinsa naji yana shiga ta,don nasan ba qaramin abune zai sakashi yin la'asar haka ba,tunda gashi nima naci albarkacin hakan.

Dora qaramin plat din hannuna nayi a qaramin glass din dake gefen kujerar.

Ga tea din"nace ina satar kallonshi,don duk sai naji ni a takure sbd cire rigar da yayi.

Tnks"ya fada tare da daukan cup din ya fara kurba.

Har na shiga yiwa kaina allah ya qara ganin bai kula soyayyan kwan ba,sai kuma naga ya fara ci.

Kije ki kwanta dare yayi fa"yace yana qara gutsirar kwan.

Tashi nayi na nufi waje dan nasan zuwa yanxu su mubina sunyi bacci saina kwanta acan gashi kuma banyi wanka ba bare na saka kayan bacci.

Ina kuma zakije?"

Tsayawa nayi ina harhado amsar da zan bashi.

Zan zanje nayi wanka ne"nace ba tare dana juyo ba.

Bathroom din nan baiyi miki bane?"yace.

Aa babu...uhmm ban dauko kaya bane"nace muryata na shaking.

Zoki wuce kiyi anan"

Da sauri na juyo na kalleshi,amma abin mamaki shi abincinsa yake ci kamar ba dashi nayi mgn ba.

Ban iya musu ba,dan haka na wuce ina tunanin wani daki zan shiga.

Juyowa nayi ko zai ganni a tsaye ya nunamin amma naga shi hankalinsa ma baya kaina.

Qofar hannuna na dama na nufa tare da budewa na shiga.

Tabbas wannan ba dakin dana kwana jiya bane amma ya hadu shima sosai kuma zai iya amsa sunan bedroom tunda akwai gado a ciki.

Ganin ba dakinshi na shigo ba hakan yasa na saki jiki.na shiga wanka na hankali kwance.

Saurin komawa nayi dan ganinshi zaune akan sofa yana danna waya.

Na dade a tsaye a bandakin kafin na qara leqowa amma naga wayam.

Ko meya kawoshi nan bacin ga dakinsa can?"nace ina turo baki kamar yana ganina.

Zaman dirshan nayi akan kujerar mirrow ina shafa cream din dana gani jere akan mirrow din.

Saida na kammala kafin na bi duk turarukan kan mirrow din na fesa a jikina tare da sakin murmushi,dan inason qamshi sosai.

Hannu nakai kan kayan dana gani a kan gadon.

Jiga da wando ne kalar red masu laushi.Ai kuwa na zira tare da kashe light nabi lpyr bed.

A hankali na bude idona inda suka sauka a kanshi,yana sanye da milk din jallabiya mai qaramin hannu.

Idan zakiyi sallah ki tashi"yace yana jan bargon dana rufa.

Idan zanyi sallah?kodai ya gane bana sallah ne?wayyo allah.

Miqewa nayi ba shiri ina tattare dan gashina daya barbazu dan jiya ba shiri na tsefe kan sbd ciwo.
Chapter 19 · 0% Book details