← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da azahar na shirya na tafi tarauni dan nusaiba ma text nayi mata nace na tapi.

ya ruqayya taji dadin zuwana sosai haka itama muka sha hira,yan samarinta haka suka dameni kowa da irin tasa fitinar.
Munif ne babba,sai mufid shine mai sunan abbi,affan da kuma qaramin mubin.
Qaunarsu nakeji har cikin raina,amma abinda zai bawa kowa mamaki shine duk yaran yayyena nafi qaunar yaran ya fatima,duk da rashin jin shahid amma ina qaunarsa.yaron fitinanne ne yafi kowa rigima a cikinsu hakan yasa nake cewa halin babansa yayo,itadai ya fatima murmushi ne kawai nata.
Yaran ya fatima shahid ne babba,sai shahida sannan iman ita yanxu shekarta daya da rabi.
Da dare haka mukaita tatsuniya munashan dariya,itadai ya ruqayya gurin mijinta ta tafi ta barmu anan.
Bacci sukayi suka barni ina zuba,qarshe dai da dai daya na kaisu makwancinsu kafin nima na nemi nawa.
Tunda na taho na kashe wayata,sai yanxu da kadaici ya isheni na kunna,dan da a gidane yanxu ina kwance kan qafar abbi munashan hira.

Kamar jira ake kiran nusaiba ya shigo.

Haba sis tun dazu inata kiranki a kashe"

Wlh sis kashe wayar nayi"

To ai kin kyauta,naga text wai kin bar unguwar?"

Eh wlh unguwar ce ta daina min dadi"

Eh lallai,dama ya sadiq ne ya tmby ni wai mene ya samu wayarki ya kira a kashe"

Dan allah da gsk?

Eh mn,dama bana fada miki ba,shi kanshi bazai iya jurewa ba,amma duk kibi ki damu kanki"

Uhmm sis baxaki gane matsayin ya sadiq a zcytah bane,baki san zafin so ba da fushin masoyi shiyasa kk fadar haka"

Sannu wadanda suka yankewa soyayya cibiya,ni kinga yaushe zaki dawo?"

Ki tmby ya sadiq,dan sai ranar daya daina fishi dani xan dawo"

Dif!naji ta kashe wayar ko ba'a fadan ba nasa haushin mgn ta taji.oh nusaiba danger,ita gani take banida aikin yi idan ina irin wadannan maganganun batasa ita kadai nake iya fallasawa sirrin zuciyata ba,dan koshi ya sadiq din cikin qorafi yake wai banasonshi.
Jin danayi nusaiba tace ya sadiq ya tmbyta ni ya tabbatar min ya sauko daga fushin da yayi,kuma a kowani lkc xai iya kirana,amma inason ya dandana abinda naji dan haka nayi addu'a tare da kashe wayar nabi lpyr gado.

Washegari ma saida muka gama aikace aikace nida ya ruqayya,nayi wanka nayi breakfast sannan na dauko wayar dan yaran gidan duk sun tafi mkrnt,mubin ne kawai tunda shi bai isa xuwa mkrnt ba kuma shi ba wata hira xamuyi da shi ba.
Data na kunna dan ganin me duniya take ciki,dan ni ban damu da hawa online sosai ba(ba kamar Er baby ba da kullum ana online😜).

Sosai nake jin dadin chatting din kiran ya sadiq ya shigo.har ta katse ban dauka ba saboda nidin mai ajice😄,duk da dunbin qaunarsa da kewarsa da nake hakan bazai sa na zubarda ajina na 'ya mace ba.
Daya qara kira ma saida ta kusa katsewa na dauka.vanyi mgn ba shima kuma baiyi ma.munkai tsahon 5mnts a haka dan da niyyata na kashe wayar tunda bashida abin fada.

"Khadija ni kk wulaqantawa koh?"najiyo muryarsa data fi kama data marasa lpy.

Nipa ba wulaqanta ka nake ba"

To mene wannan inba wulaqanci ba?ko kuma raini ne dan kinga ina wasa dake?"

Aa kayi hqr"nace dan jin ya fara mgn da fada fada.

Waye wanda na ganki dashi jiya?"
Saida nayi murmushin mugunta kafin nace.

"wani ne wai sona yake,shine ya biyoni yaga gidanmu wai zai turo a tmbyr masa izini"

Wani dan iska ne kuma a ina yake?baki fada masa ba yanxu xakiyi aure ba?ko kuma baki fada masa akwai wanda yake jiranki ba?wlh wlh khadija ki gaggauta sallamarsa idan ba haka ba kuma.."

Dif!ya kashe wayar.ni dariya ma wallahi ya bani,wannan tmbayiyi kamar yana mini interview?
Sai daga baya tausayinsa ya kamani,gsky ya sadiq masoyi ne na gsky,tun bansan kaina ba yake dakon soyayyata,kuma ya haqura da aure badan wai baya buqata ba Aa sai dan gani ya ingantan rayuwa ta ta hanyar ganin na fara karatu,dan yanxu karatun shine mutum.
Ya sadiq yana taka matsayi kala kala a gurina,wani lkc yazo min a matsayin yaya wanda yakeji da qanwarsa wanda nakan ji dadin hakan koba komai nima naji abinda masa yayye maza sukeji,wani lkcn yakanxo a matsayin masoyi yaita kasheni da kalaman soyayya dan a wannan bangaren gwani ne,wani lkcn yakanxo a matsayin yayana wanda zaimin fada tare da bani umarni shima nakanji dadin hakan dan nasan wani fada da nasihar da yakemin ko nusaiba da take qanwarsa ta haqiqa bayayi mata.
Hakan kan qara masa matsayi da qima a idona,shiyasa ko yaya naga ransa ya baci sai na shiga damuwa musamman ma idan nice silar bacin ran nasa,dan shima ko kadan bayason yaga bacin raina.ya sadiq ko budurwa yayi saiya fada min,nakan tmbyshi ki meyasa yake fadan shine yace shi bayaso zargi ya shigo cikin lamarinmu shiyasa tun kafin naji yake fadamin da bakinsa kuma da sigar da zan fahimci inda ya dosa.
Kai ya sadiq mutum ne wanda ko wace mace take fatan ya xama abokin rayuwarta amma ni qaddarar rayuwa ta nisanta ni dashi,tayi mana katangar a tsakaninmu mai wahalar rushewa😭💙💙RABON KWADO....💙💙

Na Er mutan ungogo💋💖💋

🅿26-🅿30.

A gurguje Haka rayuwa ta cigaba da tapiya inda result dinmu ya fito muka zana jamb nida nusaiba dan alhmdllh result dinmu yayi kyau.
Cikin ikon allah muka nasarar samun admission da taimakon abban su nusaiba,inda zan karanci bangaren law nusaiba kuma bio/chem.
Farin ciki wajen yaya sadiq ba'a mgn nasiha da shawarwari kuwa na shasu kamar shine abbi na.
Cikin nasara muka fara gudanar da lectures dinmu a jami'ar bayero,inda mukayi da ya sadiq xaije wani course na 6months daya dawo xa'akai mgnr aurenmu wajen abba asa rana duk a lkcn dan yace bayaso asa sama da wata biyar.
Haka mukai sallama dashi da tarin nasihohinsa gareni ya tafi ya barni da kewarsa dan har kuka saida nayi.
Sosai lectures suka fara daukan dimi,inda muka maida hankali kan krt ba wasa.
Ya fatima ce ta kirani wai nazo gidanta mijinta yayi tafiya ga dawainiyar yara ga kuma cikin da take dauke dashi.
Haka na tattara na tafi dama kuma gidanta yafi kusa da scul din tunda ita tana rijiyar xaki.
Duk wata dawainiyar yaranta nice nake musu kafin na tapi scuk duk da suma idan suka tafi tun safe sai yamma,amma fitinar shahid sai abinda ta qaru.
Yauma haka yaje ya zazzagen handbag dina a qasa ya dauko handouts dina ya yi min zane a jiki.
Naji haushin abinnan naje tana barandar gidan tana shan iska.

"Yaya kinga yadda shahid ya wuqanta min handout dan allah"

Kinga auta kuje can ku qarata na gaji da shirginku keda shahid,tsoronsa kk ji da baxaki hukunta shi ba?ko kuma idan danki ne haka zaki biye masa kina kai qararsa?"

"Amma yaya kina ganin yadda ya rainani ban isa nayi abuba sai yayi mgn kamar wata sa'arsa"

"Dan allah ni kuje ku gyaleni naji da kaina"tace tana kwanciya.

"Wlh mai rabani da yaron nan sai allah"nace ina komawa cikin gidan.

Bansan fitinar shahid takai haka ba saida naga muna dambe dashi kamar wani sa'a na,ai kuwa zuciya ta deboni na samu nasarar warbar dashi a qasa aka samu akasi goshinsa ya fashe ya kwalla qara,wadda tayi dai dai da qarasowar daddynsa da ya fatima wanda da dukkan alamu dawowarsa kenan,amma da nasan yau xai dawo da daga mkrnt na wuce gidanmu bare na kwashi wannan kayan takaicin.
ko kadan banyi nadamar abinda nayi ba sai danaga jinin da yake fitowa daga goshinsa.

"Hayaty bari muje asibiti ko zamu sami jinin ya tsaya"daddyn nasu ya fada yana wani cin magani.
Ni kuwa nace idanma dan ya ganni a gidansa ko dan najiwa dansa ciwo yake wannan abin to gobe da safe ma xan kama gaba na,yanxunma dan dare yayi ne amma da ba abinda xai hanani tafiya.
Daki na shige dan gaba daya gidan haushi yake bani.
Ban dade da kwanciya ba ya fatima ta shigo.

"Auta badai bacci ba bakici abinci ba?"

Ni na qoshi"

Haba autar ammi ki taso kici ko kadanne,ko kinason ammi tace bana baki abinci?"
Girgixa kai nayi.

"Yawwa to tashi muje kici,sai ki dauko su iman daga falo ki kyautar dasu"
Kadan naci abinci na daukosu dama tunda naxo tare muke kwana,bacci nayi bansan lkcn da yan asibiti suka dawo ba🙁
Washegari tun asuba nayi wanka dan inason barin gidan tun kafin mai gidan ya farka daga bacci.
Da yake weekend ne har 9 ina xaman jiran yaya tazo dan tana bangaren mijinta.da yake gidan babba ne gsky kuma an kashe masa kudi iya kudi,dan duk gidan ya fatima yafi na sauran haduwa.
Kiran wayarta nayi a kashe dan haka tea kawai na hada na rubuta letter na ajiye mata a gado nace mata kirana akayi muna da text 10 shiyasa na tafi kuma daga can xan wuce gida.
Daqar na samu abin hawa kasancewar safiya ce kuma unguwar shuru kowa yana cikin gida dan saida nayo tpy mai nisa kafin na samu amma duk ban damuba sbd sa kai ance yafi bauta ciwo.
Ammi batai mamakin ganina ba dan tasan halina,kuma tasan bama jituwa da gidan ya fatima,abbi ne dai yake ta tmby ko lpy na dawo yanxu kamar an koro ni?

"Abbina mafarkinka nayi shine yau da safe nace ni saina xo na ganka"na fada a shagwabe.
Dariya yayi

"Khadijatu bakya gajiya da shirme,kin baro su lpy dai koh?"
Amsa masa nayi na shige daki.
Da ya fatima ta kira kuwa nasha fada wajen ammi nidai bance komai ba tunda nazo gida.

A kwana a tashi babu wuya a wajen allah.
Yau muke saka ran dawowar ya sadiq,amma bansan mai yasa ba yau din banajin dadin jikina ga gabana da yaketa faman faduwa.
Haka na fara shirin xuwa scul ina karanta du addu'ar data xo bakina.
A scul ba haka na yini sukuku,da muka fito a lecture na fara kiran number din ya sadiq dan jin ko wani abu ne ya sameshi.

Hello yanmatanah"naji ya fada hakan ya tabbatar min yau a masoyi yake mgn,dan naga ko jiya da mukai waya sai wani rawar qafa yake waishi angon wata5 ne.

Yaya kun sauka ne?"

Eh mun sauka heartbeat tun dazu amma office na wuce dan akwai wani record da nakeson bayarwa"
Chapter 4 · 0% Book details