← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💙💙
RABON KWADO.. 💙💙

Tare da Khayratie Er Mutan Ungogo..💋

Ina roqon Allah S.W.A yadda ya bani ikon farawa ya bani ikon ganin na kammala wannan littafi.
Wannan littafi qirqirarren labari ne,wanda nake fata ya fadakar,wa'axantar,Ilimantar da kuma nishadantar da masu karatu. A matsayi na yar kowo wanda wannan shine littafi na na farko ina son idan anga kuskure ko gyara ayi gaggawar sanar dani.

Na sadaukar ga wannan littafi ga Qawata,Aminiyata kuma yaruwa mafi soyuwa agareni wato RUQAYYA RABI'U MUSA(RUKY NICE)Allah yabar qauna.

Bismillahirrahmanirrahim🙏

🅿1-🅿5

Kamar kullum yauma kwance nake akan makeken gadona ina sana'ar tawa wato kuka,wanda ya zamar min jiki duk daren duniya sai nayi shi tunda na tsinci kaena a sabuwar rayuwa.Jin Alamar bude qofa yasa na fara qiqarin hadiye kukana dan ko kadan banason yara na suxo su ganni a wannan hali.
Iman ce ta qaraso ta fara tashi na don a zatonta bacci nake.

"Aunty!Aunty!ki tashi daddy yace kiyi mana shirin bacci mu kwanta gobe akwai school"

Saida na qarasa goge hawayena da hijabin dake jikina kafin na fara sakkowa daka bed din.
Wanka nayi mata na shiryata cikin nighty dinta pink sannan na hade mata qashinta da band.

"Kije ki kira ya shahida itama tazo tayi bacci"nace ina mai nuna mata qofa dan surutunta ya fara haddasan ciwon kai ga kuma kukan da nasha.

A tare suka shigo da yoghurt dinsu a hannu.

"Aunty kinga daddy ya siyo mana kuma harda coculate ita mun shanyeta a falin daddy"shahida tace tana nuna min jarkar dake hannunta.

Murmushi nayi tare da cewa"gsky daddy ya kyauta,kunce masa kun gode koh?

"Mu mun fada amma ya shahid bai fada ba"shahida ta kuma fada.

"Wai da gaske babyna?"na tambayi iman ina shafa kanta ganin alamun bacci ta fara ji.

Cak na dauketa kasancewa suma basu da jiki kamar ni na dorata bisa gado,kafin na kama dayar akun tawa nayi mata wanka.
Saida nayi musu addu'a na tabbatar sunyi bacci kafin na fara shirin nawa wanka.
Shirina na gama cikin nawa kayan baccin milk calour kafin na feshe jikina da turare kasancewa ta ma'abociyar son qamshi.
Kaina na qurawa ido ta jikin mirrow,basai an fada min ba nasan ni kaena na rame,to ba dole na rame ba?kullum cikin aiki da walahar yara ga kuma kuka da yawan tunani.

Allah sarki Amminah gsky ina kewarta amma ita da abbi naga alamar sun manta dani tunda ko kiransu nayi a waya bata ma shiga bare nasa ran jin muryarsu.zaman kadaecin nan ya fara damuna tunda idan su iman suka tapi school tun safe sai yamma,shi kuwa mai gidan sai nayi kwana biyar,shida kai har sati daya ma ni banganshi ba.
Kana naka Allah na nasa,wai ni khadija Autar Amminta nice rayuwatah ta dawo haka?Ba haka na tsara rayuwar aure na ba amma ga a yanda taxo min.Amma a hakanma cikin godiyar Allah nake kuma na yarda da qaddara.

Nasan mai karatu yana cikin zaquwa da sonjin cikakken tarihi na,to ga asalin wacece ni👇

FLASHBACK.

Cikakken sunana shine khadija isah muhd,mu cikakkun hausawa ne maxauna garin kano unguwar karkasa.
Mahaifinmu ma'aikacin gwamnati ne ba wani mai kudi ba,muna rayuwa cikin rufin asiri da kuma qoqarin farantawa juna.

Amminmu mu biyar ta haifa duka mata,hakan yasa dangin mahaifinmu suka dora mata karan tsana acewarsu uwar mata ce taqi haifar da namiji,ko a xatansu mutun shike xabarwa kansa abinda zai haifa?oho.
Rashin jituwar dake xakanin Ammi da dangin abbi yasa ko kadan bamu qaunar zuwa wani abu daya dangancesu,tun abbi yana fada har ya gaji ya qyale mu,sbd ko munje ma ranmu a bace yake dawowa.

Yaya Aisha itace babba a gidanmu,sai Ya Ruqayya,ya Fatima,sai kuma yaya zainab wadda daga ita Ammita qara haifar wata amma babu rai,tun daga lokacin haihuwar ta tsaya sai bayan shekara 3 sannan ta samu cikina wanda kowa ya cire tsammani dashi,hakan yasa kowa ya dora soyayyarsa kan cikin tare da fatan sauka lafiya.

Bayan wata tare Ammi ta haifeni,wanda kowa yake cewa kyawun yan gidanmu aka tattaramin,a cewarsu nafi kowa kyau tun ina jaririya.

Haka na taso cikin gata da kulawar iyaye na da yayyena abin alfarina,dan kowacce ji take dani komai aka samo to na autar ammi ne,haka abbi duk fitar da zaiyi to sai da tsarabar auta zai dawo.

Ina primary 5 akayi bikin yaya Aisha inda aka kaita unguwar sharada.
Munyi kewarta sosae duk da a lokacin ba wani wayo ne dani ba amma nasan shaquwar dake tsakaninmu,dan so da dama muna sharing problems ayi a gama ammi batasan anyi ba,duk da lokacin ba wani fahimtar abinda suke mgn nake ba hakan bayasa su ware ni muna tare koda yaushe school ce kawai take raba mu,hakan yasa bani da wasu qawaye bayan yayyena sai Nusaiba da muke class daya kuma a farkon layinmu gidansu yake shiyasa muke tafiya tare mu dawo tare.

Tafiyar yaya aisha yasa gidan ya fara shiru dan ya ruqayya ba xama take ba tana schooling a CAS kano.
Ya fatima tayi candy tana waiting result yanxu koda yaushe tana gida,amma kasancewarta bamai yawan mgn ba yasa bama wani hira sosai,to ni dimma ba wata gwanar surutu bace,barni da da shagwaba da son jiki,koda yaushe ina jikin ammina ko su yaya fatima.
Ya zainab yanxu tana Ss1,mu kuma muna shirye shiryen common interest.

Cikin ikon allah mukai Exam,inda rana tsaka abbi yazo da mgnr data tayarwa da duk yan gidan hankali,wai xa'a kai autar ammi bording school.saida aka kai ruwa rana kafin aka shayo kan ammi ta yarda akaini ni kuwa banda kuka babu abinda nakeyi.
Ammi dasu yaya fatima kullum cikin rarrashi,nice a siyon wannan a siyon wancan har ranar tafiya mkrnt tazo aka kaini makarantar yan mata ta DALA.
Fadin irin kukan dasha bata lkc ne dan harta abbi nasan kawai dauriya yake amma su yaya zainab suma sunsha kuka.

Bansha wani wahala ba kasancewa ta kyakkyawa kuma mai tsafta yasa seniors suka ringa nan nan dani nidae a daddafe mukae first term,sbd ni irin mutanennance masu maqon uwa bare tawa uwar da muka shaqu sosai.

Ranar da muka samu hutu kuwa murna biki har baka😬.
Abbi ne yaxo ya daukeni a machine dinsa.muna xuwa gida kuwa duk yanuwana sun hallara,abinci kuwa kala kala kamar ana jiran dalibi daga malesia😜.
Ranar nayi yinin farin ciki,inda nake maqale da jaririyar yaya Aisha mai suna muhibba.Anan nakejin zancen sa ranar ya ruqayya amma abin takaicin ina school xa'ayi.
Tun daga lkcn na fara kukan shagwaba ina buga qafata a qasa ni a dole yar auta😄

"Kinga ni miqon 'yata karki fadarmin da ita"ya aisha ta fada tana karbar muhibba.
"Dan allah ya ruqayya kice a daga bikin sai na nawo"na fada ina zama akan cinyarta.

"To Ammi haka za'ayi"tace tana ture ni daga jikinta.
Dukansu dariya suka saka hakan ya bani haushi nayi dakunmu da gudu kamar xanyi kuka.
Ina jiyosu suna hira akan yawan shagwaba da son jikina Ammina tana shigarmin.
Sai dare mijin ya aisha yaxo ya dauketa,ba mgnr da bata min ba naqi kulata dan har lkcn fushi nake dasu hakan yasa ko dakin ban kwana ba na tafi gadon ammi na kwanta.

Washe gari gidansu Nusaiba na yini inata bata labarin bording ita kuma allah da yayita tana sha'awar bording school.Sai wajen magriba na dawo.

Haka har hutunmu ya qare babu yadda ya aisha batai ba naxo gidanta hutu naqi,nace ni ban gaji da gani abbi da ammi ba.haka dai na tattara na koma inata kumbure kumbure na.

🥰Khayratie Er mutan Ungogo😘

💙💙 RABON KWADO... 💙💙

💋 Er mutan Ungogo💋

🅿6-🅿10

Haka rayuwa ta cigaba da tapiya,inda akayi bikin ya ruqayya da mijinta abbas aka kaita gidanta dake tarauni.

Ya fatima ta samu gurbin karatu a polytechnich dake nan kano.

Yau satinmu daya da dawowa daga mkrnt,sosai nake jindadin holyday din dan nakaiwa yanuwa na xiyara nida ya zainab kasancewar ya fatima lectures sun mata zafi.
Yau Lahadi na tashi da shirin xuwa gidansu qawata Nusaiba dan ammi tace xuwanta biyu bama nan,kuma nayo mata guxurin labarurruka kala kala na mkrntrmu.

Ammi nayiwa sallama na dauki sabon hijab din data siyamin ina mkrnt na saka na fice abuna kicin nutsuwa.

Sallama naita kwadawa a qofar falon kafin daga bisani najiyo alamar tafiya.

Dogon saurayi ne mai cikar halitta sai saje da qasunba da sukayiwa dogon hancinsa qawanya,duk da a lokacin shekaruna 13 ba wani kyakkyawa na sani ba amma xan iya cewa wannan kyakkyawa ne.ko ba'a fadan ba nasan wannan yayan nusaiba ne duk da ban taba ganinsa ba amma kamanninsu ya nuna hakan.

Kamar yadda ya zuba masa ido haka shima ya zuba min nasa idanun.bazan iya tantance iya lokutan da muka dauka a haka ba kowa da abinda yake kissimawa a ransa.
Sallamar Nusaiba ce ta katse mana kallon da mukewa juna na qurrilla.Duk sai naji kunya ta kamani amma shi gogannaka falon ya koma ba tare da yace komai ba.

Da gudu nusaiba taxo ta rungume ni tana dariya.

"Ai naxata baxaki xo ba harki koma"

"haba dae xanxo mana,Ammi ma tace zuwanki biyu bama nan"

"Eh mn,ai na qagu nasha lbrn bording,daxu ma fa har umma na tmby da xata fita nace xanxo gidanku shine ya sadiq ya hanani"

"Au dama wannan shine ya sadiq din?"nace ina rage muryar kamar ina tsoron karya jini.

"Eh shine,shima shekaran jiya ya dawo,ni banso dawowarsa ba gashi sai aiki yake saka mutan....."bata qarasa ba mukajuyo muryarsa mai sanyi yana cewa"Nusaiba!!

A tare muka xaro ido dan a xatonmu yaji mgnr da mukeyi.
Da sauri ta shiga falon.
Bata dade ba ta fito tana tura baki gaba.

"kinga ni koh?wai chemist zanje na siyo masa mgnin mura,kuma fa idan umma nanan ba'a aikena titi"

"To muje na raka ki dan nima yau yawo nakeso"

Tafiya muke ina bata labarin bording,mun kusa tsallakawa titi kawai naji kamar an watsamin ruwa a jiki.Mexan gani?kwata a jikin hijabi na sabo??
Bin motar nayi da ido dataketa sharara gudu ba alamar zata tsaya ma.

Nusaiba na kalla dan tuni idanuna suka ciko da kwalla ganin yadda mutane suke kallo na wasu har dariya suke min.

"Kiyi hqr bari naje na siyo na dawo,shi kuma shida allah"nusaiba tace tana yin gaba da sauri.
Chapter 1 · 0% Book details